Dan Kano Ya Yi Wakar Zaman Lafiya da Harsuna 11 Ya Isar da Sako ga Duniya
- Wani matashin mawaki daga Kano da ya fara harkar waka tun a shekarar 2018 ya bayyana yadda ya ke kokarin kawo zaman lafiya
- Capital K ya ce ya shirya waƙar “We Want Peace” da harsuna 11 domin isar da saƙon zaman lafiya ga duniya baki daya
- Ya bayyana burinsa na ganin waƙar ta isa ga mutane a faɗin duniya, tare da fatan shugabannin ƙasashe su dauki darasi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Wani matashin mawaki da ke zaune a Kano, Khalid Umar da aka sani da Capital K ya bayyana cewa ya fara harkar waka ne kimanin shekaru bakwai da suka gabata.
Ya ce yana da cikakken imani da baiwar da yake da ita a fannin waka, kuma yana fatan amfani da ita wajen cimma wani babban abu da zai ɗaukaka sunan Najeriya.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Legit Hausa, inda ya yi bayani kan yadda ya koyi harsunan da ya yi amfani da su wajen tsara waƙar.
Saƙon da wakar Capital K ta kunsa
Matashin ya ce sunan waƙar da ya rera da harsuna 11 shi ne “Capital K – We Want Peace”, kuma yana shirin fitar da ita a dandalin Audiomack.
Ya bayyana cewa ya rubuta waƙar ne saboda yadda duniya ke cikin rikice-rikice da tashe-tashen hankula a sassa daban-daban.
A cewarsa, amfani da harsuna daban-daban zai taimaka wajen isar da saƙon zaman lafiya ga mutane daga sassa daban-daban na duniya.
Harsunan da ya yi amfani da su
Capital K ya bayyana cewa harsunan da aka yi amfani da su a cikin waƙar sun haɗa da Turanci, Swahili, Larabci, Italiyanci, Farisanci, Hindu, Ibrananci, Sifaniyanci, Faransanci, Rashanci da yaren Ukrainiya.
Mawakin ya ce ba wai ya sanya waɗannan harsunan ne don nuna bambancin harshe kawai ba, sai dai domin kowanne harshe da aka yi amfani da shi yana ɗauke da saƙon zaman lafiya.
Daga cikin kalmomin da ya yi amfani da su akwai saƙon Larabci na neman zaman lafiya, yayin da a Faransanci ya yi kira da a samu zaman lafiya.
Ya kuma yi amfani da kalmomi daga Rashanci da Ukrainiya wajen ci gaba da isar da wannan saƙo. Matashin ya ce yana iya magana da Faransanci, Sifaniyanci, Turanci, Larabci da Hindu.
Ya bayyana cewa yana ci gaba da koyon wasu harsuna saboda yana matuƙar son koyon harsuna da fahimtar al’adun mutane daban-daban.

Source: Original
Burin Capital K a kan waƙar
Mawakin ya ce babban burinsa shi ne waƙar ta isa ga masu sauraro a faɗin duniya, musamman shugabannin ƙasashe, domin su fahimci cewa akwai mutane da dama da ke neman zaman lafiya.
Ya kuma yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da UNICEF da su fahimci cewa akwai mutane da dama a duniya da ke fatan kawo ƙarshen rikice-rikice.
A cewarsa, yana fatan waƙar ta sanyaya zukatan mutanen da ke cikin rikici a Sudan, Iran, Najeriya, Ukraine da Rasha, tare da nuna musu cewa yana tare da su a cikin wannan hali.
Rasha ta kai hari Ukraine
A wani labarin, mun ruwaito cewa Rasha ta kai hari a birnin Kamianske da ke yankin Dnipropetrovsk na kudu maso gabashin Ukraine, inda mutane biyar suka rasa rayukansu.
Harin na ranar Asabar ya zo ne yayin da wakilan Amurka na musamman, Steve Witkoff da Jared Kushner, suka isa Moscow domin tattaunawa da Shugaban Rasha Vladimir Putin.
Rahotanni sun nuna cewa shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce ya yi takaitacciyar magana da Witkoff da Kushner kafin zuwansu Kyiv.
Asali: Legit.ng


