Dan Majalisa Da Aka Kama Yana Kallon Fim Ɗin Batsa a Wayansa Yayin Zaman Majalisa Ya Yi Murabus

Dan Majalisa Da Aka Kama Yana Kallon Fim Ɗin Batsa a Wayansa Yayin Zaman Majalisa Ya Yi Murabus

  • Neil Parish, Dan Majalisar Dokokin Birtaniya ya sauka daga mukaminsa bayan amsa cewa ya kalli bidiyon batsa a cikin majalisa
  • Dan majalisar ya ce da farko tsautsayi ce a faru a lokacin da ya ke kallon wasu bidiyon motoccin noma amma na biyun da gangan ne
  • Tunda farko jam'iyyarsa ta Conservative ta dakatar da shi saboda zargin ta kuma kafa kwamitocci biyu don bincike kan zargin da ake masa

Birtaniya - Dan Majalisar Birtaniya daga Jam'iyyar Conservative masu mulki a kasar ya yi murabus a ranar Asabar bayan ya amsa cewa da gangan ya kalli fim din 'batsa' a zauran House of Commons.

Neil Parish, wanda ya wakilci Southwest England a majalisar ya ce ya yi murabus don haka za a yi zaben cike gurbi a Tory bayan abin da ya kira 'hauka karara', rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Kotu ta jefa Ma'aikatan banki 2 kan laifin sace miliyoyin kudi na kwastoman da ya mutu

Dan Majalisa Da Aka Kama Yana Kallon Fim Din Batsa a Wayansa Yayin Zaman Majalisa Ya Yi Murabus
Dan Majalisar Burtaniya Da Aka Kama Yana Kallon Fim Din Batsa a Wayansa Yayin Zaman Majalisa Ya Yi Murabus. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

"Ina ganin hankali na ya gushe baki daya kuma mutuntaka ta ta gushe a lokacin," ya shaida wa BBC a wani hira da ta yi da shi da aka saki ranar Asabar inda ya sanar da murabus dinsa.
"Wannan lokacin tamkar hauka ne kuma bai dace ba ... ba zan bada uzuri kan abin ba."

Tun a ranar Juma'a an dakatar da dan majalisar mai shekaru 65 kuma an kafa a kalla kwamitoci biyu na binciken abin.

Wasu yan majalisa mata su biyu sun yi ikirarin cewa sun gan shi yana kallon bidiyon batsa a wayansa lokacin yana zaune kusa da su, BBC Hausa a rahoto.

Amma ya ce shi motoccin noma ya ke kallo, ya shiga wani shafi na intanet mai suna irin ta shafin motoccin noman ya dan kalla duk da ya san bai dace ba. Sai dai laifinsa shine sake shiga ya kalla karo na biyu.

Kara karanta wannan

Sabon Sarkin Oyo zai gaje matan Oba Lamidi 11, Yarima mai jiran gado Ladigbolu

Jigawa: 'Yan Hisbah sun kama mutum 47 suna sheƙe ayansu, ciki har da mata 16, an ƙwace kwallaban giya 745

A wani rahoton, Hukumar Hisbah reshen jihar ta kama mutane 47 da ake zargin su na aikata rashin da’a ciki har da mata 16 kamar yadda

The Nation ta ruwaito. Kwamandan rundunar ta jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya tabbatar da kamen ta wata hira da menama labarai su ka yi da shi jiya a Dutse, babban birnin jihar.

Bisa ruwayar jaridar The Nation, Dahiru ya ce a cikin wadanda aka kama har da wadanda ake zargin karuwai ne su 16.

Kuma an kama su ne bayan kai samamen da hukumar ta yi a gidajen giya, gidajen karuwai da sauran wuraren da mutanen banza ke zama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel