EFCC Ta Kama Mutum 2 Yan Najeriya, Ta Mika Su ga Amurka saboda Laifin da Suka Aikata

EFCC Ta Kama Mutum 2 Yan Najeriya, Ta Mika Su ga Amurka saboda Laifin da Suka Aikata

  • EFCC ta taimaka wajen mika wasu ‘yan Najeriya biyu ga hukumomin Amurka domin fuskantar shari’a kan zargin cin zarafin yara ta intanet
  • Wadanda ake zargin, Mudashiru Afeez Olawale da Adebola Festus Adekunle, an mika su ga hukumomin Amurka ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2026
  • Binciken FBI ya alakanta lamarin da wasu matasa ‘yan Amurka da suka mutu ta hanyar kashe kansu bayan fuskantar zargin cin zarafi da kwace kudi ta intanet

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta taimaka wajen mika wasu ‘yan Najeriya biyu ga Amurka domin fuskantar shari’a.

Ana zargin yan Najeriyan ne da hannu a cikin cin zarafin yara ta intanet da karbar kudin fansa daga matasan kasar Amurka.

EFCC.
Hedkwatar hukumar EFCC da ke birnin tarayya Abuja Hoto: EFCC Nigeria
Source: Facebook

EFCC ta mika mutum 2 ga Amurka

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun harbe shugaban jam'iyyar APC, sun tafi da mutumin da suke tare

A sanarwar da ta wallafa a Facebook, EFCC ta bayyana sunan wadanda ake zargin, Mudashiru Afeez Olawale da Adebola Festus Adekunle.

Ta ce an mika su ga hukumomin Amurka ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2026, ta hannun ofishin EFCC na Lagos.

A cewar EFCC, ana zargin mutanen biyu da hannu a karbar kudin fansa ta hanyar barazana da hotunan batsa, inda suka fi kai taba yara maza masu shekaru tsakanin 13 zuwa 17.

Hukumar ta ce wadanda ake zargin sun yi amfani da hotunan cin zarafin yara ta hanyar lalata (CSAM) wajen yi wa wadanda abin ya shafa barazana tare da neman kudi daga gare su.

Binciken FBI ya alakanta mutanen biyu da wani lamari da ya shafi matasan Amurka da suka mutu ta hanyar kashe kansu bayan zargin fuskantar cin zarafin yada hotunan su ma batsa da kuma karbar kudade ta hanyar barazana a intanet.

Yadda yan Najeriya suka aikata laifi

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ce a daya daga cikin abubuwan da suka faru, wani yaro dan shekara 13 ya samu sakon kai tsaye a shafinsa na Instagram daga wani mutum da ya ba da shawarar musayar hotunan tsiraici.

Kara karanta wannan

Neja: Bayan umarnin Tinubu, an gano abin da yan sanda ke yi don ceto masallata da aka sace

Bayan samun hotunan, mutumin ya yi barazanar yada su ga mutanen da ke cikin jerin abokan yaron na Instagram matukar bai biya kudi ba.

Binciken FBI ya gano cewa tattaunawar ta ci gaba har bayan matashin ya bayyana cewa yana da niyyar kashe kansa.

Bayan gudanar da binciken, an kama Adekunle tare da gurfanar da shi a gaban EFCC.

EFCC.
Mutane 2 da hukumar EFCC ta mika wa Amurka kan zargin aikata laifin cin zarafin yara Hoto: EFCC Nigeria
Source: Facebook

Hadin gwiwar Najeriya da Amurka

EFCC ta ce mika mutanen biyu ya nuna yadda hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da na yaki da laifuka na Najeriya da Amurka ke kara karfi wajen yaki da laifukan da suka shafi kasashen duniya da kuma laifukan intanet.

Hukumar ta jaddada cewa hadin gwiwar da take da shi da FBI na da muhimmanci musamman wajen magance laifukan intanet da suka shafi cin zarafin yara da kuma karbar kudade ta hanyar barazana.

EFCC za ta masu bata bayanai lada

Kun ji cewa hukumar EFCC ta ce za ta bai wa masu tsegunta mata bayanan kadarorin da aka wawashe wani lada mai tsoka da za a dauko daga dukiyar.

EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ya ce za a bayar da ladan tsakanin kashi 2.5 zuwa 5 cikin 100 na dukiyar da aka kwato.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262