Maganar Zargin Kisan Kiristoci Ya Dawo yayin da Zaɓen Najeriya ke Ƙaratowa
- Majalisar Dokokin Amurka za ta gudanar da zama kan zargin tsananta wa Kiristoci da matsalar tsaro a yankin Arewa ta Tsakiya
- Chris Smith ne zai jagoranci zaman, inda jami’an gwamnatin Amurka da masana za su yi bayani kan yadda Najeriya ke kare al’ummomin da ke fuskantar hare-hare
- Zaman zai kuma duba matakan da Amurka za ta ɗauka domin taimaka wa Najeriya wajen dakile hare-haren ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Gwamnatin Amurka za ta gudanar da zaman jin ƙai a Majalisar Dokokinta domin duba zargin tsananta wa Kiristoci da kuma matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
An shirya gudanar da zaman ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamba, 2026, inda za a tattauna irin ƙoƙarin da gwamnatin Najeriya ke yi wajen kare Kiristoci da sauran al'ummomin da ke fuskantar barazanar hare-hare.

Source: Facebook
Chris Smith, shugaban kwamitin kula da harkokin Afirka na Majalisar Wakilan Amurka, shi ne zai jagoranci zaman, cewar TheCable.
A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a ranar Litinin, an bayyana cewa taken zaman shi ne, 'Shekara Ɗaya Bayan Nan: Tantance Ƙoƙarin Najeriya na Kare Kiristoci da Tabbatar da Tsaro a Arewa ta Tsakiya'.
Abubuwan da za a tattauna a zaman
Rahoton Punch ya bayyana cewa zaman zai mayar da hankali kan hare-haren ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi, ciki har da Boko Haram, da kuma matakan da gwamnatin Najeriya ke ɗauka domin magance matsalar.
Haka kuma, za a tantance ƙoƙarin hukumomin Najeriya wajen dakile cin zarafin mabiya addinin Kirista da hukunta mutanen da ake samu da hannu wajen aikata laifukan tashin hankali.
Wani ɓangare na tattaunawar zai kuma mayar da hankali kan irin taimakon da Amurka za ta iya bayarwa domin tabbatar da cewa hukumomin Najeriya sun ɗauki matakan kare Kiristoci da Musulman da ba sa da hannu a ayyukan tsattsauran ra'ayi.

Source: Facebook
Jami'ai da masana za su halarta
Zaman farko zai samu halartar Frank Garcia, mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da Afirka, da Riley Barnes, mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da dimokuraɗiyya, haƙƙin ɗan Adam da ayyukan ƙwadago.
A zaman na biyu kuma, ana sa ran Nina Shea, babbar masaniya kuma shugabar Cibiyar 'Yancin Addini ta Hudson Institute, da Ryan Brown, babban jami'in gudanarwa na Open Doors US, za su gabatar da bayanai.
Haka kuma, Oge Onubogu, darakta kuma babbar masaniya kan shirin Afirka a Cibiyar Nazarin Dabarun Ƙasa da Ƙasa (CSIS), na cikin waɗanda za su halarta.
An tsara fara zaman ne da ƙarfe 11:00 na safe a ginin Rayburn House Office da ke birnin Washington DC. Haka kuma, za a watsa shi kai tsaye ta shafin YouTube.
Dan Majalisar Amurka ya shawarci yan Najeriya
A wani labarin, an ji cewa wani dan majalisar wakilan Amurka, Chris Smith, ya zargi gwamnatin Najeriya da gazawa wajen kare 'yan kasarta.
Harin da aka kai ya rutsa da wasu mazauna Jwak Maitumbi da Bin-Per a Mangu, inda aka kashe mutane da dama.
Smith ya bukaci gwamnatin Najeriya ta dauki matakin gaggawa, yayin da ya ce Amurka na bukatar a kare al'ummomin Kirista.
Asali: Legit.ng


