Tsugune ba Ta Ƙare ba, Amurka Ta Sake Bijiro da Maganar Sulhu da Ƙasar Iran
- Ministan tsaro a Amurka ya yi magana game da yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran inda ya ce shirin na nan duk da hare-hare sama
- Pete Hegseth ya bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da kare zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz domin tabbatar da cinikayyar duniya ba ta tsaya ba
- Janar Dan Caine ya ce sama da ma’aikatan ruwa 22,500 sun makale cikin Tekun Fasha saboda tashin hankalin Iran da hare-haren jiragen ruwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Ministan tsaro a Amurka, Pete Hegseth ya dawo da maganar tsagaita wuta a yaƙi da Isra'ila.
Hegseth ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran tana nan duk da karuwar rikice-rikice da hare-hare daga Tehran.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Pentagon ranar Talata 5 ga watan Mayun shekarar 2026, cewar tashar Al Jazeera.
Shirin Amurka kan mashigar Hormuz
Hegseth ya ce Gwamnatin Amurka za ta ci gaba da kare mashigar Hormuz tare da tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci.
Ya ƙara da cewa shugaban ƙasa Donald Trump ne zai yanke hukuncin ko hare-haren Iran sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta.
Shugaban hafsoshin sojin Amurka Janar Dan Caine ya ce Iran ta kai hare-hare sama da 10 kan sojojin Amurka tun bayan fara yarjejeniyar ranar 8 ga Afrilu 2026.
Ya kuma ce Iran ta harba bindigogi kan jiragen ruwa sau tara tare da kwace jiragen dakon kaya biyu.
Caine ya bayyana hare-haren Iran a matsayin ƙananan hare-haren tsokana da suka shafi yankin kudancin mashigar Hormuz.
Ya ce gwamnatin Iran na fama da matsin lamba yayin da take ƙoƙarin cigaba da iko a cikin ƙasar, cewar rahoton BBC.

Source: Getty Images
Matakin da sojojin Amurka ke dauka
A ranar Litinin 4 ga watan Mayun 2026, sojojin Amurka sun ƙaddamar da aikin “Project Freedom” domin bai wa jiragen ruwa damar wucewa cikin mashigar Hormuz ba tare da tsoron hare-haren Iran ba.
Janar Caine ya bayyana cewa ma’aikatan ruwa 22,500 sun makale a cikin Tekun Fasha kan jiragen ruwa sama da 1,550 saboda tashin hankalin yankin.
Hegseth ya ce jiragen ruwan Amurka biyu sun ratsa mashigar Hormuz tare da rakiyar jirgin yaƙin Amurka cikin nasara.
Ya ce Iran ta kasa hana zirga-zirgar jiragen ruwa duk da ikirarin cewa tana iko da mashigar.
A yayin taron, Hegseth da Caine sun yi watsi da rahotannin da ke cewa Iran na amfani da dabbar dolphin masu ɗauke da bama-bamai wajen kai hare-hare.
Hormuz: Ana shirin rufe wata mashigar ruwa
A wani labarin, an ji cewa wani jami’i a Gwamnatin ‘yan Houthi ya yi barazanar rufe mashigar Bab al-Mandeb idan manufofin Donald Trump suka ci gaba.
Hussein al-Ezzi ya ce idan Sanaa ta rufe mashigar, babu wanda zai iya sake bude ta, yana kira a dakatar da manufofin da ke hana zaman lafiya.
Mashigar Bab al-Mandeb hanya ce mai muhimmanci ga kasuwancin duniya, tana hada Tekun Ja da Gulf of Aden tare da saukaka zirga-zirgar mai da kaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

