Trump Ya Ware Tukwicin Miliyoyin Dala kan Kwamandojin Iran, Ya Yi Albishir ga Mutane
- Amurka ta sanar da bayar da ladan miliyoyin dala ga duk wanda ya ba da bayanan manyan kwamandojin Rundunar Iran
- Shirin ya nemi bayanai kan manyan jami’an IRGC biyar da ake zargi da kai hare-hare kan Amurkawa da muhimman ababen more rayuwa
- Daga cikin wadanda ake nema akwai Ahmad Vahidi, Ali Abdollahi, Saeed Aghajani, Hamidreza Lashgarian da Majid Khademi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Kasar Amurka ta sanar da cewa za ta bayar da ladan har dala miliyan 10 kan wasu kwamandojin kasar Iran.
An ce za ta ba da tukuicin ne tare da yiwuwar sake matsuguni ga duk wanda ya samar da muhimman bayanai.

Source: Facebook
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana hakan ne ta shirin Rewards for Justice, wanda ke neman bayanai kan manyan kwamandojin Rundunar Kare Juyin Juya Hali ta Iran, cewar The Hill.
Amurka ta ba da tukuici kan kwamandojin Iran
Shirin ya nemi bayanai kan Ahmad Vahidi, kwamandan IRGC na Iran, da Ali Abdollahi, shugaban Babban Hedikwatar Khatam al-Anbiya.
Sauran wadanda ake nema sun hada da Saeed Aghajani, kwamandan rundunar jiragen sama marasa matuka ta IRGC, da Hamidreza Lashgarian.
Haka kuma, shirin na neman bayanai kan Majid Khademi, kwamandan Ofishin Leken Asiri na IRGC, wanda ke cikin manyan jami’an rundunar.
A cewar kasar Amurka, wadannan jami’ai ne ke jagorantar sassan IRGC da aka zargi kai hare-haren makamai kan jami’an Amurka da hare-haren yanar gizo.
Amurka ta bukaci mutane su taimaka wajen dakile barazanar ta hanyar gabatar da bayanan da za su taimaka wajen gano tare da dakile ayyukan wadannan jami’ai.

Source: Getty Images
Yawan adadin wadanda ba sa son aure, haihuwa
Kimanin mutane 100,000 ne suka halarci wani kuri’ar ra’ayi da Iran International ta gudanar a Instagram, inda tara cikin goma suka ce ba sa son aure ko haihuwa.

Kara karanta wannan
Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah
Mahalarta sun bayyana matsin tattalin arziki, rashin tabbas kan ayyukan yi, tsadar gidaje da damuwa game da makomar yara a matsayin manyan dalilan matsayar.
Fiye da mutane 12,000 sun kuma yi tsokaci, inda wasu suka ce suna son aure ko haihuwa amma ba su da damar tattalin arziki, cewar rahoton A News.
Wasu kuma sun danganta rashin son aure da matsalolin saki, rashin nasarar aure da kuma wahalar samun abokin rayuwa da ya dace.
Maza sun kasance kashi 68 cikin 100 na mahalarta, yayin da mata suka kasance kashi 32 cikin 100 na wadanda suka shiga kuri’ar.
Mafi yawan mahalarta suna tsakanin shekaru 25 zuwa 34, wadanda suka kai kashi 40.3 cikin 100, sai masu shekaru 35 zuwa 44 da kashi 29.2.
Masu shekaru 18 zuwa 24 sun kasance kashi 13.3 cikin 100, yayin da wadanda ke tsakanin shekaru 45 zuwa 54 suka kai kashi 9.8.
Trump ya ɗauki matakin rusa Iran
An ji cewa Amurka ta ƙaddamar da wani sabon shirin matsin tattalin arziki kan Iran, tare da shirin katse hanyoyin samun kuɗin gwamnatin Tehran.
Ministan Baitul Malin Amurka, Scott Bessent, ya ce za su yi amfani da takunkumi wajen hana ƙasashe da kamfanoni ci gaba da hulɗa da Iran.
Iran ta yi watsi da sabon shirin na Amurka, yayin da ministan harkokin wajenta, Abbas Araghchi, ya ce takunkumin tattalin arziki ba sabon abu ba ne.
Asali: Legit.ng

