Faɗa Ya Kaure tsakanin Netanyahu da Wanda Ya ba Shi Wuta a Zaɓe kan Yaƙin Iran
- Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, na fuskantar saɓani da Gadi Eisenkot, wanda ake ganin zai iya maye gurbinsa, kan batun sake kai hare-hare Iran
- Eisenkot ya buƙaci Netanyahu da ya guji ɗaukar manyan matakan tsaro kafin kafa sabuwar gwamnati, yana mai gargadin haɗarin matakan da za a iya ɗagewa
- Ya kuma nemi Antoni Janar na Isra'ila ta tabbatar masa da samun bayanan sirri kan tsaro domin sa ido kan matakan gwamnatin riƙon kwarya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel – Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, na shirin fuskantar takaddama da Gadi Eisenkot, wanda ake kallon zai iya maye gurbinsa a matsayin sabon firaministan ƙasar, kan yiwuwar sake kai hare-hare Iran.
Eisenkot na fargabar cewa Netanyahu, wanda ke jagorantar gwamnatin riƙon kwarya, zai iya sake umartar kai hare-hare Iran bisa dalilan da ba su da inganci, domin ƙoƙarin ci gaba da riƙe madafun iko.

Kara karanta wannan
APC ta yi gyara a kwamitin kamfen din Tinubu bayan an yi abun kunya a idon duniya

Source: Getty Images
A cikin wata wasiƙa da ya aikewa Netanyahu ranar Laraba, Eisenkot ya buƙaci firaministan da kada ya ɗauki wasu manyan matakai da suka shafi tsaron ƙasa a wannan lokacin da ake sauyin gwamnati, cewar Bloomberg.
Ya kuma gargaɗe shi da ya guji ɗaukar matakan da ka iya jefa ƙasar cikin haɗari, musamman waɗanda za a iya jira har sai an rantsar da sabuwar gwamnati.
Eisenkot ya nemi sa hannun Antoni Janar
Haka kuma, Eisenkot ya buƙaci Gali Baharav-Miara, Antoni Janar ta Isra'ila, da ta taimaka wajen tabbatar da cewa yana samun bayanan sirri kan tsaron ƙasar a kai a kai.
A cewarsa, samun waɗannan bayanai zai taimaka masa wajen gudanar da ingantaccen sa ido kan matakan da gwamnatin riƙon kwarya ke ɗauka.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar sauyin siyasa a Isra'ila, inda batun tsaro da dangantakar ƙasar da Iran ke cikin muhimman abubuwan da za su iya tasiri kan sabuwar gwamnati.
Ƙarin bayani na tafe....
Ana shirin kafa gwamnati babu Netanyahu
Mun ba ku labarin cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi gargadin cewa haɗin gwiwar jam’iyyun adawa da Larabawa zai iya haddasa rugujewar ƙasar Isra’ila.
Jagoran adawa, Gadi Eisenkot, na ƙoƙarin haɗa kai da wasu jam’iyyun Yahudawa da Larabawa domin kafa sabuwar gwamnati.
Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya nuna cewa Eisenkot na samun goyon bayan ’yan majalisa fiye da Netanyahu wajen kafa gwamnati.
Asali: Legit.ng
