Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yi Murabus bayan Hura Masa Wuta

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yi Murabus bayan Hura Masa Wuta

  • Mataimakin shugaban ƙasar Indonesia, Gibran Rakabuming Raka, ya yi murabus bayan wata kotu ta nuna cewa babu sahihiyar shaida da ke tabbatar da cewa ya kammala karatun sakandare
  • Matakin ya zo ne bayan shafe watanni ana takaddama kan cancantarsa ta riƙe muƙamin mataimakin shugaban ƙasa, duk da cewa ya lashe zaɓen 2024 tare da Shugaba Prabowo Subianto
  • Rikicin ya ƙara tsananta dangantakar siyasa tsakanin Shugaba Prabowo da tsohon shugaban ƙasa Joko Widodo, mahaifin Gibran, wanda ya taimaka masa wajen samun tikitin takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Indonesia – Mataimakin shugaban ƙasar Indonesia, Gibran Rakabuming Raka, mai shekaru 39, ya yi murabus daga muƙaminsa bayan wata takaddama da ta shafi takardun karatunsa.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a siyasar ƙasar, musamman bayan wata kotu ta bayyana cewa babu wata sahihiyar shaida da ke tabbatar da cewa Gibran ya kammala karatun sakandare.

Gibran Rakabuming Raka
Gibran Rakabuming Raka da ya yi murabus. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

The Guardian ta rahoto cewa rikicin ya ƙara tsananta ne bayan majalisar dokokin ƙasar ta fara ƙoƙarin tsige shi daga muƙaminsa, lamarin da ya kai ga ganawarsa da Shugaba Prabowo Subianto.

Dalilin murabus da ya yi

Gibran ya shafe watanni yana fuskantar tambayoyi kan cancantar takardun karatunsa, musamman bayan an shigar da ƙara a kotun tsarin mulkin ƙasar domin a cire shi daga muƙaminsa.

A hukuncin da ta yanke a watan da ya gabata, kotun ta ce babu wata sahihiyar shaida da ke tabbatar da cewa Gibran yana da takardar shaidar kammala sakandare ko makamancinta daga wata ƙasa.

Sai dai kotun ta bayyana cewa ba za ta iya soke sakamakon zaɓen 2024 da ya ba shi damar zama mataimakin shugaban ƙasa ba, duk da cewa dokokin Indonesia sun tanadi takardar kammala sakandare a matsayin ɗaya daga cikin sharudan tsayawa takara.

Gibran ya yi karatu a makarantar sakandare ta Orchid Park da ke Singapore, sannan ya halarci UTS a Australia kafin ya samu digirin farko ta hannun Cibiyar Gudanarwa ta Singapore.

Duk da haka, hakan bai gamsar da masu sukar sa ba kuma bayan hukuncin kotun, majalisar dokokin ƙasar ta ƙara ƙaimi wajen ƙoƙarin tsige shi.

A ranar Talata, Gibran ya gana da Shugaba Prabowo Subianto, inda ya miƙa takardar murabus dinsa. Zuwa yammacin Laraba, wani babban hadiminsa ya tabbatar da cewa ya sauka daga muƙamin.

Tarihin Gibran da abubuwan da ya yi

Rahoto ya nuna cewa Gibran ɗan tsohon shugaban ƙasar Indonesia ne, Joko Widodo, wanda aka fi sani da Jokowi.

Kafin shiga siyasa, bai nuna sha'awar harkar mulki sosai ba, domin ya fi mayar da hankali kan kasuwanci, musamman harkokin abinci.

BBC ta wallafa cewa a shekarar 2019, ya shiga siyasa inda ya tsaya takarar kujerar magajin garin Solo.

Lokacin da aka fara maganar zai tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa a 2024, Gibran bai cika sharadin shekarun da ake buƙata ba, domin dokar ƙasar ta tanadi cewa dole ɗan takara ya kai shekaru 40.

Sai dai kafin a kammala rajistar ’yan takara, kotun tsarin mulkin ƙasar ta samar da keɓantaccen hukunci da ya ba wa waɗanda ba su kai shekaru 40 ba damar tsayawa takara idan sun taɓa riƙe muƙami.

Gibran Rakabuming Raka
Gibran Rakabuming Raka a wajen taron G20. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abin da ya ƙara tayar da kura shi ne, babban alkalin kotun a lokacin, Anwar Usman, kawun Gibran ne kuma surukin Jokowi.

Daga baya aka same shi da laifin karya ƙa'idojin ɗa'a saboda sauraron shari'ar duk da alaƙar da ke tsakaninsa da wanda abin ya shafa.

An cire Anwar daga muƙaminsa, amma hukuncin da ya bai wa Gibran damar tsayawa takara ya ci gaba da aiki.

Shugaban kasa ya yi murabus

A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasar Paraguay, Santiago Peña, ya yi murabus a lokacin da ƙasar ke fuskantar rikicin siyasa sakamakon durƙushewar bankin Ueno.

Peña ya sanar da murabus dinsa ne a ranar Alhamis, inda ya ce ya ɗauki matakin ne domin kare zaman lafiyar ƙasar, haɗin kan al'umma da cibiyoyin dimokuraɗiyya.

A cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, shugaban ya nemi afuwar al'ummar ƙasar idan har ya taɓa yin kuskure a lokacin mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng