UAE Ta Cire Takunkumin Hana 'Yan Najeriya Biza? Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Gaskiya

UAE Ta Cire Takunkumin Hana 'Yan Najeriya Biza? Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Gaskiya

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ƙaryata rahoton da ke cewa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta ɗage takunkumin da ta sanya wa Najeriya
  • A cewar fadar shugaban ƙasar, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Najeriya ko ta kasar UAE kan wannan batun da ke ta yaɗuwa
  • Ku tuna cewa a shekarar 2022, gwamnatin UAE ta haramtawa wasu ƙasashen Afirka 20, ciki har da Najeriya, tafiye-tafiye zuwa cikinta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Har yanzu ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ba ta ci gaba da bayar da biza ga ƴan Najeriya da ke son zuwa ƙasar ba, a cewar fadar shugaban ƙasa.

Kafofin yada labarai da dama sun ruwaito cewa UAE a ranar Litinin, 4 ga Maris, ta dage takunkumin hana matafiya ƴan Najeriya biza.

Kara karanta wannan

NYCN ta tsoma baki kan yunƙurin tsige mataimakin gwamnan PDP, ta faɗi mafita 1 tak

Ba a cire takunkumin hana 'yan Najeriya bizar Dubai ba
UAE ta hana 'yan Najeriya da wasu kasashe 20 shiga cikinta Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sai dai, Bayo Onanuga, mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, ya ƙaryata hakan a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X, a ranar Talata, 5 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Oktoban 2022, UAE ta haramtawa ƴan ƙasashen Afirika 20 shiga cikin iyakokinta.

Jerin ƙasashen Afirika da UAE ta daina ba biza

Daga cikin ƙasashen da abin ya shafa akwa Najeriya, Uganda, Ghana, Saliyo, Sudan, Kamaru, Laberiya, Burundi, Jamhuriyar Guinea, Gambiya, Togo, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Sanagal, Benin, Ivory Coast, Congo, Rwanda, Burkina Faso, Guinea-Bissau, Comoros, da Jamhuriyar Dominican.

Tun bayan dakatarwar ne dai ƙasashen UAE da Najeriya ke takun saƙa a tsakaninsu dangane da batun adadin jiragen sama da zu riƙa shige da fice da hana zirga-zirga.

Da yake mayar da martani a ranar Talata, Bayo Onanuga ya rubuta cewa:

Kara karanta wannan

Sauki ya zo: An samu hanyar da za a kawo karshen 'yan bindiga a Najeriya

"UAE ba ta dawo da bayar da biza ga ƴan Najeriya ba. Takardar da ke yawo ba gwamnatin Najeriya ko UAE ba ne suka fitar da ita."

Ƙasashen da Ƴan Najeriya Za Su Iya Zuwa Ba Biza

A wani rahoton da aka kawo a baya, mun jero muku ƙasashen da ƴan Najeriya za su iya zuwa ba tare da biza ba.

Ƴan Najeriya dai na da ƙasashe 45 a duniya waɗanda za su iya zuwa ba tare da biza ba, abin da kawai za su yi amfani da shi shine fasfo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel