Jerin Duka Alkawura 120 da Bola Tinubu Ya Dauka, Ya Sha Alwashi Zai Yi a Wa'adi na 2

Jerin Duka Alkawura 120 da Bola Tinubu Ya Dauka, Ya Sha Alwashi Zai Yi a Wa'adi na 2

Abuja - APC ta bayyana sabon tsarin manufofi mai ginshiƙai huɗu, wanda ya ƙunshi manufofin Bola Ahmed Tinubu da ke kujerar mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima wajen kamfe a Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Shugaba Bola Tinubu yana neman karin wa'adi

Idan Mai girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu wa’adi na biyu a mulki a zaben baɗi, ana sa ran zai yi waɗannan ayyuka su kimanin 130.

Punch ta ce tsarin ya ƙunshi alkawuran magance matsalar tsaro, rage tsadar rayuwa, bunƙasa abubuwan more rayuwa daga 2027 zuwa 2031.

Takardar mai taken Renewed Hope Agenda 2.0, ta tattara manufofin gwamnatin Tinubu mai ginshiƙai guda takwas zuwa manyan ginshiƙai huɗu.

Alƙawuran da Bola Tinubu ya yi a 2027

A ƙarƙashin waɗannan ginshiƙai, APC ta bayyana aƙalla alkawura sama da 120 kamar yadda aka gani.

A. DAWO DA ZAMAN LAFIYA

Kara karanta wannan

Barakar cikin kungiyar dattawan Arewa ta kara munana ana saura kwanaki zabe

  1. Kammala gina sabbin rundunonin sojoji huɗu da samar musu da kayan aiki a Makurdi, Ilorin, Jalingo da Benin da ƙarin jami’an soja 28,000 da aka amince da ɗauka kuma a tura su bakin aiki.

2. Ƙarfafa shirye-shiryen miƙa wuya da gyaran halin tsofaffin ‘yan ta’adda, tare da tabbatar da gaskiyar bayanan waɗanda aka karba.

3. Samar da rundunonin musamman na yaƙi da ta’addanci a shiyyoyi, tare da ƙarfafa tsaron makarantu, kasuwanni, wuraren ibada da manyan hanyoyi.

4. Faɗaɗa shirye-shiryen samar da zaman lafiya, taimakon waɗanda suka fuskanci matsaloli da yaƙi da tsattsauran ra'ayi

5. Sama da rundunar ’yan sanda da jama’a za su gani, su amince da ita.

6. Horar da sababbin ’yan sanda 50,000 tare da tura su aiki.

7. Aiwatar da shirin gyaran rundunar ’yan sanda ta hanyar amfani da fasahar zamani/

8. Mayar da aikin tsaro zuwa wasu wurare na musamman daga ’yan sanda zuwa rundunar NSCDC.

9. Yin aiki da Majalisar Tarayya, majalisun dokokin jihohi da gwamnoni domin samar da dokokin kafa rundunonin ’yan sanda na jihohi da na al’umma.

Kara karanta wannan

Muhammed Idris ya lissafo hanyoyin da kowane ɗan Najeriya ke amfana da mulkin Tinubu

10. Kammala amfani da na’urorin sa ido na zamani a dukkan wuraren da aka tsara na kan iyakokin ƙasa.

11. Faɗaɗa aikin rundunar Mining Marshals domin kare dukkan wuraren haƙar ma'adinai da aka gano.

12. Tura jami’an Forest Guards, Agro-Rangers da Mining Marshals domin kare gonaki, gonaki, labi, dazuzzukan gwamnati da wuraren ma'adinai.

13. Aiwatar da cikakken tsarin kare muhimman kadarorin ƙasa, tare da sanya na’urorin sa ido a bututun mai, tashoshin wutar lantarki, layukan dogo, makarantu da asibitoci.

14. Faɗaɗa kera harsasai, kayan kariya, motocin yaƙi da jirage marasa matuƙa a cikin Najeriya.

15. Gina haɗaɗɗun cibiyoyin sadarwa da tattara bayanan sirri domin gano barazana da wuri da kuma daukar matakin gaggawa.

16. Ƙarfafa binciken kimiyya da fasahar tsaro, tare da yin yarjejeniyar musayar fasaha da haɗin gwiwa da kamfanoni da ƙasashen duniya.

17. Aiwatar da ƙarin albashin jami’an tsaro da aka amince da shi, tare da ƙara alawus na aiki da samar musu da gidaje, kiwon lafiya da tallafin karatu ga iyalansu.

18. Gaggauta biyan kuɗin inshora da fansho ga waɗanda suka cancanta, tare da tabbatar da kula da iyalan jami’an tsaron da suka mutu a bakin aiki da tallafa wa karatun ’ya’yansu.

Kara karanta wannan

Bidiyon minista tana raba ɗauri ɗaurin N100,000 ya tada kura, mutane sun dura kanta

19. Kammala gyaran barikin ’yan sanda da gidajen jami’an tsaro da suka lalace.

20. Samar da horo na zamani da taimakon lafiyar kwakwalwar jami’an tsaro.

21. Faɗaɗa hanyoyin hukunta masu ƙananan laifuffuka ba tare da tsare su a gidan yari ba, tare da horar da su sana’o’i domin rage cunkoson gidajen gyaran hali.

22. Zamantar da wuraren kashe gobara, kayan aikin jami’an kwana-kwana kuma a faɗaɗa ayyukansu zuwa dukkan ƙananan hukumomi.

23. Inganta sa ido a teku, tsaron yanar gizo, hanyoyin sadarwar gaggawa da jirage marasa matuƙa domin gano haɗurra da gudanar da ayyukan ceto.

24. Yi wa kashi 95% na ’yan ƙasa da mazauna rajista a ma'ajiyar bayanan shaidar ɗan ƙasa

25. Haɗa sauran ma'ajiyar bayanai da hukumomi cikin babban tsarin shaidar ɗan ƙasa.

26. Kare sirrin bayanan jama’a tare da amfani da tsarin tantance mutum ta hanyar zanen yatsa da sauran bayanan halittarsa domin yaƙi rashin gaskiya.

B. INGANTA RAYUWA DA RAGE TSADAR KAYAYYAKI

Kara karanta wannan

Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya, ya fadi shirinsa kan kawo karshen rashin tsaro

1. Faɗaɗa shirin HOPE-EDU a duk faɗin ƙasar domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta

2. Ɗaukar ƙarin malamai 20,000 da horar da su, tare da ba da fifiko ga mata da al’ummomin karkara da ba su da isassun malamai.

  1. Ƙarfafa tsaron makarantu, samar da ruwan sha da tsaftar muhalli
  2. Mayar da hankali kan ilimin matakin farko, kimiyya, fasaha, injiniyanci, lissafi da ƙwarewar amfani da na’urorin zamani
  3. Ƙarfafa haɗin gwiwa da kamfanoni domin ba ɗalibai horon aikace-aikace da ya dace da ayyukan yau.
  4. Faɗaɗa shirin NELFUND, National Smart Learning Initiative da tallafin jari ga ɗaliban da ke son kafa sana’o’i
  5. Faɗaɗa koyon sana’o’i da fasahar zamani.
  6. Faɗaɗa shirye-shiryen wasanni a makarantu, tare da bunƙasa shirin N-SEEP zuwa dukkan jihohi.
  7. Faɗaɗa asibitocin shan magani
  8. Ci gaba da shirye-shiryen kula da mata masu juna biyu, jarirai, rigakafi da gano cututtukan daji tun da wuri.
  9. Ƙara yawan mutanen da ke da inshorar lafiya
  10. Kammala gyaran kusan asibitocin shan magani 1,000 da ake kan aikin gyarawa
  11. Kammala tsarin tattara bayanan kiwon lafiya na ƙasa domin tabbatar da samun bayanan marasa lafiya ta hanyar kwamfuta kafin 2031.
  12. Ɗaukar ma’aikatan lafiya, horar da su da inganta jin daɗinsu.
  13. Aiwatar da cikakken tsarin samar da ayyukan yi ga matasa
  14. Faɗaɗa horar da matasa miliyan biyu, tare da faɗaɗa shirin Digital Literacy for All zuwa mutane miliyan 30.
  15. Faɗaɗa rancen NEXTGEN Bank, Nigeria Youth Investment Fund da YouthCred, tare da samar da dokar kafa bankin matasa.
  16. Faɗaɗa shirye-shiryen tallafin kuɗi da rance ga ’yan bautar ƙasa da matasa masu ƙirƙire-ƙirƙire domin su kafa sana’o’insu.
  17. Faɗaɗa cibiyoyin tallafa wa ƙananan sana’o’i da cibiyoyin horas da masu son kafa kamfanoni.
  18. Kammala nazarin farko na shirin NYSC a tarihinsa na shekaru 53, domin mayar da shi shiri mai dogaro da koyon ƙwarewar aiki da sana’o’i.
  19. Tabbatar da cewa mata sun samu aƙalla 35% na mukamai a majalisar ministoci mai zuwa da manyan ma’aikatun gwamnati.
  20. Faɗaɗa shirin rancen kuɗi na GLOW da kuma shirin Nigeria for Women zuwa dukkan jihohi 36.
  21. Yin aiki da Bankin Raya Najeriya da sauran cibiyoyin kuɗi domin samar wa mata ’yan kasuwa sauƙin samun rance.
  22. Samar da cibiyoyin kai rahoton cin zarafin mata da yara da wuraren ba da mafaka da shawarwari a dukkan jihohi, tare da gaggauta gurfanar da masu laifi.
  23. Kammala tantance rajistar tallafin jama’a ta ƙasa ta hanyar NIN.
  24. Aiwatar da shirin HOPE-SP mai kuɗin dalar Amurka biliyan ɗaya
  25. Faɗaɗa tallafin jin daɗin jama’a ga yara, tsofaffi, masu nakasa da iyalai marasa ƙarfi.
  26. Aiwatar da dokar hana nuna wariya ga masu nakasa, domin tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati, makarantu, sufuri da wuraren aiki sun dace da bukatunsu.
  27. Tabbatar da aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N70,000 a duk faɗin ƙasar
  28. Aiwatar da tsarin ƙaura domin neman aiki na shekarun 2027 zuwa 2031, tare da kare haƙƙin ’yan Najeriya da ke aiki bisa doka a ƙasashen waje.
  29. Daidaita farashin kayan abinci ta hanyar shirin Guaranteed Minimum Price
  30. Rage ɓarnar amfanin gona da kuɗin da ake kashe wa wajen jigilar abinci daga gona zuwa kasuwa
  31. Rage kuɗin jigilar abinci ta hanyar amfani da iskar gas ta CNG, hanyoyin mota, jirgin ƙasa da tashoshin jiragen ruwa.
  32. Samar da tallafin abinci mai gina jiki ga yara da mata ta makarantu da asibitocin farko, tare da faɗaɗa shirin ciyar da ɗalibai.
  33. Ƙarfafa ƙa’idojin tabbatar da lafiyar abinci a masana’antu, kasuwanni da wuraren fitar da kaya zuwa ƙasashen waje.
  34. Kammala aiwatar da dokokin kula da rancen kuɗi ta hanyoyin zamani
  35. Ƙarfafa kare haƙƙin masu amfani da bankuna da kamfanonin fasahar kuɗi
  36. Ƙarfafa kotun sauraron ƙararrakin gasar kasuwanci da kare masu sayayya domin ta riƙa yanke hukunci cikin lokaci.
  37. Faɗaɗa sa ido kan farashin abinci, mai, magunguna da sauran kayan masarufi. 9. Za mu samar da gidajen jama’a masu araha, rancen gidaje da takardun mallakar filaye
  38. Kammala gina gidajen Renewed Hope Cities and Estates sama da 15,000
  39. Ƙara jarin MREIF zuwa Naira tiriliyan ɗaya domin samar da rancen gidaje na shekaru 20. Haka kuma, ƙara adadin rancen da FMBN ke bayarwa daga Naira miliyan 50 zuwa miliyan 85.
  40. Fara shirin Land4Growth domin samar da takardun mallakar filaye na zamani
  41. Faɗaɗa hanyoyin samun gidaje ta hanyar tsarin gina gida a hankali
  42. Neman amincewar shugaban ƙasa da majalisar zartarwa kan sababbin manufofin kula da gidaje a cikin kwanaki 100 na farko

Kara karanta wannan

'Ku sake zaɓen Tinubu': APC ta faɗi ɓangarori 4 da zai ba muhimmanci

C. HARKOKIN MAKAMASHI

1. Inganta samar da wutar lantarki ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da jihohi

2. Aiwatar da ayyukan samar da wutar lantarki ta amfani da iskar gas, tare da gyara matsalolin samar da gas, jigilar sa da tsarin biyan kuɗi.

3. Inganta layukan wutar lantarki, tsarin sadarwa da na’urorin sarrafa rarraba wutar lantarki

4. Tabbatar da cewa gidaje da kamfanoni sun samu na’urorin auna wutar lantarki, tare da rage asarar wuta a hanya

5. Samar da wutar lantarki ta musamman ga manyan wuraren masana’antu da yankunan kasuwanci na musamman

6. Faɗaɗa tashoshin sayar da iskar gas ta CNG da wuraren sauya motocin da ke amfani da fetur zuwa CNG

7. Mayar da hankali kan masana’antu, fasahar zamani, ƙirƙire-ƙirƙire, sarrafa kayayyaki da samar da ayyukan yi.

Kara karanta wannan

Zaben shugaban kasa: ‘Dan Atiku ya zage da yi wa Tinubu kamfe a doke mahaifinsa a Jigawa

8. Samar da aƙalla babbar cibiyar masana’antu guda ɗaya a kowace shiyyar

9. Zamantar da yankunan kasuwanci na musamman domin su zama cibiyoyin samar da kayayyaki da fitar da su zuwa ƙasashen waje.

10. Ƙarfafa amfani da kayayyakin da ake ƙerawa a Najeriya wajen ayyukan gwamnati

11. Haɓaka kuɗin da Najeriya ke samu daga fitar da kayayyakin da ba na mai ba

12. Bunƙasa fitar da kayayyakin da aka sarrafa, magunguna, kayayyakin masana’antu da ayyukan fasahar zamani zuwa ƙasashen waje.

13. Yin aiki da bankunan kasuwanci, cibiyoyin bayar da rancen raya ƙasa da masu zuba jari domin samar wa kamfanoni jari da sauƙin samun kuɗi

14. Kammala manyan hanyoyin mota da layukan dogo da ke haɗa yankunan noma, wuraren haƙar ma'adinai, masana’antu, manyan birane da iyakokin ƙasa.

15. Inganta tashoshin jiragen ruwa ta hanyar ƙara kayan aiki, samar da hanyoyin jigilar kaya ta jirgin ƙasa da tabbatar da aiki na sa’o’i 24.

16. Samar da wuraren adana kayan abinci masu sanyaya, musamman kayan da ake fitarwa zuwa ƙasashen waje, domin hana lalacewarsu.

Kara karanta wannan

Tallafin N50,000: SERAP ta jero tambayoyin da ke bukatar amsa daga gwamnatin Tinubu

17. Inganta tsarin National Single Window domin sauƙaƙa harkokin shigo da kaya da fitar da su zuwa ƙasashen waje.

18. Aiwatar da Project BRIDGE, wanda zai samar da sama da kilomita 90,000 na layin yanar gizo

19. Faɗaɗa hanyoyin intanet zuwa masana’antu, makarantu, asibitoci, cibiyoyin bincike, tashoshin jiragen ruwa da al’ummomin da ba su da isasshen tsarin sadarwa.

20. Mayar da hankali kan bunƙasa masana’antun manhajojin kwamfuta, bayanan zamani, fasahar sadarwa da sauransu

21. Bunƙasa haƙar ma'adinai, sarrafa ƙarafa, aluminium da sauran muhimman albarkatun ƙasa.

22. Faɗaɗa masana’antun sarrafa gas zuwa taki, sinadarai da sauran kayayyakin masana’antu.

23. Bunƙasa sarrafa amfanin gona, samar da abinci, sukari, auduga, masaku, tufafi, takalma da kayayyakin fata.

24. Ƙarfafa masana’antun roba, marufi, takardu da sauran kayayyakin masarufi.

25. Samar da cibiyoyin masana’antu a yankuna domin haɗa manoma, masu sarrafa amfanin gona, masu ƙera kayayyaki da masu fitar da su zuwa ƙasashen waje.

26. Ƙarfafa amfani da fasahar zamani da kare haƙƙin mallakar fasahohi da ƙirƙire-ƙirƙire.

27. Tabbatar da samar da wutar lantarki mai inganci, samun kuɗin ƙasashen waje cikin sauƙi da samar da manufofin tattalin arziki masu ɗorewa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bayyana tarkon da ya shirya a EFCC ga duk wanda zai gaje shi a mulki

28. Samar da tsarin manufofin kasuwanci da zuba jari masu inganci, tare da tabbatar da cewa dokoki da ƙa’idojin gwamnati ba sa canzawa ba tare da tsari ba.

29. Ci gaba da buɗe ƙofofin shigo da muhimman kayan masana’antu, injuna da fasahohin zamani.

30. Ƙara kuɗin da Najeriya ke samu daga fitar da kayayyaki da ayyuka zuwa ƙasashen waje, domin rage dogaro da shigo da kayayyaki.

31. Ƙarfafa zuba jari a masana’antu, samar da rance, inganta hanyoyin kasuwanci da gina manyan ababen more rayuwa.

32. Samar da tsarin bibiyar manyan ayyukan zuba jari daga lokacin amincewa da su zuwa lokacin kammalawa

Taron APC
Taron kamfen APC a Rivers Hoto: @Dolusegun
Source: Twitter

D. INGANTACCEN SHUGABANCI NA ADALCI DA BIN DOKA

  1. Faɗaɗa amfani da tsarin shigar da ƙara ta yanar gizo a kotu
  2. Ƙarfafa ’yancin kuɗin gudanar da harkokin shari’a a dukkan jihohi.
  3. Samar da ƙayyadaddun lokutan shigar da ƙara, sauraron shari’a da yanke hukunci, tare da amfani da fasahar zamani wajen bibiyar shari’o’i.
  4. Ɗaukar ƙarin alƙalai a wuraren da ake buƙata, faɗaɗa hanyoyin sasanta rikice-rikice ba tare da zuwa kotu ba, da inganta tsarin bayar da taimakon lauya ga marasa ƙarfi.
  5. Aiwatar da manufofin shari’a na ƙasa tare da ƙarfafa Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Ƙasa (NJC) wajen gaggauta hukunta jami’an shari’a da suka aikata ba daidai ba.
  6. Ƙarfafa hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da kotuna domin su gudanar da bincike da gurfanar da masu laifi cikin doka.
  7. Ƙarfafa dawo da dukiyoyin da aka samu ta haramtacciyar hanya da yaƙi da safarar kuɗi da mutane.
  8. Gudanar da bincike mai zaman kansa kan ayyukan gwamnati da ba a kammala ba ko kuma ba a amfani da su yadda ya kamata cikin kwanaki 100 na farko, tare da wallafa sakamakon binciken.
  9. Ci gaba da aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli na Yulin 2024, wanda ya tabbatar da ’yancin kuɗin ƙananan hukumomi 774.
  10. Kammala haɗa wasu hukumomin gwamnati kamar yadda rahoton Oronsaye ya tsara, domin rage kuɗin gudanar da gwamnati.
  11. Ci gaba da nazarin kundin tsarin mulki da rabon kuɗi domin mayar da wasu iko da albarkatu ga gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi.
  12. Ƙara damar jama’a shiga cikin tsara kasafin kuɗi da sa ido kan ayyukan gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi.
  13. Mayar da ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya zuwa tsarin gudanar da ayyuka ta yanar gizo, domin sauƙaƙa neman takardu da samun ayyukan gwamnati.
  14. Ƙaddamar da tsarin Citizen Service Guarantee, wanda zai bayyana lokacin da ya kamata a kammala ayyukan gwamnati
  15. Aiwatar da shirin Federal Civil Service Strategy and Implementation Plan 2030
  16. Inganta horar da ma’aikata, tsarin sayen kayayyakin gwamnati, jin daɗin ma’aikata da muhallin aikinsu.
  17. Faɗaɗa rajistar shaidar ɗan ƙasa domin kowane mutum ya samu shaida guda ɗaya da za a iya amfani da ita wajen samun ayyukan gwamnati.
  18. Haɗa sauran ma'ajiyar bayanai da hukumomi cikin babban tsarin shaidar ɗan ƙasa domin rage yawan takardun da ake buƙatar jama’a su gabatar.
  19. Amfani da tsarin shaidar ɗan ƙasa wajen taimaka wa mutane buɗe asusun banki, karɓar tallafi da sauransu
  20. Gudanar da tarurrukan tattaunawa da jama’a da masu ruwa da tsaki duk bayan watanni uku, tare da samar da hanyar karɓar korafe-korafe da ra’ayoyinsu.
  21. Bayyana ƙa’idojin ayyukan gwamnati, sakamakon ayyuka da yadda aka bi diddigin korafe-korafen jama’a.
  22. Ƙarfafa wayar da kan jama’a game da al’amuran ƙasa, kammala taskar bayanai na zamani da inganta sadarwar gwamnati mai gaskiya da ɗa'a.
  23. Jagorantar haɗin gwiwar ƙasashen yankin Afirka kan zaman lafiya, dimokuraɗiyya, tsaron iyakoki da yankin tafkin Chadi.
  24. Kammala ragowar 30% na shirin samar da ayyukan jakadanci ta yanar gizo, inganta bayanan ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje domin ƙarfafa kuɗin da suke aikowa gida.
  25. Ƙarfafa matsayin Najeriya a ƙungiyar BRICS, neman shiga ƙungiyar G20 da neman kujerar Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
  26. Ƙara tasirin Najeriya a tattaunawar ƙasashen duniya kan sauyin yanayi da harkokin teku.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya yi wa yankin Tinubu gori kan kuri'u, ya bugi kirki kan Arewa

Tanadin da ake yi wa Bola Tinubu

An ji labari cewa Gwamna Seyi Makinde ya tabbatar da cewa ana ci gaba da zama kan haɗakar jam'iyyun adawa domin a tunkari APC da murya daya.

Ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da Atiku Abubakar ko Peter Obi, muddin hakan zai taimaka wajen cimma burinsu na kawo sauyi a Najeriya a 2027.

Makinde ya ce har yanzu ba a yanke shawarar wanda za a tsayar ba, domin za a yi la’akari da ƙwarewar 'yan takara, ayyukansu a baya da ma ra'ayin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng