Kanada Za Ta Shigo Najeriya da Wasu Kasashe Ta Dauki Ma'aikata, Abubuwan da Ake Bukata Sun Fito
- Kasar Kanada na shirin daukar ma’aikata 230,000 daga kasashe daban-daban a 2026, ciki har da ’yan Najeriya
- Hakan dai ya biyo bayan wasu sauye-sauye da gwamnatin Kansda ta yi wanda zai ba ta damar ɗaukar ƙarin ma’aikatan wucin gadi daga ƙasashen waje
- ’Yan Najeriya za su buƙaci samun sahihin aiki da kuma mai ɗaukar aiki a Kanada kafin neman izinin aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Canada - Kasar Kanada na shirin daukar ssbabbin ma’aikatan ƙasashen waje 230,000 a shekarar 2026, ciki har da ’yan Najeriya da ke neman damar aiki a ƙasar.
Gwamnatin Kanada ta gabatar da sauye-sauye da za su iya bai wa wasu masu ɗaukar ma’aikata damar ɗaukar ƙarin ma’aikata daga ƙasashen waje na wucin gadi.

Source: Getty Images
Vanguard ta ce adadin ya ƙunshi ma’aikata 60,000 ta Shirin Ma’aikatan Ƙasashen Waje na Wucin Gadi (TFWP) da wasu 170,000 ta Shirin Motsi na Ƙasashen Duniya (IMP), a ƙarƙashin tsarin matakan shige da fice na Kanada na 2026.
Sabon sauyin ya shafi masu ɗaukar ma’aikata da ke gudanar da ayyukansu a ƙananan wuraren aiki da dama, kuma hakan na iya ƙara samar da damar aiki ga ’yan ƙasashen waje a fannonin da TFWP ya shafa.
Sabon sauyin na iya amfanar kasuwancin da ke da ƙananan wuraren aiki da dama, waɗanda a baya ke fuskantar takura wajen ɗaukar ma’aikatan ƙasashen waje ta tsarin ma’aikatan masu ƙaramin albashi.
Masu ɗaukar ma’aikata a kasar Kanada da ke son ɗaukar ma’aikata ta TFWP galibi dole ne su samu sakamakon Labour Market Impact Assessment (LMIA) mai kyau ko tsaka-tsaki daga ESDC.
Ana amfani da LMIA wajen nuna cewa mai ɗaukar aikin bai samu ɗan ƙasar Kanada ko wanda ke da izinin zama na dindindin da ya dace da aikin ba.
Bayan mai ɗaukar aikin ya samu amincewar da ake buƙata, ma’aikacin ƙasar waje zai iya ci gaba da neman izinin aiki.
Yadda ’yan Najeriya za su nema
’Yan Najeriya masu sha’awar yin aiki a Kanada ta TFWP ya kamata su fara neman sahihin kanfanin da ke neman ma'aikata a Kanada kafin su cike neman aikin.
Ga tsarin da ake bi gaba ɗaya:
1. Nemo aikin da ya cancanta a Kanada
Duk dan Najeriya da ke neman aikin yana buƙatar sahihiyar takardar tayin aiki daga wani kamfani ko dan kasuwsar Kanada da ke son ɗaukar ma’aikatan ƙasashen waje.
2. Mai ɗaukar aiki ya nemi LMIA
Duk wani kamfani ko dan kasuwa a Kanada zai nemi LMIA daga ESDC idan ana buƙatar hakan. Dole ne ya nuna cewa aikin ya cika ƙa’idojin da suka dace kuma akwai buƙatar ɗaukar ma’aikacin ƙasar waje.
3. Samun LMIA mai kyau ko tsaka-tsaki
Idan an amince da buƙatar, mai daukar aikin zai bai wa ma’aikacin takardun da ake buƙata domin neman izinin aiki.
4. Neman izinin aiki a Kanada
Daga nan ma’aikacin ƙasar waje ciki har da dan Najeriya zai nemi izinin aiki tare da gabatar da takardun da ake buƙata, ciki har da bayanan aikin da kuma na mai ɗaukar aikin a Kanada.
5. Cika sharuɗɗan cancanta na Kanada
Masu neman izinin aiki dole ne su cika ƙa’idojin shige da fice na Kanada, waɗanda za su iya haɗawa da tabbatar da cewa sun cancanci aikin da aka ba su da kuma cika sauran sharuɗɗan kiwon lafiya, tsaro da makamantansu.
Hukumar Kwastam ta fitar da sunaye
A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar Kwastam ta Najeriya ta fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasara a daukar ma'aikatan ASC II na shekarar 2024/2025.
An umurce mutane da su shiga shafin da hukumar ta tanada ta amfani da Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN) ko adireshin imel da suka yi rajista da shi.
Asali: Legit.ng


