Amurka ta bukaci Najeriya ta saki mawakin Kano da aka yanke wa hukuncin kisa
- Gwamnatin Amurka ta bukaci gwamnatin tarayya ta saki mawakin nan na jihar Kano, Yahaya Sharif-Aminu, wanda aka tsare tun 2020
- Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Amurka, Riley Barnes, ya ce kasarsa na tattaunawa da hukumomin Najeriya domin ganin an saki mawakin
- An dai kama mawakin tre da yanke masa hukuncin kisa ne bisa laifin batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Gwamnatin Amurka ta bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya ta saki mawakin darika, Yahaya Sharif-Aminu, wanda ya shafe shekaru a gidan yari tun 2020.
Ana tsare da mawkain ne bayan wata kotun Shari’a ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa zargin batanci.

Source: Getty Images
Amurka ta nemi a saki Yahaya Sharif-Aminu
Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Amurka mai kula da Dimokuradiyya, Hakkokin Dan Adam da Kwadago, Riley Barnes, ya bukaci gwamnatin Najeriya ta sake shi.
Ya yi wannan kira a ranar Alhamis yayin wani zaman sauraron ra’ayoyi na karamin kwamitin Afirka kan harkokin wajen Majalisar Wakilan Amurka.
Barnes ya ce Amurka na matsa wa hukumomin Najeriya lamba domin ganin an saki mawakin tare da kawo karshen aiwatar da dokokin batanci ga addini.
“Muna ci gaba da matsa wa gwamnatin Najeriya lamba, muna kuma kira da a saki mawakin sufi, Yahaya Sharif-Aminu, wanda ke fuskantar hukuncin kisa saboda zargin batanci ga addini.
"Haka kuma muna ci gaba da kira ga gwamnati da ta dakatar da aiwatar da dokokin batanci,” in ji shi.
Ya kuma soki gurfanar da ’yan Najeriya bisa zargin batanci ga addini, ciki har da shari’o’in da suka shafi bayyana ra’ayi cikin lumana.
Barnes ya ce:
“Jami’an jihohi na ci gaba da gurfanar da mutane bisa zargin batanci ko kalaman da ake ganin sun zagi Musulunci, ciki har da bayyana ra’ayi cikin lumana. Wannan ya saba wa wajibcin Najeriya na kare ’yancin fadin albarkacin baki da ’yancin addini.”

Kara karanta wannan
Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta
Amurka ta bukaci daukar karin matakai
Zaman sauraron ra’ayoyin, mai taken “Shekara Daya Bayan Nan: Tantance Kokarin Najeriya na Kare Kiristoci da Samar da Tsaro a Yankin Middle Belt”, ya mayar da hankali kan matakan da Najeriya ke dauka wajen magance rashin tsaro.
An gudanar da zaman ne kusan shekara guda bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ayyana Najeriya a matsayin kasa da ke bukatar kulawa ta musamman kan batun ’yancin addini.
A yayin zaman, Barnes ya bukaci Najeriya ta kara kaimi wajen dakile hare-hare da kuma tabbatar da cewa ’yan gudun hijira sun samu damar komawa cikin aminci zuwa al’ummominsu.
Ya ce Amurka za ta ci gaba da tantance kokarin Najeriya bisa raguwar hare-hare da kuma gurfanar da wadanda ke da alhakin aikata tashe-tashen hankula.
An kama Sharif-Aminu ne a watan Maris na 2020 bayan ya wallafa wasu baitocin waka da ya rubuta ta manhajar WhatsApp. An dauki baitocin a matsayin kalaman batanci ga Annabi SAW da ma Musulunci baki daya.
Kun ji cewa
Asali: Legit.ng
