2024: Ƙasashe 45 da Ƴan Najeriya Za Su Iya Zuwa Ba Tare da Biza Ba

2024: Ƙasashe 45 da Ƴan Najeriya Za Su Iya Zuwa Ba Tare da Biza Ba

 • Najeriya ta ƙara samun daraja a jerin ƙasashen da ke ta ƙarfin fasfo, wanda ke ba ƴan ƙasar wani tagomashi yayin tafiye-tafiye zuwa turai
 • Wani sabon kididdiga da shafin Henley Passport Index ya fitar, ya nuna cewa yanzu Najeriya ta koma ta 95 a ƙasashe 104 masu ƙarfin fasfo
 • Legit Hausa ta tattaro bayani kan jerin kasashe 45 da ƴan Najeriya za su iya zuwa ba tare da sun yi amfani da biza ba, sai dai da fasfo kawai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Shafin Henley Passport Index, wanda ya lissafa wasu fasfo mafi karfin iko a duniya, ya ce 'yan Najeriya na da kasashe kusan 45 da za su iya zuwa ba tare da biza ba, kawai za su yi amfani ne da fasfo dinsu.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: An yi hasashen Dala za ta kai N4000 kafin karshen 2024, an fadi dlalili

Wannan dai na kunshe ne a cikin sabon jaddawali wanda ya nuna cewa Najeriya ce ta 95 a cikin kasashe 104 masu karfin fasfo.

Jerin kashe 45 da 'yan Najeriya ba sa bukatar biza idan za su je
Jerin kashe 45 da 'yan Najeriya ba sa bukatar biza idan za su je, sai dai su yi amfani da fasfo.
Asali: Getty Images

Fasfo din Najeriya ya kara daraja a duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanan Henley Passport Index galibi na dogara ne akan kebantaccen bayanai daga kungiyar sufurin jiragen sama ta duniya (IATA). u and Haiti, Leadership News ta ruwaito.

Bisa kididdigar da aka yi, Najeriya ta wuce Gana, Guinea, Kenya, Lesotho, Moroko, Benin da Namibiya wadanda ke a matsayi na 76, 83, 67, 65, 71, 79 da 65.

Kasashe 45 da ‘yan Najeriya za su iya zuwa da fasfo ba tare da biza ba:

 1. Barbados
 2. Benin
 3. Burkina Faso
 4. Burundi
 5. Kambodiya
 6. Kamaru
 7. Tsibirin Cape Verde
 8. Chadi
 9. Tsibirin Kamoro
 10. Tsibirin Cook
 11. Cote d'Ivoire
 12. Djibouti
 13. Jamhuriyar Dominican
 14. Fiji
 15. Gana
 16. Guinea
 17. Guinea-Bissau
 18. Haiti
 19. Iran
 20. Kenya
 21. Kiribati
 22. Lebanon
 23. Laberiya
 24. Madagaska
 25. Maldives
 26. Mali
 27. Mauritiana
 28. Mauritius
 29. Micronesia
 30. Montserrat
 31. Mozambique
 32. Nijar
 33. Niue
 34. Tsibirin Palau
 35. Rwanda
 36. Samoa
 37. Senegal
 38. Sierra Leone
 39. Somaliya
 40. St. Kitts da Nevis
 41. Gambiya
 42. Timor-Leste
 43. Togo
 44. Tuvalu
 45. Vanuatu

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Jerin ƙasashe 5 da ya kamata ku ziyarta a 2024

A wani rahoton, Legit Hausa ta tattaro bayani game da wasu kasashe wadanda ya kamata ace ƴan Najeriya sun ziyarta a 2024 don yawon bude ido.

Wadannan kasashen wadanda suke cike da al'adu masu burgewa, gine-gine masu ban sha'awa, na neman masu yawon bude ido su ziyarce su don ganin abubuwan ban mamaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel