Atiku Ya Jajanta wa ƴan Najeriya kan yadda Tinubu Ya Nakasa Su a cikin ƙasarsu
- Atiku Abubakar ya nuna damuwarsa kan yadda kusan kashi 40 na mambobin ƙungiyar masu gidajen burodi a Najeriya suka daina sana’ar cikin shekaru biyu
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce tsadar makamashi, kuɗin ruwa da sauran kuɗaɗen gudanar da kasuwanci na tilasta wa kamfanoni rufewa
- Atiku ya yi kira ga gwamnatin Tinubu ta magance tsadar makamashi da rashin samun lamuni mai sauƙi domin farfaɗo da masana’antun cikin gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna tausayawarsa ga ’yan Najeriya kan halin kunci.
Atiku ya duba matsin tattalin arzikin da suke fuskanta sakamakon tsadar kayayyaki da sauran manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Source: Twitter
Atiku ya taba salon mulkin Tinubu
Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan rahoton da ke nuna cewa ƙungiyar masu gidajen burodi ta ƙasa ta rasa kusan kashi 40 cikin 100 na mambobinta cikin shekaru biyu, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan
2027: Gwamna ya ce nasarorin da ya samu za su taimaka masa wajen zama shugaban ƙasa
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC ya fitar a Bauchi, Atiku ya ce wannan lamari ya nuna irin matsin tattalin arzikin da masu sana’o’i ke fuskanta.
Ya bayyana cewa tsadar makamashi, hauhawar kuɗin ruwa da sauran kuɗaɗen samar da kayayyaki na tilasta wa kamfanoni da dama rufe ƙofofinsu, lamarin da ke ƙara wa ’yan Najeriya wahalar sayen abinci.
Atiku ya lissafa illar tsadar burodi
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce rufe gidajen burodi da dama ya jawo asarar ayyukan yi tare da tashin farashin burodi a sassan Najeriya.
Ya ce hakan na ƙara wa iyalai matsala, musamman ganin cewa burodi na cikin abincin da miliyoyin ’yan Najeriya ke amfani da shi a kullum.
Atiku ya ce:
“Abubuwan da suka biyo baya sun fara bayyana a faɗin ƙasar. Gidajen burodi da dama sun rufe, mutane sun rasa ayyukansu, sannan farashin burodi ya tashi matuƙa. Ga miliyoyin iyalai da ke dogaro da burodi a matsayin abincin yau da kullum, duk wani ƙarin farashi na ƙara musu wahalar ciyar da iyalansu.”

Source: Twitter
Atiku ya koka kan tsadar man dizal
Atiku ya bayyana cewa masu gidajen burodi na kashe kusan rabin kuɗaɗen gudanar da sana’arsu wajen samar da makamashi, cewar Punch.
Ya ce wani mai gidan burodi yana kashe Naira miliyan tara a kowane wata wajen sayen dizal, amma kuɗin ya tashi zuwa Naira miliyan 19.
Ya ƙara da cewa ƙaramin gidan burodi na buƙatar tsakanin Naira miliyan 40 zuwa 50 domin sauya tsarin samar da makamashi zuwa wasu hanyoyi.
Haka kuma, ya ce masu neman lamuni daga bankuna na fuskantar kuɗin ruwa da ya kai kashi 34 cikin 100.
Ya zargi gwamnatin Tinubu da gazawa
Atiku ya ce matsalolin da manoma, masana’antun sarrafa kayayyaki da masu gidajen burodi ke fuskanta na nuna gazawar manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, kamar yadda ya bayyana.
Ya kuma yi tambaya kan yadda gwamnatin ke ci gaba da karɓar basussukan cikin gida da na ƙasashen waje yayin da ƙananan masana’antu ke durƙushewa.

Kara karanta wannan
Akume ya ɗauko abin da ya faru a 1999, ya zargi Atiku da yunƙurin karya alƙawari a zaɓen 2027
A cewarsa, ya kamata ’yan Najeriya su san inda ake amfani da kuɗaɗen bashin da gwamnatin ke karɓa.
Atiku: Yan takarar gwamnan ADC sun fusata
An ji cewa kungiyar ’yan takarar gwamnan ADC ta ce hukuncin da ya soke shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin David Mark barazana ne ga ’yancin dimokuraɗiyya.
Sun buƙaci kotunan ɗaukaka ƙara su gaggauta nazarin hukuncin, tare da kira ga Tinubu da APC su mutunta tsarin jam’iyyu da dama.
Yan takarar sun nemi AU, ECOWAS, Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa su sa ido kan yadda ake wa ’yan adawa a Najeriya.
Asali: Legit.ng
