Jerin shahararrun Taurari 6 da suka zama ‘Yan takaran siyasa a zaben 2023

Jerin shahararrun Taurari 6 da suka zama ‘Yan takaran siyasa a zaben 2023

Nigeria - Kiran da ake yi wa matasa na shiga siyasa zai yi aiki a zaben 2023. Jaridar nan ta Punch ta bayyana haka a wani rahoto da ta fitar a makon nan.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A wannan rahoto, an tattaro sunayen matasan taurari da suka amsa wannan kira, suka shiga siyasa, har suka samun tikitin shiga takara a zabe mai zuwa.

A nan za a samu taurari biyar da za a gwabza da su wajen neman kujerar siyasa a 2023:

1. Funke Akindele

A 2023, ‘Yar wasar Nollywood kuma mai hada fina-finai, Miss Funke Akindele za ta tsaya takarar kujerar matamakiyar gwamnan jihar Legas a jam’iyyar PDP.

Dr. Olajide Adediran wanda aka fi sani da Jandor ya dauki ‘yar wasar a matsayin abokiyar takararsa. Tun 1999 har yau, PDP ba ta taba mulkin Legas ba.

Kara karanta wannan

Magoya bayan ‘Dan takaran Shugaban kasa sun zargi Gwamna da hana su yin taro

2. Banky W

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mawakin nan kuma ‘Dan fim, Bankole Wellington wanda aka fi sani da Banky W ya sake tsayawa takara a 2023, ya na neman kujerar majalisar tarayya a PDP.

Idan Banky W ya yi nasara a zaben, zai wakilci mazabar Eti Osa a majalisar wakilan tarayya.

Shahararrun Taurari
Funke Akindele da Tsohon Mijinta Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

3. Desmond Elliot

Yanzu haka Desmond Elliot ne yake rike da kujerar ‘dan majalisar dokoki na mazabar Surulere a jihar Legas, wannan karo ya sake samun tikiti a jam’iyyar APC.

Tun 2015 ‘dan wasan kwaikwayon ya zama ‘dan majalisa, akwai yiwuwar ya zarce har 2027.

4. Ned Nwoko

Ned Nwoko bai cikin matasa, amma shahararren mutum ne a Najeriya. Attajirin zai yi wa PDP takarar Sanata a mazabar Arewacin jihar Delta a zabe mai zuwa.

Mai kudin ya na auren taurariyar ‘yar wasar fim dinnan, Regina Daniels, su na da ‘ya ‘ya biyu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Osun

5. Odi Okojie

Na karshe a jerin da Punch ta fitar shi ne Odi Okojie wanda ya samu tikitin takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya a jihar Edo, yana so ya wakilci yankin Esan a 2023.

Odi Okojie ya yi suna, haka zalika mai dakinsa Mercy Johnson wanda tsohuwar ‘yar fim ce.

6. Caroline Hutchings

An kaddamar da Jaruma Coroline Hutchings wanda aka fi sani da Caroline Danjuma a matsayin abokiyar takarar Mr Iboro Otu, dan takarar gwamna na jam'iyyar African Action Congress (AAC) a zaben 2023 a Akwa Ibom.

Godsday Elder Orubebe ya zama DG

Dazu kun ji cewa tsohon jigon PDP, Godsday Elder Orubebe yana da farar kafa, domin shi ne zai jagoranci takarar Gwamnan APC a jihar Delta a zabe mai zuwa.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege mai takara ya bada wannan sanarwa ta bakin Kakakin kamfe, Ima Niboro a makon nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel