Batun Cafke Netanyahu Ya Karu, Trump Ya Fadi Me zai Faru idan Ya Je Amurka
- Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewa ba za a kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ba idan ya kai ziyara Amurka
- Kalaman Trump sun biyo bayan bayanin magajin garin New York, Zohran Mamdani, cewa har yanzu ana nazarin yiwuwar kama Netanyahu
- Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya ta fitar da sammacin kama Netanyahu tun a shekarar 2024 kan zargin aikata laifuffukan yaƙi a Gaza
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington DC – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ba za a kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ba idan ya kai ziyara ƙasar Amurka.
Trump ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, inda ya jaddada cewa babu wani yanayi da zai sa a cafke Netanyahu yayin da yake Amurka.

Kara karanta wannan
Netanyahu zai iya shiga matsala, an fara maganar cafke shi idan ya je birnin New York

Source: Getty Images
Maganar da Donald Trump ya yi
Rahoton Reuters ya nuna cewa Donald Trump ya bayyana ba yadda za a yi wasu jami'ai su kama Benjamin Netanyahu saboda ya shiga New York.
Ya ce:
"Ba za a kama Benjamin Netanyahu ba ta kowace hanya ko salo yayin da yake cikin Amurka."
Me ya jawo wannan martani?
Kalaman shugaban Amurkan sun biyo bayan wata hira da magajin garin birnin New York, Zohran Mamdani, ya yi, inda ya ce har yanzu sashen shari'a na birnin na nazarin irin matakin da doka ta ba su damar ɗauka idan Netanyahu ya shiga birnin.
A cikin hirar da ya yi, Mamdani ya ce ya kamata Netanyahu ya gurfana a gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya (ICC).
Ya bayyana cewa:
"Na yi imanin cewa Firaminista Netanyahu ya kamata ya kasance a Hague. Shi mutum ne da Kotun ICC ta tuhume shi da aikata laifuffukan yaƙi."

Source: Getty Images
Isra'ila ta yi martani
Tun a shekarar 2024 ne Kotun ICC ta fitar da sammacin kama Netanyahu bisa zargin aikata laifukan yaƙi a lokacin yaƙin Gaza.
Sai dai Isra'ila ta yi watsi da ikon kotun, tana mai cewa ba ta amince da huruminta ba, tare da musanta zarge-zargen aikata laifuffukan yaƙi.
A martanin da ta yi, the Guardian ta rahoto cewa gwamnatin Isra'ila ta bayyana sammacin kama Netanyahu a matsayin mara inganci, tana mai zargin Mamdani da ƙoƙarin karkatar da hankalin jama'a.
Rahotanni sun nuna cewa Netanyahu kan kai ziyara birnin New York a duk watan Satumba domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA).
Sojan Amurka ya mutu a Iraki
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani sojan Amurka ya mutu a Arewacin Iraki yayin wani aiki na tarwatsa wata mai fashewa da ake zargin ta Iran ce.
Rahotanni sun ce wani sojan ya kuma jikkata a wannan aiki, yayin da wannan mutuwar ta ƙara yawan sojojin Amurka da suka rasa rayukansu tun bayan sake ɓarkewar rikici tsakanin Amurka da Iran.
Haka kuma, dakarun Iran sun yi iƙirarin kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka da ke Jordan da Kuwait, tare da cewa sun hallaka sojojin Amurka da dama.
Asali: Legit.ng
