Wata Sabuwa: Babban Yaron Netanyahu Ya Burma cikin Matsala a Amurka
- An gaggauta mayar da Yair Netanyahu, babban ɗan Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, daga Amurka zuwa Isra’ila
- Hukumar leƙen asirin cikin gida ta Isra’ila, Shin Bet, ta ce an yi hakan ne bayan tantance girman barazanar da ke fuskantar Yair
- Rahotanni sun ce a baya an zargi Iran da shirya kashe Yair a Florida, inda ya shafe shekaru yana zaune
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel Aviv, Israila - An gaggauta mayar da Yair Netanyahu, babban ɗan Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, daga Amurka zuwa Isra’ila.
An mayar da babban yaron na Netanyahu zuwa Israila ne bayan hukumar leƙen asirin cikin gida ta ƙasar ta gano wata barazana ga rayuwarsa.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa hukumar Shin Bet ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin Asabar, 29 ga watan Agustan 2026.
Hukumar ta bayyana cewa an samu “babbar barazana ta cutar da Yair Netanyahu”, lamarin da ya sa aka yanke shawarar dauke shi cikin gaggawa tare da tawagar tsaron da ke tare da shi zuwa Isra’ila.
Sai dai hukumar ba ta bayyana inda barazanar ta fito ba.
Zargin shirin kashe Yair Netanyahu
Gidan talabijin na Amurka Newsmax ya ruwaito a farkon wannan makon cewa an zargi Iran da shirya kashe Yair Netanyahu a watan Disamba na bara, lokacin da yake zaune a Florida.
Rahoton ya ce jami’an leƙen asirin Isra’ila sun sanar da hukumomin Amurka bayan sun samu labarin zargin shirin, inda Newsmax ta ruwaito hakan daga wani jami’in tsaron Amurka.
Rahoton ya fito ne bayan Benjamin Netanyahu ya shaida wa tashar Channel 14 ta Isra’ila cewa, “Iran ta kai hari kan ɗaya daga cikin ’ya’yana. Iran ta yi ƙoƙarin kashe, ta yi ƙoƙarin hallaka ɗaya daga cikin ’ya’yana.”
Newsmax ta ce an umarci Yair Netanyahu, wanda kullum yake tare da tawagar tsaron Isra’ila, da ya bar yankin nan take. An ce ya bar kayansa a wurin sannan ya dawo kai tsaye zuwa Isra’ila.
Rayuwar Yair a Florida
Babban ɗan Netanyahu ya shafe shekaru yana zaune a Florida, inda rahotanni suka ce “rayuwarsa mai tsada da kuma tsaron da gwamnati ke ɗaukar nauyinsa” sun sha jawo hankalin jama’a a Isra’ila.
Ci gaba da zamansa a Amurka bayan harin da Hamas ta jagoranta kan Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023, ya jawo suka daga Isra’ilawa da dama.
Rahoton ya ce wasu Isra’ilawa sun yi tambaya kan bambancin yadda ake kallon lamarin, inda ɗan Netanyahu yake ci gaba da zama a ƙetare yayin da aka kira ɗaruruwan dubban sojojin ajiya na Isra’ila zuwa aikin soja.
Yair na sukar abokan hamayyar mahaifinsa
Yair Netanyahu, wanda ke goyon bayan ra’ayin masu tsattsauran ra’ayin dama kuma mai gabatar da shirye-shirye, yana yawan amfani da kafafen sada zumunta wajen bayyana ra’ayoyinsa kan siyasar Isra’ila.
Yana kuma yawan sukar abokan hamayyar siyasar mahaifinsa, masu sukar gwamnati da kuma ’yan jarida.

Source: Twitter
Netanyahu ya yi wa Birtaniya shagube
A wani labarin kuma, kun ji cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya kira Birtaniya “Jamhuriyar Musulunci ta Birtaniya”, a wani furuci da ya yi cikin fushi.
Majiyoyi sun bayyana cewa Netanyahu ya furta haka ne ga ɗaya daga cikin tsofaffin ƙawayen Isra’ila a Turai.
Asali: Legit.ng

