Tinubu ya bayyana tarkon da ya shirya a EFCC ga duk wanda zai gaje shi a mulki
- Shugaban ƙasa ya ce duk kuɗin da EFCC ta ƙwato daga hannun waɗanda suka wawure dukiyar ƙasa za su shiga NELFUND
- Ya ce matakin zai taimaka wajen rage wa iyaye nauyin biyan kuɗin makaranta tare da ba ɗalibai damar samun ilimin zamani
- Bola Tinubu ya ce babu wanda zai iya sauya wannan tsari, har ya bayyana cewa tuni gwamnati ta fara ware kuɗi domin hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi dabarar da za ta sa dole a cigaba da amfani da tsarin da ya kawo ko da bayan barinsa ofis.
Bola Ahmed Tinubu ya ce duk kuɗin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta karɓo za a karkatar da su zuwa hukumar NELFund.
The Cable ta ruwaito shugaban yana bayanin tanadin da gwamnati ta yi wa Asusun Ba da Lamunin Karatu na Ɗaliban Najeriya wato NELFUND.
Abin da aka samu daga hannun waɗanda suka wawure dukiyar ƙasa za su tafi wajen ganin yaran talakawa sun samu ilmin gaba da sakandare.
Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin ƙaddamar da otal ɗin Arise Palm Resort da ke Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.
Ya ce matakin na da nufin rage wa iyaye nauyin biyan kuɗin makaranta da kuma bai wa dukkan 'yan Najeriya damar samun ilimi mai zurfi.
Shugaban ya ce ya fahimci irin wahalar da iyaye ke sha wajen biyan kuɗin karatun 'ya'yansu, don haka gwamnati ta ɗauki matakin tallafa wa ɗalibai.
Ta hanyar shirin lamunin karatun nan, yanzu yara suna iya samun bashin biyan kuɗin karatu da za su biya da zarar sun fara aiki idan an yaye su.
Ya jaddada cewa daga yanzu duk kuɗin da EFCC ta karɓo za a sanya su cikin shirin NELFUND, yana mai cewa babu wanda zai iya sauya wannan shirin.
A ranar 19 ga watan Agusta ne Mai girma Tinubu ya bayar da umarnin karkatar da abin da EFCC ta karɓo zuwa asusun NELFUND a Najeriya.

Kara karanta wannan
Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya
Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya kuma bayyana cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince a karkatar da wasu rarar kuɗi zuwa wannan shiri.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa tun shekarar 2024, gwamnati ta ware Naira biliyan 100 daga abin da suka kwato zuwa NELFund.
Olukayode ya ce idan hukumar ta raba marasa gaskiya da dukiarsu, sai a yi amfani da maƙudan kudin wajen tallafa wa shirin lamunin karatun ɗalibai.
Asali: Legit.ng
