Ana Batun Rahoton Tinubu, Amurka Ta Saki Sunaye da Hotunan 'Yan Najeriya 4 da Suka Tafka Laifi

Ana Batun Rahoton Tinubu, Amurka Ta Saki Sunaye da Hotunan 'Yan Najeriya 4 da Suka Tafka Laifi

  • Hukumar FBI ta Amurka ta wallafa sunaye da hotunan ’yan Najeriya hudu da ake nema ruwa a jallo bisa zargin hannu a wata damfarar BEC
  • Ana zargin mutanen hudu, wadanda ake kyautata zaton suna zaune a Najeriya, da laifukan damfarar kudi daga Amurkawa akalla 70
  • Daya daga cikinsu na fuskantar zargin gudanar da damfarar soyayya da ta shafi tsofaffi da zawarawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta wallafa sunaye da hotunan ’yan Najeriya hudu da take nema fuwa a jallo.

Hukumar FBI na neman wadannan mutane ne bisa zargin hannu a wata damfarar imel ta kasuwanci (BEC) da ta janyo asarar sama da Dala miliyan $6 ga kamfanonin Amurka sama da 70.

Jami'an FBI.
Jami'an hukumar binciken manyan laifuffuka ta kasar Amurka (FBI) a bakin aiki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sunayen wadanda Amurka ke nema

Kara karanta wannan

Ta faru ta ƙare: Sojoji sun shiga maɓoyar ƙasurgumin ɗan bindiga, Kachalla Muhammadu

A sanarwar da FBI ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ana kyautata zaton dukkaninsu suna zaune a Najeriya a halin yanzu

Mutanen hudu da Amurka ke bema ruwa a jallo sun hada da;

1. Richard Izuchukwu Uzuh

2. Felix Osilama Okpoh

3. Nnamdi Orson Benson

4. Micheal Olorunyomi.

An bayar da sammacin kama kowannensu bayan wata babbar kotun tarayya ta Amurka da ke Omaha, Nebraska, ta gurfanar da su bisa tuhume-tuhume daban-daban.

Yadda damfarar ta gudana

A cewar FBI, Uzuh, wanda aka haifa ranar 29 ga Afrilu, 1986, shi ne ya tsara yadda damfarar ta gudana, inda ya rika aika sakonnin imel na bogi ga dubban kamfanoni a fadin Amurka.

Ana zargin sakonnin sun yaudari kamfanonin wajen amincewa da tura kudade ta banki zuwa asusun da ba sahihi ba.

FBI ta ce Uzuh ya yi aiki tare da masu halasta kudaden haram, masu damfarar soyayya da wasu mutane da ke cikin kungiyoyin damfarar BEC domin raba kudaden da aka samu..

An tuhumi Uzuh a ranar 18 ga Oktoba, 2016, da laifin damfarar kudi ta hanyar waya da hada baki wajen aikata irin wannan laifi.

Kara karanta wannan

EFCC ta kama mutum 2 'yan Najeriya, ta mika su ga Amurka saboda laifin da suka aikata

Okpoh ya samar da susun banki

Okpoh, wanda aka haifa ranar 9 ga Maris, 1989, ana zarginsa da samar da daruruwan asusun banki da aka yi amfani da su wajen karbar kudaden da aka sata.

Rahotanni sun nuna cewa asusun da ya samar sun karbi kudaden haram da suka zarce dala miliyan 1 daga kamfanonin da aka yi wa damfarar.

Benson, wanda aka haifa ranar 21 ga Maris, 1987, shi ma yana fuskantar zargin hada baki wajen aikata damfarar kudi ta hanyar waya da ta shafi wannan shiri da aka kai wa kamfanoni sama da 70 hari.

Zargin damfarar soyayya

Olorunyomi, wanda aka haifa ranar 12 ga Mayu, 1983, ana zarginsa da gudanar da damfarar soyayya da aka fi kai wa tsofaffi da zawarawa hari.

Hukumar FBI ta ce an damfari wadanda abin ya shafa sama da dala miliyan $1.

Amurka.
Jami'an gwamnatin Amurka da hoton daya daga cikin wadanda FBI take nema ruwa a jallo Hoto: FBI
Source: Getty Images

Sammacin kama yan Najeriya 4

Kotun tarayya ta Amurka ta bayar da sammacin kama Uzuh, Okpoh, Benson da Olorunyomi kuma har yanzu b su shiga hannu ba

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun harbe shugaban jam'iyyar APC, sun tafi da mutumin da suke tare

FBI ta wallafa sunayensu da hotunansu ne a wani yunkuri na sanar da jama'a game da sammacin kama su, tare da neman bayanan da ka iya taimakawa wajen gano inda suke da kuma kama su.

Abin da ya hana kama Tinubu a Amurka

A wani labarin, kun ji cewa ɗaya daga cikin lauyoyin Bola Tinubu ya ce rashin hujja kan zargin safarar miyagun kwayoyi ce ta hana Amurka kama shugaban kasa.

Lauyan ya ce da a ce akwai hujjar da ke alakanta shugaban da safarar miyagun kwayoyi a Amurka, da hukumomin kasar sun kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262