Cikin Shekaru 10: Dalilan da Ke Sa Firaministocin Birtaniya Sauka daga Mulki
Birtaniya – Murabus din Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer, ya kara wani sabon babi a tarihin siyasar kasar da ta shafe shekaru 10 tana fuskantar sauye-sauyen shugabanci da ba a taba gani ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Daga sakamakon zaben Brexit zuwa annobar COVID-19 da matsalolin tattalin arziki da siyasa, gwamnatin Birtaniya ta fuskanci kalubale da suka sauya yanayin siyasar kasar.

Source: Getty Images
Cikin shekaru 10 kacal, mutane shida ne suka rike kujerar Firayim Minista a lamba 10 Downing Street, kamar yadda rahoton The Guardian ya nuna.
A lokacin sanar da murabus dinsa, Starmer ya ce ya “ji amsar” jam’iyyarsa kan ko shi ne mutumin da ya dace ya jagoranci Labour zuwa babban zabe na gaba, inda ya ce ya amince da hukuncin “cikin mutunci”.
Ga jerin shugabannin da suka jagoranci Birtaniya a wannan lokaci:
1. David Cameron (2010–2016)

Source: Getty Images
David Cameron ya zama Firayim Minista a 2010, inda ya fara mulki a karkashin hadin gwiwa da jam’iyyar Liberal Democrats kafin ya samu rinjaye a zaben 2015.
Gwamnatinsa ta aiwatar da manufofin rage kashe-kashe domin rage gibin kasafin kudi bayan matsalar tattalin arzikin duniya ta 2008.
Sai dai abin da ya fi sanya sunansa cikin tarihi shi ne kuri’ar jin ra’ayin jama’a kan zaman Birtaniya a Tarayyar Turai (EU) a 2016, kamar yadda BBC ta ruwaito.
Cameron ya goyi bayan ci gaba da kasancewa cikin EU, amma bayan masu kada kuri’a sun zabi ficewa daga kungiyar, ya yi murabus yana mai cewa kasar na bukatar sabon shugaba domin tafiyar da tsarin Brexit.
2. Theresa May (2016–2019)

Source: Getty Images
Theresa May ta gaji Cameron a watan Yulin 2016, inda ta karbi babban kalubalen fitar da Birtaniya daga Tarayyar Turai.
Rahoton Aljazeera ya nuna cewa mafi yawan lokutan mulkinta sun karkata ne wajen tattaunawar Brexit da kokarin samun amincewar majalisa kan yarjejeniyar ficewa.
Sai dai rashin samun goyon bayan majalisa sau da dama ya raunana matsayinta. Daga bisani matsin lamba daga cikin jam’iyyarta ta Conservative ya tilasta mata sanar da murabus a 2019.
3. Boris Johnson (2019–2022)

Source: Getty Images
Boris Johnson ya zama Firayim Minista a Yulin 2019 da alkawarin kammala aikin Brexit. A karkashin jagorancinsa, Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai a watan Janairun 2020.
Ya kuma jagoranci kasar lokacin annobar COVID-19, inda aka aiwatar da dokokin kulle-kulle, shirye-shiryen rigakafi da tallafin tattalin arziki.
Sai dai gwamnatinsa ta shiga matsala bayan badakalar Partygate, wadda ta shafi tarukan da aka yi a lokacin da ake da dokar hana taro saboda annobar, cewar rahoton Reuters.
Rikicin ya rage masa goyon baya daga ‘yan majalisar Conservative, lamarin da ya kai ga murabus dinsa a 2022.
4. Liz Truss (2022)
Liz Truss ta zama Firayim Minista a watan Satumban 2022 bayan ta lashe zaben shugabancin jam’iyyar Conservative.
Sai dai mulkinta ya fuskanci matsalar tattalin arziki bayan gabatar da wani sabon tsarin kasafin kudi da ya girgiza kasuwannin kudi.
Rashin amincewa da manufofinta ya kara tsananta, wanda ya kai ga yin murabus bayan kwanaki 45 kacal a kan mulki.
Wannan ya zama mafi gajeren wa’adi da Firayim Minista ya taba yi a tarihin Birtaniya, kamar yadda CNN ta ruwaito.
5. Rishi Sunak (2022–2024)
Rishi Sunak ya maye gurbin Truss a watan Oktoban 2022 a lokacin da kasar ke fama da matsalar tattalin arziki da rashin tabbas a siyasa.
Gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen rage hauhawar farashi, dawo da kwarin gwiwa a tattalin arziki da kula da kudaden gwamnati.
Sai dai ya fuskanci matsaloli da suka hada da matsin lambar bakin haure, yajin aiki da tsadar rayuwa, a cewar wani rahoto na CNBC.
Duk kokarinsa na farfado da gwamnati bai hana jam’iyyar Conservative shan kaye a babban zaben 2024 ba, wanda ya kawo karshen mulkin jam’iyyar na shekaru 14.
6. Keir Starmer (2024–2026)

Source: Twitter
Keir Starmer ya zama Firayim Minista a 2024 bayan ya jagoranci jam’iyyar Labour zuwa nasara a babban zabe.
Gwamnatinsa ta mayar da hankali kan gyaran tattalin arziki, inganta ayyukan gwamnati da dawo da amincewar jama’a bayan shekaru na rikicin siyasa.
Sai dai mulkinsa ya kare a 2026 bayan ya sanar da murabus, yana mai cewa ya amsa sakon jam’iyyarsa kan jagorancinsa.
Ficewar Starmer ya kara nuna irin sauyin da siyasar Birtaniya ta shiga cikin shekaru 10 da suka gabata.
Wanda ake sa ran zai gaji Starmer
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Andy Burnham, ya zama ɗan takarar da ake ganin zai gaji kujerar Firayim Ministan Birtaniya bayan murabus ɗin Keir Starmer daga Downing Street.
Bayan manyan jiga-jigan Labour sun nuna goyon baya gare shi, hanyar Burnham ta zama shugaba na ƙara bayyana cikin sauƙi yayin da jam’iyyar ta zabe shi matsayin shugaba.
A lokacin da Starmer ya sanar da murabus dinsa, masana sun ce 'yar manuniya ce ta nuna cewa Burnham zai tsaya takarar Firaministan Birtaniya don shugabantar kasar.
Asali: Legit.ng



