Netanyahu Zai Iya Shiga Matsala, an Fara Maganar Cafke Shi idan Ya Je Birnin New York

Netanyahu Zai Iya Shiga Matsala, an Fara Maganar Cafke Shi idan Ya Je Birnin New York

  • Magajin garin New York, Zohran Mamdani, ya yi magana kan yiwuwar cafke Benjamin Netanyahu a Amurka
  • Mamdani ya ce har yanzu yana tattaunawa da masu shari'a kan yiwuwar kama Firayin ministan na Isra'ila idan ya ziyarci birnin
  • Ya bayyana cewa duk abin da doka ta ba shi damar yi a New York zai aiwatar, amma ba zai kirkiri sabbin dokoki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

New York, US - Magajin garin New York, Zohran Mamdani, ya bayyana shirin kama Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.

Mamyani ya bayyana cewa har yanzu yana tattaunawa da hukumomin shari'a kan yiwuwar kama Netanyahu idan ya halarci taron Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumba.

An fara maganar cafke Netanyahu a birnin New York
Magajin garin New York, Zohran Mamdani da Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: John Nacion, Marc Israel SELLEM/POOL/AFP.
Source: Getty Images

Shirin magajin gari, Mamdani kan Netanyahu

Mamdani ya shaida wa jaridar The New York Times cewa yana tattaunawa da Sashen Shari'a na birnin New York domin tantance abin da doka ta ba shi damar yi.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya gano abin da ake bukata don rage talauci a Najeriya

Magajin garin ya bayyana himmatuwarsa wurin tabbatar da cewa ya bi doka da oda ba tare da yin amfani da kujerarsa domin cimma wata manufa ba.

Tun bayan hawansa kujerar, Isra'ila ta sha zargin Mamdani na nuna wariya ga Yahudawa sabanin yadda suka saba mu'amala da tsohon magajin garin birnin New York.

Mamdani ya ce:

"Duk abin da doka ta ba ni damar yi a birnin New York, shi ne zan yi, amma ba za mu kirkiri sababbin dokoki domin cimma wannan buri ba."
Magajin garin New York zai iya cafke Netanyahu
Magajin garin New York da aka rantsar, Zohran Mamdani. Hoto: Zohra Kwami Mamdani.
Source: Facebook

'Abin da ya kamata a yi wa Netanyahu'

Magajin garin ya kara da cewa yana ci gaba da gudanar da tattaunawa mai zurfi da masu ba da shawarar shari'a kan batun yiwuwar daukar irin wannan mataki.

Mamdani ya bayyana ra'ayinsa cewa Firaminista Benjamin Netanyahu ya kamata ya gurfana a Hague, inda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ke da hedikwata.

Ya ce an fitar da sammacin kama Netanyahu bisa zargin aikata laifukan yaki da suka shafi rikicin Gaza, yana mai jaddada cewa wannan shi ne matsayinsa.

Mamdani ya kara da cewa mutane da dama suna da irin wannan ra'ayi saboda abin da suka yi imanin cewa manufofi da ayyukan Netanyahu sun haifar cikin shekaru da suka gabata.

Kara karanta wannan

'Abin da Habila da ta mutu a gidan minista ta fada wa saurayinta kafin ta rasu'

Sai dai ya nanata cewa duk wani mataki da zai dauka zai kasance ne cikin iyakar abin da dokokin New York da Amurka suka tanada, ba tare da kauce wa tsarin doka ba, kamar yadda France 24 ta ruwaito.

Mamdani ya ruguza shirin Isra'ila

A wani labarin, an ji cewa sabon magajin birnin New York, Zohran Mamdani, ya soke wasu dokokin da tsohon Magajin gari Eric Adams ya sanya masu alaƙa da kasar Isra’ila.

Gwamnatin Isra’ila ta zargi Mamdani da ƙara rura wutar kyamar Yahudawa bayan janye ma’anar IHRA kan nuna wariya da ya yi yana shiga ofis.

Mamdani ya mayar da hankali kan batun gidaje, inda ya bayar da umarni na gaggawa domin hanzarta gina gidaje a birnin domin saukaka rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.