An Samu Barkewar Mummunar Cuta a Makarantar da ke Dalibai Sama da 2,000 a Kano
- Hukumomin lafiya sun tabbatar da mutane 12 sun kamu da cutar diphtheria a Kwalejin First Lady da ke Mariri, ƙaramar hukumar Kumbotso
- An yi wa mutum 313 gwajin cutar, yayin da aka kai ɗaya daga cikin ɗaliban da suka kamu da ita mai tsanani asibitin IDH
- KNCDC ta nuna damuwa kan ƙarancin allurar rigakafi, tana mai cewa makarantar na buƙatar babban shirin yi wa ɗalibanta sama da 2,000 rigakafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - An samu barkewar cutar diphtheria a Kwalejin First Lady da ke Mariri, ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano, inda hukumomin lafiya suka tabbatar da mutane 12 sun kamu da cutar.
Hakan ya biyo bayan gwajin mutum 313 da ake zargin sun kamu da cutar, a makarantar kwana mai ɗalibai sama da 2,000.

Source: Facebook
Wani ma’aikacin makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa jaridar Daily Trust ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwamban 2026 cewa an fara gano cutar ne tsakanin ɗaliban makarantar.
Hukumomin lafiya sun fara ɗaukar mataki
Majiyar ta ce jami’an Hukumar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) sun shiga cikin lamarin ranar Alhamis bayan samun rahoton barkewar cutar.
A cewar majiyar, ɗaya daga cikin ɗaliban da suka kamu da cutar, wanda alamomin cutar suka tsananta a jikinsa, an kwantar da shi a Asibitin Cututtuka Masu Yaɗuwa (IDH) da ke Kano.
Sauran ɗaliban da abin ya shafa kuwa na samun kulawar lafiya ne a cikin makarantar.
Majiyar ta ce:
“Sun zo ne da tawagar gaggawa ta tunkarar barkewar cututtuka (RRT), tare da jami’ai daga ƙananan hukumomin Kumbotso, Tarauni da Nassarawa.”
An tabbatar da mutane 12 sun kamu
Da aka tuntube shi, Darakta-Janar na KNCDC, Farfesa Muhammad Adamu Abbas, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce hukumar ta samu rahoton barkewar cutar ranar Laraba, sannan ta tura jami’ai makarantar nan take domin gudanar da bincike da ɗaukar matakan dakile yaɗuwarta.
A kalamansa:
“Mun samu rahoton ne ranar Laraba, sannan muka je makarantar nan take domin gudanar da bincike da ɗaukar matakan dakile ƙarin yaɗuwar cutar.
“Mun yi gwajin mutum 313 da ake zargin sun kamu da cutar, inda aka tabbatar da mutane 12 sun kamu da ita ta hanyar binciken lafiya.
“Mun gudanar da binciken gano masu alamomin cutar a makarantar, sannan muka ba duk waɗanda ake zargin sun yi mu’amala da masu cutar magunguna. Haka kuma, mun wayar da kan sauran ɗalibai game da cutar.”
An nuna damuwa kan ƙarancin allurar rigakafi
Farfesa Abbas ya nuna damuwa kan ƙarancin allurar rigakafin cutar, yana mai cewa makarantar na buƙatar babban shirin yi wa ɗalibanta sama da 2,000 rigakafi domin kare su daga kamuwa da cutar.
Ya ce hukumar ba ta da isassun allurai a halin yanzu, don haka za ta nemi ƙarin allurai domin gudanar da shirin rigakafin.

Source: Original
A kalamansa:
“Akwai buƙatar gudanar da babban shirin rigakafi a makarantar, amma a halin yanzu ba mu da isassun allurai. Dole ne mu nemi ƙarin allurai domin yi wa ɗaliban rigakafi.”
Wannan sabon lamari ya ƙara tayar da hankula kan sake yaɗuwar cutar diphtheria a jihar Kano.
A watan da ya gabata, Legit Hausa ta ruwaito cewa wani mutum a yankin Danbare da ke Kano ya rasa ’ya’yansa biyar sakamakon cutar cikin kwanaki takwas.
Bakuwar cuta ta bulla Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa ma’aikatar lafiya ta jihar Zamfara ta ce an samu mutum 38 da suka kamu da wata bakuwar cuta da ba a gano asalinta ba.
Haka kuma, an samu wasu masu cutar a garin Moriki da ke ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Asali: Legit.ng


