'Yar Jihar Gombe Ta Yi Zarra a Duniya, Maryam Ta Lashe Gasar Kur'ani a Saudi
- Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana farin cikinsa bayan Maryam Ibrahim Dan’azumi ta lashe gasar Al-Qur’ani ta duniya
- Maryam Dan’azumi ta wakilci Najeriya a gasar karo na 46, inda ta zama ta daya a bangaren haddar Al-Qur’ani gaba daya tare da tajwidi da tafsiri
- Gwamna Inuwa Yahaya ya ce zai karrama Maryam da kansa idan ta dawo Najeriya, yana mai cewa nasararta abin alfahari ne ga Gombe da kasa baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya taya Maryam Ibrahim Dan’azumi murnar zama wadda ta lashe gasar Al-Qur’ani ta kasa da kasa karo na 46 da aka gudanar a kasar Saudiyya.
Maryam, wadda daliba ce a makarantar Abubakar Siddiq da ke unguwar Herwagana a Gombe, ta wakilci Najeriya a babbar gasar da ta hada mahalarta daga kasashe daban-daban.

Source: Facebook
Sanarwar da kakakin gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya fitar a Facebook ta ce Maryam ta zama ta daya a gasar bayan ta yi fice a bangaren haddar Al-Qur’ani gaba daya, karatu, tajwidi da tafsiri.
Maryam Dan'azumi ta kafa tarihi
Nasarar Maryam Dan’azumi ta kasance ta musamman, domin an ce wannan ne karo na farko da mata suka samu damar shiga gasar tun bayan fara ta shekaru 46 da suka gabata.
Maryam ta yi nasara ne a bangaren haddar Al-Qur’ani mai girman izu 60 tare da tafsiri, inda ta zarce sauran mahalarta daga kasashe daban-daban.
Kafin wakiltar Najeriya a gasar da aka gudanar a Makkah, Maryam ta fara zama ta daya a matakin karamar hukumar Gombe, sannan ta lashe gasar jihar Gombe da kuma ta kasa baki daya.
Inuwa ya taya Maryan murna
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce nasarar Maryam ta nuna irin muhimmancin jajircewa, ladabi da dagewa wajen neman ilimi.

Kara karanta wannan
Abubuwan da ya dace a sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya
Ya ce nasarar ta kawo wa jihar Gombe da Najeriya daukaka a idon duniya, tare da nuna irin baiwa da basirar da matasan jihar ke da ita.
Gwamnan ya ce:
"Na yi matukar alfahari da wannan gagarumar nasara da 'yarmu ta samu a matakin duniya. Nasarar Maryam ta nuna irin kwarewa da kyakkyawan tarihin ilimi da jihar Gombe take da shi."
Inuwa Yahaya ya ce ya yi imanin cewa wannan nasara za ta zaburar da matasa da dama, musamman 'yan mata, wajen jajircewa domin samun daukaka a fannonin da suka zaba.
Gwamna zai karrama Maryam
Gwamna Inuwa Yahaya ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa ilimin matasa, ciki har da ilimin Al-Qur’ani da sauran karatun addini.
Ya ce irin wadannan nasarori suna taimakawa wajen gina tarbiyya, kyawawan halaye da kuma samar da matasa masu anfani ga al'umma.
Gwamnan ya ce yana fatan karbar Maryam da kansa tare da karrama ta idan ta dawo Najeriya, domin karfafa mata gwiwa da kuma zaburar da sauran matasa.
Ya kuma yaba da gudunmawar makarantar Abubakar Siddiq wajen horar da Maryam har ta kai wannan babban matsayi.

Source: Facebook
Malamai ba barazana a Gombe
A wani labarin, mun ruwaito cewa hadakar kungiyoyin ma’aikatan manyan makarantun jihar Gombe ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 14 domin magance matsalolin albashi, karin matsayi da sauransu.
Kungiyoyin sun yi gargadin cewa rashin daukar mataki mai ma’ana wajen warware matsalolin cikin wa’adin da suka bayar na iya jawo shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.
Hadakar ta ce duk da yabawa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya kan kokarin da take yi wajen tallafa wa ilimin manyan makarantu, har yanzu akwai muhimman batutuwan da ba a warware ba.
Asali: Legit.ng

