Abu Ya Girma: Gwamna Ya Dakatar da Sarki Mai Martaba, Ya Kafa Kwamitin Mutum 12

Abu Ya Girma: Gwamna Ya Dakatar da Sarki Mai Martaba, Ya Kafa Kwamitin Mutum 12

  • Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya dakatar da Alhaji Aliyu Lame, Sarkin Lame da ke ƙaramar hukumar Toro
  • Gwamnan ya kuma kafa kwamitin bincike mai mambobi 12 domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa basaraken
  • An bai wa kwamitin makonni uku domin gudanar da bincike tare da miƙa rahotonsa da shawarwarinsa ga gwamnatin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi – Gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da Alhaji Aliyu Lame, Sarkin Lame da ke ƙaramar hukumar Toro, sakamakon zarge-zargen aikata ba daidai ba da ake yi masa.

Gwamnatin ta kuma amince da kafa kwamitin gudanar da bincike mai mambobi 12 domin bincikar zarge-zargen da ake yi wa basaraken.

Gwamna Bala.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed a gidan gwamnatinsa Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed
Source: Twitter

Daily Trust ta ce hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mukhtar Gidado, mai ba gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, shawara kan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, ya fitar ranar Asabar a Bauchi.

Kara karanta wannan

2027: Gwamna ya ce nasarorin da ya samu za su taimaka masa wajen zama shugaban ƙasa

Zarge-zargen da ake wa basaraken

A cewarsa, gwamnan ne ya amince da matakin bayan samun ƙorafe-ƙorafe a hukumance da rahotannin sirri daga shugabannin al'umma, masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro.

Mukhtar Gidado ya bayyana cewa zarge-zargen sun haɗa da shiga harkokin filaye ba bisa ƙa'ida ba, karɓar haraji ba tare da izini ba, tsoma baki a ayyukan kamfanonin haƙar ma'adinai da sauran zarge-zargen aikata ba daidai ba.

Ya ƙara da cewa waɗannan ayyukan da ake zargin basaraken da aikatawa sun haifar da tashin hankali a masarautar Lame tare da jawo fargaba kan zaman lafiya da tsaron jama'a.

Dalilin dakatar da Sarkin Lame

Ya ce:

"Ma'aikatar ƙananan hukumomi da harkokin masarautu ta nemi basaraken ya yi bayani kan zarge-zargen tun da farko, inda ya miƙa amsoshinsa a rubuce.
"Sai dai gwamnatin ta yi la'akari da bayanan da ya bayar, ta kuma gamsu cewa ba su wadatar ba, don haka ta ga ya zama dole a gudanar da bincike mai zaman kansa."

Kara karanta wannan

Za a yi fadan cikin gida a kotu, gwamnati ta kai shugaban kwastam kara gaban alkali

Kakakin gwwmnan ya bayyana cewa kwamitin da aka kafa na ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin sufeto-janar na rundunar 'yan sanda, Sani Mohammed.

Kwamitin ya ƙunshi wakilan hukumomin tsaro, ma'aikatun da abin ya shafa, ƙaramar hukumar Toro da sauran hukumomin gwamnati.

Wa'adin da aka ba kwamitin bincike

Gidado ya ce an bai wa kwamitin makonni uku domin gudanar da bincike kan zarge-zargen, nazarin takardun da suka dace, gayyatar waɗanda abin ya shafa da kuma miƙa sakamakon bincike da shawarwarinsa ga gwamnati.

Mai magana da yawun gwamna ya ƙara da cewa dakatarwar mataki ne na gudanarwa da aka ɗauka domin kare sahihancin binciken tare da hana yiwuwar tsoma baki wajen shaidu da takardun hukuma.

Ya ce gwamnati ta buƙaci mazauna masarautar Lame da ƙaramar hukumar Toro, shugabannin al'umma, masu riƙe da sarautun gargajiya da matasa da su kwantar da hankalinsu, su zauna lafiya tare da bin doka da oda.

Sarakuna 19 sun fara mulki a Zamfara

Kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal ya miƙa sandar mulki ga Sarkin Gusau na 16, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello II, tare da wasu sarakuna 18 a Zamfara.

Gwamnan ya buƙaci sarakunan gargajiya su haɗa kai da gwamnati wajen dawo da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262