Kurunkus: Matakin da INEC Za Ta Dauka kan Batun Rusa Takarar Atiku a 2027
- Hukumar zabe ta INEC ta yi magana kan hukuncin kotu da ya soke shugabancin ADC da takarar Atiku Abubakar
- Kotun ta soke shugabancin kwamitin riƙon ƙwarya na David Mark, tare da rushe matakan da kwamitin ya ɗauka, ciki har da zaɓen Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027
- INEC ta ce za ta tattauna batun a taronta na mako mai zuwa, kuma za ta bi duk wani sabon umarnin kotu idan ɓangaren David Mark ya ɗaukaka ƙara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ba za ta ɗauki matsaya kan rikicin shugabancin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ba, har sai ta samu tare da nazarin sahihin kwafin hukuncin kotu.
Matakin na INEC ya biyo bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamban 2026 inda ta soke shugabancin kwamitin riƙon ƙwarya da David Mark ke jagoranta.

Source: Facebook
Legit Hausa ta fahimci cewa kotun ta kuma soke matakan da aka ɗauka a ƙarƙashin wannan shugabanci, ciki har da zaɓen tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027.
INEC ta bayyana matakin da za ta ɗauka
Da yake magana da jaridar The Punch, kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Haruna, ya ce hukumar za ta fara da neman sahihin kwafin hukuncin.
Ya bayyana cewa INEC ba za ta yanke hukunci bisa rahotannin kafafen yaɗa labarai ba, saboda akwai yiwuwar bayanan da aka wallafa ba su yi daidai da abin da kotu ta yanke ba.
Haruna ya ce:
“Ba za mu iya ɗaukar matsaya ba har sai mun ga hukuncin da kanmu. Dole ne mu samo sahihin kwafin hukuncin, domin ba ma yanke shawara bisa rahotannin abin da aka ce kotu ta yanke, saboda rahotannin na iya kasancewa ba daidai ba.”
Ya ƙara da cewa hukumar za ta tattauna batun a taronta na mako mai zuwa domin tantance matakin da ya dace ta ɗauka.
“Wannan batu a bayyane yake. Amma duk da haka, muna nan har zuwa mako mai zuwa, lokacin da hukumar za ta gudanar da taronta. Dole ne mu zauna mu tattauna a kansa,” in ji shi.
INEC za ta bi duk wani sabon umarnin kotu
Haruna ya kuma nuna cewa hukumar za ta mutunta duk wani umarnin kotu da zai biyo bayan ɗaukaka ƙarar da ɓangaren David Mark zai iya yi.
Ya ce idan ɓangaren Mark ya ɗaukaka ƙara kuma ya samu umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin, INEC za ta bi wannan umarni.
“Babu shakka, idan ɓangaren David Mark ya ɗaukaka ƙara, wanda na tabbata za su yi, kuma suka samu umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin, to dole ne mu bi umarnin kotun,” in ji kwamishinan.

Source: Facebook
ADC ta daukaka kara
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 5 ga Nuwamba, 2026, a shari’a mai lamba FHC/ABJ/CS/1619/2025.
Hon. Nafiu Bala Gombe shi ne ya shigar da karar, inda daga karshe kotu ta rusa shugabancin ADC karkashin tsohon shugaban Majalisar dattawa, Sanata David Mark.
Asali: Legit.ng

