Zuwan Bola Tinubu Jos, an Tsaurara Jami'an Tsaro a Dukan Lungu da Saƙo
- An girke jami’an tsaro sosai a wasu muhimman wurare a Jos gabanin ziyarar Shugaba Bola Tinubu domin halartar gangamin APC na shiyyar Arewa ta Tsakiya
- Tinubu zai halarci gangamin yakin neman zaben APC a filin wasa na Zaria Road, tare da kaddamar da manyan ayyukan raya kasa guda uku
- Gwamna Caleb Mutfwang ya ce cibiyar BPO za ta samar da guraben ayyukan yi 2,400, yayin da motocin bas 50 za su inganta sufuri a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau – An tsaurara matakan tsaro a Jos, babban birnin jihar Plateau, gabanin isowar Shugaba Bola Tinubu a ranar Asabar.
Tinubu zai shiga Jos ne domin halartar gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a shiyyar Arewa ta Tsakiya.
Wakilin jaridar Vanguard da ya zagaya wasu sassan birnin ya lura da yadda aka jibge jami’an tsaro a muhimman wurare domin tabbatar da tsaro gabanin ziyarar shugaban kasar.

Kara karanta wannan
An yi arangama da 'yan daba suka kai hari wurin taron magoya bayan Obi da Kwankwaso
Daga cikin wuraren da aka girke jami’an tsaron akwai Hill Station Junction, Zaria Road, Polo Roundabout da wasu sassan Yakubu Gowon Way.
Ayyukan da Tinubu zai kaddamar a Plateau
Ana sa ran Tinubu zai halarci gangamin APC da za a gudanar a filin wasa na Zaria Road da ke Jos.
Haka kuma, shugaban kasar zai kaddamar da manyan ayyukan raya kasa guda uku da gwamnatin jihar Plateau ta aiwatar.
Ayyukan sun hada da cibiyar samar da ayyukan yi ta hanyar fasahar zamani (BPO Centre) da ke Jos, cibiyar ayyukan tsaro ta musamman ta Plateau (P-SAC) da kuma motocin bas masu amfani da makamashi iri biyu guda 50.
Gabanin ziyarar shugaban kasar, Gwamna Caleb Mutfwang, shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda da tsohuwar mataimakiyar gwamna, Dame Pauline Tallen, sun duba ayyukan.
Cibiyar BPO za ta samar da ayyukan yi 2,400
Da yake magana kan cibiyar BPO, Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa aikin wata muhimmiyar zuba jari ce wajen bunkasa ilimi da kwarewar matasa, samar da ayyukan yi da inganta tattalin arziki.
A cewar wata sanarwa da daraktan yada labaransa, Gyang Bere, ya sanya wa hannu, cibiyar ta samo asali ne daga hadin gwiwar gwamnatin Plateau, kamfanin Outsource Global da MTN Nigeria.
Sanarwar ta bayyana cewa cibiyar tana da karfin daukar ma'aikata 800, kuma ana sa ran za ta samar da ayyukan yi na dindindin guda 2,400 idan aka fara gudanar da ayyukanta cikin cikakken tsari na sauye-sauye uku a rana.
Gwamnan ya ce cibiyar za ta bai wa matasan Plateau damar shiga harkokin tattalin arzikin duniya ta hanyar ayyukan kula da kwastomomi, tallafin fasaha da sauran ayyukan ofis.
Ya kara da cewa matasan za su iya yi wa kungiyoyin kasa da kasa aiki daga Jos tare da samun albashinsu a kudaden kasashen waje.
Sabuwar cibiyar tsaro da motocin bas 50
Game da cibiyar ayyukan tsaro ta musamman ta Plateau, Mutfwang ya ce an kafa ta ne domin karfafa ayyukan tsaro da suka dogara da tattara bayanan sirri.
Ya jaddada cewa tsaro na daga cikin muhimman abubuwan da ake bukata domin samun ci gaba mai dorewa.
Cibiyar ta kunshi sashen tattara da nazarin bayanan sirri, sashen Geo-Intelligence/GIS, sashen jiragen sama marasa matuki (Drones), cibiyar horaswa da dakin tantance bayanai.
A cewarsa, wadannan sassa za su taimaka wajen tattara bayanan sirri, gano barazanar tsaro, nazari da kuma tsara matakan dakile matsalolin tsaro.
Haka kuma, gwamnan ya ce motocin bas masu amfani da makamashi iri biyu guda 50 za su inganta zirga-zirgar jama'a, rage kudin sufuri da saukaka tafiye-tafiye tsakanin kananan hukumomi 17 na jihar.
APC na sa ran samun dimbin magoya baya
Yayin da yake duba filin wasan Zaria Road da za a gudanar da gangamin, Mutfwang ya bayyana kwarin gwiwar cewa za a samu dimbin magoya bayan APC da masu ruwa da tsaki daga yankin Arewa ta Tsakiya.
Ya bukaci al'ummar jihar su fito da yawa domin tarbar Tinubu, wanda ya bayyana a matsayin jagoran kasa mai kishin ci gaba da tsaron Plateau.
A nasa bangaren, shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya yabawa gwamnan da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa bisa yadda suka tsara shirye-shiryen taron.
Yilwatda ya ce ya gamsu da shirye-shiryen da aka yi kan filin taron, tsaro, harkokin filin jirgin sama da kuma kula da zirga-zirgar ababen hawa.
Ya ce:
"Shirye-shiryen sun yi kyau matuka, kuma na gamsu da abin da na gani dangane da shirya filin taron, tsaro, filin jirgin sama, tsara tituna da sauran abubuwa. Komai ya yi kyau. Ina sa ran gobe za ta kasance abin mamaki a Plateau."
Yilwatda ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa APC za ta samu gagarumin goyon baya ga Tinubu, yana mai danganta hakan da karuwar karfin jam'iyyar da shigar tsofaffin gwamnoni, mataimakan gwamnoni, shugabannin majalisu da sauran manyan 'yan siyasa.
Ƙarin bayani na tafe ....
Asali: Legit.ng


