Manyan Alkawura da Andy Burnham Ya Dauka da Ya Zama Sabon Firaministan Birtaniya
- Andy Burnham ya zama firaministan Birtaniya bayan Sarki Charles na III ya gayyace shi kafa gwamnati bayan murabus din Keir Starmer a hukumance
- Burnham ya yi alkawarin dawo da amincewar jama'a, farfado da tattalin arziki da kuma bai wa yankuna karin iko maimakon Westminster kadai
- Sabon firaministan ya ce Birtaniya na bukatar sabon salo a siyasa domin kawo karshen rikice-rikice da rashin tabbas da aka dade ana fama da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Birtaniya - Andy Burnham ya zama firaministan Burtaniya a hukumance bayan da Sarki Charles na III ya gayyace shi don kafa gwamnati.
A taron, Burnham ya yi alƙawarin dawo da aminci a siyasar Birtaniya, da kuma samar da iko daga Westminster da kuma sanya ƙasar a kan sabuwar hanyar sabunta tattalin arziki na dogon lokaci.

Kara karanta wannan
A karshe, Peter Obi ya bar boye boye, ya fadi dalilin daukar Kwankwaso mataimakinsa

Source: Getty Images
Birtaniya ta yi sabon firaminista
An naɗa Burnham a hukumance a ranar Litinin a Fadar Buckingham, inda Sarki Charles na III ya nemi ya kafa sabuwar gwamnati bayan murabus ɗin Keir Starmer, cewar rahoton BBC.
A cikin wata sanarwa da Fadar Buckingham ta fitar ta ce:
"Mai Martaba ya tarbi dan majalisa Rt Hon Andrew Burnham kuma ya nemi ya kafa sabuwar gwamnati. Dan majalisa Rt Hon Andrew Burnham ya amince da tayin Sarki kuma ya karbi nadinsa a matsayin Firayim Minista kuma shugaban baitulmali na farko."
Fadar ta ƙara da cewa matar Burnham, Marie France van Heel, ita ma ta samu tarba daga sarki. Burnham ya zama firayim minista na takwas a jam'iyyar Labour kuma na 59 a jimilla a Birtaniya.
Nadinsa ya kuma sanya shi firayim minista na huɗu a zamanin Sarki Charles na III, wanda ya fara mulki a shekarar 2022, kuma mutum na biyar da ya mamaye titin 10 Downing a cikin shekaru huɗu kacal, wanda ya tsawaita lokacin rashin zaman lafiya a gwamnatin Birtaniya.
Alkawuran da Burnham ya dauka a Birtaniya
Da yake gabatar da jawabinsa na farko a matsayin firayim minista, Burnham ya amince da karuwar takaicin da jama'a ke nunawa game da siyasa, kuma ya ce dole ne gwamnatinsa ta dawo da amincewar masu kada kuri'a.
"Ina jin kukan mutane. Ba mu yi abubuwa masu kyau ba kuma muna bukatar mu inganta harkokin mu. Tabbas za mu inganta siyasar mu," in ji Burnham.
Sabon firayim ministan ya bayyana gwamnatinsa a matsayin wata dama ta sake farfado da siyasar Birtaniya bayan shekaru da dama na rarrabuwar kawuna da rashin tabbas.
"Za mu mai da wannan lokacin ya zama abin da zai kawo ci gaba mai dorewa ga Birtaniya kuma za a sami sabon tsarin siyasa," in ji shi.

Source: Getty Images
Burnham zai magance matsalar tattali
Burnham ya yi jayayya cewa ƙalubalen tattalin arziki da siyasa na Birtaniya sun samo asali ne daga wasu shawarwari da aka yanke a shekarun 1980, ciki har da mallakar kamfanoni da kuma rage masana'antu, wanda ya ce ya bar al'ummomi da yawa a baya.
Kafar labaran CNN ta rahoto sabon Firaministan yana cewa:
"Yankuna da yawa har yanzu ba su farfaɗo daga wannan matsala ba. Lallai ne za mu mai da hankali kan magance matsalolin tattalin arziki maimakon samun daukakar siyasa kawai."
Ya kuma ce dole ne shugabannin siyasa na zamaninsa su tashi tsaye don magance kalubalen da kasar ke fuskanta.
Keir Starmer ya yi murabus daga minista
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Firayim Ministan Birtaniya, Sir Keir Starmer, ya sanar da murabus daga mukaminsa bayan ya shafe ƙasa da shekaru biyu a kan mulki.
Murabus ɗin ya biyo bayan watanni na rikice-rikicen siyasa, sauyin manufofi, raguwar farin jini a wajen jama’a, da kalaman Donald Trump.
A jawabi mai cike da sosa rai da ya yi a wajen gidan gwamnati na 10 Downing Street, Starmer ya ce ya dauki dukkan matakai a gwamnatinsa don kare muradun kasar da yake kauna.
Asali: Legit.ng

