'Na Yi Mamakin Abin da Atiku Ya Yi Mini': Nafiu Bala Ya Yi Ɓarin Zance
- Nafiu Bala Gombe ya ce yana kallon Atiku Abubakar a matsayin uba, amma ya yi mamakin yadda tsohon mataimakin shugaban kasar bai tuntube shi ba
- Shugaban bangaren ADC ya ce hukuncin kotu ya tabbatar da sahihancin shugabancinsa, inda ya bukaci Atiku da David Mark su hada kai
- Bala ya ce yana son hada kan ‘yan adawa domin tunkarar zaben 2027, yana mai cewa ba ya adawa da Atiku da sauran jiga-jigan jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
ABUJA – Nafiu Bala Gombe, shugaban wani bangare na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya ce bai ji dadin abin da Atiku Abubakar ya yi masa ba.
Nafiu ya nuna takaicinsa kan yadda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, bai tuntube shi ba duk da cewa dukansu sun fito daga shiyya daya.

Source: Twitter
Bala ya bayyana hakan ne yayin wata hira da BBC Hausa a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, 2026.
Ya ce yana kallon Atiku a matsayin uba, amma ya yi mamakin yadda bai kira shi ba duk da rikicin shugabancin da ke faruwa a jam’iyyar.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan hukuncin kotun da ya tabbatar da matsayar bangarensa a rikicin shugabancin ADC.
Nafiu Bala ya ce kotu ta yi masa adalci
Bala ya ce hukuncin kotun ya tabbatar da cewa bangarensa ne halastaccen shugabancin jam’iyyar, yana mai cewa matsayarsu ya dogara ne da kundin tsarin mulkin ADC.
Ya ce:
"Alhamdulillah. Kamar yadda muka saba fada, gaskiya ita ce gaskiya, karya kuma karya ce. Allah ya yi mana nasara. Kotu ta ga hujjojin da ke cikin karar da gaskiyarmu, sannan ta yanke hukuncin mayar mana da shugabancin jam’iyyar."
Ya bayyana cewa bangarensa na jiran kwafin hukuncin kotun da aka tabbatar da sahihancinsa domin su mika shi ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), don ta yi gyaran da ya dace a bayanan shugabancin jam’iyyar.
Bala ya mika hannun sulhu ga Atiku, Mark
Sai dai shugaban bangaren ADC din ya yi gargadin cewa bai kamata a dauki hukuncin kotun a matsayin damar daukar fansa kan sauran bangaren ba.
Ya ce har yanzu yana son hada kai da Atiku, tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, da sauran jiga-jigan jam’iyyar domin karfafa ‘yan adawa gabanin zaben 2027.
A kalamansa:
"Wannan ba fada ba ne. Allah ya ba mu nasara, amma mu ba makiya ba ne. Muna mika musu hannun sada zumunci domin su daina girman kai da duk abin da za su fada, mu hada karfi domin karfafa ‘yan adawa da fuskantar gwamnati."
Atiku ya yabawa Bala Mohammed
Mun ba ku labarin cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar da tawagar shi sun isa jihar Bauchi domin gudanar da yakin neman zabe.
Atiku Abubakar da abokin takarar shi a ADC, Rotimi Amaechi sun ziyarci fadar mai martaba Sarkin Bauchi ranar Juma'a da yamma.
A bayanan da ya yi a fadar sarkin, Atiku ya yi godiya ga gwamna Bala Mohammed kan yadda ya bari suka shiga garin lami lafiya.
Asali: Legit.ng


