Kasashe 13 na Afrika da Lebanon ke Ba Biza bayan Sun Isa Kasar

Kasashe 13 na Afrika da Lebanon ke Ba Biza bayan Sun Isa Kasar

  • Lebanon ta amince da 'yan ƙasashen Afrika 13 da za su samu damar shiga kasar ba tare da sun yi biza kafin su hau jirgi zuwa yawon bude ido
  • Najeriya na cikin jerin ƙasashen da za su amfana da wannan tsari, inda za a bayar da biza bayan 'yan kasar sun sauka a filin jirgin Lebanon
  • Sai dai Lebanon ta bayyana cewa dole ne matafiya su cika wasu sharudda kafin a ba su izinin shiga kasar da kuma mika masu biza

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Lebanon – Hukumomin tsaron kan iyakokin ƙasar Lebanon sun fitar da jerin ƙasashen Afrika 13 da 'yan ƙasarsu za su iya samun bizar yawon buɗe ido bayan sun isa ƙasar, ba tare da neman biza a ofishin jakadancin Lebanon kafin tafiya ba.

Kara karanta wannan

Masoyan Tinubu sun mayar wa Kwankwaso martani kan tikitin Musulmi Musulmi

Sabon tsarin ya bai wa matafiya daga ƙasashen da aka amince da su damar samun bizar wata guda idan sun isa filayen jiragen sama.

Lebanon ta fitar da kasashen Afrika da za su iya shiga kasar ba biza
Shugaban kasar Lebanon Joseph Aoun Hoto: Joseph Aoun
Source: UGC

Jaridar Punch ta wallafa cewa haka kuma za a iya ba su biza idan sun isa mashigan kasar na kan iyaka, muddin sun cika dukkan sharuddan shiga ƙasar.

Kasashen da Lebanon za ta ba biza

Lebanon ta sahalewa kasashen Afrika 13 samun biza bayan sun sauka a cikin kasarta, inda ta raba zuwa yankin Afrika ta Arewa, Afrika ta Yamma da Afrika ta Kudu.

Kasashen Afrika da ke cikin wannan tsari sun haɗa da:

1.Aljeriya

2.Masar

3.Libya

4.Mauritania

5.Morocco

6.Tunisiya

7. Ghana

8. Côte d’Ivoire

9. Najeriya.

10.Comoros

11. Djibouti

12. Somalia

13. Sudan

Sharuddan shiga Lebanon

Ko da yake ba sai an nemi biza kafin tafiya ba, hukumomin shige da fice na Lebanon sun ce dole ne matafiya su gabatar da wasu takardu da shaidu idan sun isa ƙasar.

Najeriya ta shiga cikin jerin kasashen da za su shiga kafin a ba si biza
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Source: Facebook

Daga cikin sharuddan akwai tikitin komawa ƙasarsu ko tikitin ci gaba da tafiya zuwa wata ƙasa, tare da hujjar inda za su sauka, wato otal da aka tabbatar ko adireshin gidan wanda zai karɓe su a Lebanon da lambar wayarsa.

Kara karanta wannan

Matukan tankar mai sun ruga da gudu a Hormuz yayin da Iran ke barin wuta

Haka kuma dole ne matafiyi ya nuna yana da aƙalla Dala 2,000 a tsabar kuɗi ko kuma takardar cakin banki mai wannan daraja domin tabbatar da cewa yana da isassun kuɗin da zai kashe yayin zamansa.

Hukumomin Lebanon sun yi gargaɗin cewa duk wanda bai cika waɗannan sharudda ba na iya rasa damar shiga ƙasar, duk da kasancewarsa daga cikin ƙasashen da suka cancanci samun biza bayan isa.

Isra'ila ta bijire kan Lebanon

A baya, kun samu labarin cewa ministan tsaron Israila, Israel Katz, ya yi maganar janye dakarun sojojin kasarsa daga Kudancin Lebanon inda su ke tafka barna yayin da su ke kai wa Hezbollah hari.

Israel Katz ya bayyana cewa dakarun sojojin Israila za su ci gaba da zama a Kudancin Lebanon domin ba mutanen Arewacin kasar, inda ya ce wai sun nemi a ba su kariya daga dakarun Hezbollah.

Ministan tsaron na Israila ya nuna cewa idan Amurka ta nemi a janye sojojin daga Kudancin Lebanon, wanda ke kunshe a cikin sharuddan dakatar da yaki da Iran ta gabatar, amma ya ce ba za su yi biyayya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng