Gwamnatin Najeriya Ta Tsoma Baki a Yakin Gaza da Isra'ila

Gwamnatin Najeriya Ta Tsoma Baki a Yakin Gaza da Isra'ila

  • Gwamnatin Najeriya ta bukaci Isra'ila da Gaza su tabbatar da an aiwatar da matakan yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Kasar ta kuma goyi bayan mafita ta kasashe biyu a matsayin hanyar samar da zaman lafiya mai dorewa tsakaninsu
  • Gwamnatin Bola Tinubu ta shawarci Qatar, Misira da Amurka da su ci gaba da bibiya da sa ido don kammala yarjejeniyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnatin Najeriya ta bukaci Isra’ila da Gaza su tabbatar da cikakken aiwatar da mataki na biyu da na uku na yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla tsakanin bangarorin biyu.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar ta ce Najeriya tana goyon bayan mafita ta kasashe biyu a matsayin hanyar samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin kasashen.

Kara karanta wannan

Kudiri yayi nisa a majalisa, Gwamna Abba zai kafa hukumar tsaro mallakin jihar Kano

Tinubu
Gwamnatin Najeriya ta yabi yarjejeniyar tsagaita wuta Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

NTA ta ruwaito cewa Najeriya ta yaba da yarjejeniyar tsagaita wutar ta da za ta kawo karshen salwantar rayukan fararen hula, wanda su ka hada da mata da dattawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna Gaza da ke Falasɗinu sun shafe akalla watanni 15 Isra'ila ta na zazzaga mata ruwan bama-bamai babu kakkautawa, inda ya raba dubban Falasɗinawa da gidajensu.

Gaza/Isra'ila: Najeriya ta jinjina tsagaita wuta

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Najeriya ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila sassauci ne ga iyalan Isra’ilawan da ke hannun Hamas a Gaza.

Haka kuma ana sa ran hakan zai kawo sauki wasu daga cikin Falasdinawa da ke tsare a gidajen yari na Isra’ila na tsawo shekaru, duk da wasu sun rasa rayukansu a daure.

Najeriya ta yaba da samun damar isar da kayan agaji da tallafi ga al’ummar yankin da wannan yarjejeniya ta ba dama da Isra'ila ta hana samun kowane irin tallafi a baya.

Kara karanta wannan

Najeriya na fuskantar barazanar Trump, Amurka ta toshe tallafin lafiya

Najeriya ta yaba wa Misira, Qatar da Amurka

Gwamnatin Najeriya ta jinjinawa Misira, Qatar, da Amurka saboda kokarinsu na cimma yarjejeniyar tsagaita wutar duk da tsaiko da aka rika samu, musamman a kan yarjejeniyar.

Gwamnatin Bola Tinubu ta yi fatan kasashen za su ci gaba da kasancewa masu lura da aiwatar da yarjejeniyar da aka sha wahala kafin Hamas da Isra'ila su amince da sanya hannu a kai.

Kasashen sun yi ta kai da kawowa a teburin sulhu domin tabbatar da tsagaita wuta a Gaza da ta fuskanci kisan kiyashi cikin watanni 15 da suka gabata, ciki har da jarirai.

Isra'ila, Hamas sun cimma yarjejeniya tsagaita wuta

A baya mun ruwaito cewa bayan rikici mai tsawo da ya yi sanadiyar salwantar rayuka da barnata dukiyoyi a yankin Gaza, Isra’ila da kungiyar Hamas sun amince da tsagaita wuta.

Wannan yarjejeniya, wadda aka kulla karkashin kulawar kasashen duniya, na da nufin kawo sassauci ga miliyoyin fararen hula, musamman a Gaza da ke fama da rikici a yankin.

Kara karanta wannan

Shettima ya bugi kirji a kan rashawa, ya ce za a magance matsalolin Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa an tsara yarjejeniyar a matakai uku, inda matakin farko ya hada da dakatar da duk wani farmaki daga bangarorin biyu domin kawo karshen yakin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.