Wata Sabuwa: Saudi Arabia Ta Kafa Sabbin Ka'idojin Daukar Ma'aikata 'Yan Kasashen Waje
- Hukumar Saudi Arabia ta sauya tsarin bizar aiki da take bai wa sababbin kamfanoni na kasashen waje
- Dokar za ta shafi 'yan kasashen waje masu neman aiki sakamakon sababbin tsare-tsaren shirin Nitaqat
- Tsarin ya banbanta tsakanin kamfanonin da suka shafe shekaru biyu da kuma sababbin da aka kafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Riyadh, Saudi Arabia - Gwamnatin kasar Saudi Arabia ta fitar da sababbin ka'idoji game da adadin bizar aiki da take bai wa sababbin kamfanoni masu zaman kansu.
Wannan sabon tsari yana tafiya ne kaɗan-kaɗan bisa la'akari da shekarun da kamfani ya yi yana aiki gami da matsayinsa a shirin ‘Establishing Programme’ da tsarin 'Nitaqat' na kasar.

Source: Getty Images
Abin da sabuwar dokar ta kunsa
A tsarin da aka yi gyara a kansa, kamfanonin da ba su cika shekaru biyu da kafawa ba za su iya samun bizar aiki duka-duka har guda biyar ne kacal.
Ita kuwa ma'aikata ko kamfanonin da suka shafe sama da shekaru biyu suna gudanar da ayyukansu, suna da damar samun bizar aiki har guda 50.
Irin waɗannan kamfanoni za su iya neman bizar a lokaci guda ko kuma ta hanyar gabatar da buƙatu daban-daban a tsawon mako guda, rahoton Hindustan Times.
Matsayin tsarin "Establishing Programme" da Nitaqat
Ga kamfanonin da ke ƙarƙashin shirin 'Establishing Programme', da farko za a ba su damar samun bizar aiki guda biyu kacal.
Adadin bizar zai riƙa ƙaruwa ne kawai yayin da suke ci gaba a cikin shirin kuma suke samun shaida mai kyau a tsarin zaman Saudiyya na 'Nitaqat'.
Tsarin Nitaqat shi ne hanyar da gwamnatin kasar ke bi wajen rarraba ma'aikatu domin tabbatar da ana ɗaukar ɗan ƙasa aiki kafin 'yan ƙasashen waje.
Tasirin dokar ga 'yan ƙasashen waje
Hukumar kula da shige da fice ta Fragomen ta tabbatar da cewa waɗannan ka'idoji sababbi ne kuma ba su cikin tsarin da aka riƙa amfani da shi a baya.
Wannan sauyi zai shafi 'yan ƙasashen waje masu neman aiki a Saudi Arabia, musamman waɗanda ke neman samun gurbin aiki a ƙananan kamfanoni ko sababbin kafawa.
Domin haka, masana sun shawarci ma'aikatan ƙasashen ketare da su riƙa bincika matsayin kamfanin da tsarin Nitaqat dinsa kafin sanya hannu a kan kwangilar aiki.

Source: Getty Images
Kasashe irin Saudiyya na daya daga inda jama'a ke cincirindon zuwa domin samun damar aiki kasancewar ana samun saukin rayuwa.
Sai dai, a kan samu tsaiko wajen shiga da fice na 'yan kasashen waje, musamman wadanda ke zuwa daga kasashen Afrika.
'Yar Najeriya ta ci gasar karatun Al-Qur'ani a Saudiyya
A wani labarin kuma, kun ji yadda wata 'yar jihar Gombe a Najeriya ta lashe gasar hadatta littafi mai tsarki; Al-Qur'ani.
Rahotanni sun bayyana cewa, dalibar mai suna Maryam Ibrahim Dan'azumi ta zama ta daya ne a gasar yayin da ta doke adadin mutane da yawa daga sassa daban-daban na duniya.
Wannan gasa dai an ruwaito tana dauke da tukuicin makudan kudade, wadanda ake kyautata zaton sun haura Naira miliyan 100, kamar yadda majiya ta tabbatar.
Wanda ya tantance Salisu Ibrahim, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

