Sanatan Amurka da Ke Zuga Trump kan Yaƙar Iran da Sauran Manufofin Kasar Ya Rasu

Sanatan Amurka da Ke Zuga Trump kan Yaƙar Iran da Sauran Manufofin Kasar Ya Rasu

  • Sanatan Amurka mai shekara 71, wanda ke daya daga cikin manyan abokan Donald Trump ya yi bankwana da duniya
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya kwatsam, kamar yadda ofishinsa ya sanar
  • Sanatan ya shahara wajen ba Trump shawara kan manufofin ketare, musamman Iran da Rasha, kuma kwanan nan ya ziyarci Ukraine karo na 10

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - An shiga wani Irin yanayi a Amurka bayan sanar da rasuwar fitaccen sanata da ke tare da Donald Trump.

Sanatan Amurka Lindsey Graham, daya daga cikin manyan abokan Donald Trump a Majalisa, ya rasu.

Rahoton ya ce marigayin ya rasu da yammacin Asabar 11 ga watan Yulin 2026 bayan gajeriyar rashin lafiya da ta zo ba zato.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarkin Qatar da ya daga darajar kasar a duniya ya rasu yana da shekaru 74

Ofishinsa ya sanar da rasuwar cikin wata sanarwa amma bai bayyana karin bayani kan musabbabin mutuwarsa ba.

Sanatan mai wakiltar South Carolina yana da shekaru 71 a duniya, kuma yana neman wa'adi na biyar a Majalisar Dattawan Amurka.

Iyalan Graham sun bukaci a ci gaba da yi musu addu'a tare da girmama bukatarsu ta samun sirri yayin da suke fuskantar wannan babban rashi.

An zabi Graham a Majalisar Dattawa a shekarar 2002, sannan ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2016 inda ya soki Donald Trump sosai.

Daga baya ya zama daya daga cikin aminan Trump mafi kusa, yana yawan ganawa da shi tare da kasancewa abokin wasan golf na shugaban kasar.

Graham ya kasance mai ba Trump shawara kan harkokin ketare, musamman batutuwan Iran da Rasha, kuma Juma'a ya sanar da yarjejeniya kan takunkuman Rasha.

Kafin rasuwarsa, Graham ya kai ziyara ta goma zuwa Ukraine inda ya gana da Shugaba Volodymyr Zelenskyy, wanda ya gode masa saboda goyon bayansa ga sojojin kasar.

Tun yana dan Majalisar Wakilai a shekarun 1990, Graham ya goyi bayan manufofin da suka takaita Iran tare da hana ci gaban shirinta na makamai masu linzami.

Kara karanta wannan

Alaka ta munana: An hada baki da sojoji aka tsare dan majalisar Amurka a Isra'ila

Haka kuma ya yabawa matakin Trump na kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran a bara, sannan ya goyi bayan rikicin da ya fara watanni kadan da suka gabata.

A lokacin wa'adin Trump na biyu, Graham shi ne shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manyan dokoki.

Kwamitinsa ya jagoranci tsarin sulhu na majalisa wanda ya bai wa 'yan Republican damar amincewa da dokoki, ciki har da dokar haraji ba tare da katsalandan ba.

A baya ya jagoranci Kwamitin Shari'a na Majalisar Dattawa lokacin da aka tabbatar da Amy Coney Barrett a matsayin alkalin Kotun Koli ta Amurka.

Ana sa ran Graham zai sake jagorantar wannan kwamitin idan jam'iyyar Republican ta ci gaba da rike rinjaye a Majalisar Dattawa bayan zaben tsakiyar wa'adi na bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.