Yadda aka Ce Dan Amurka Yana ba Iran Bayanan Sirrin Isra'ila domin Ruguza Ta
- Gwamnatin Isra'ila ta kama wani matashi ɗan ƙasar Amurka mai shekaru 20 da haihuwa kan zargin yi wa hukumomin leƙen asirin Iran aiki
- Isra'ila na zargin matashin da ɗaukar hotuna da tattara bayanan sirri kan muhimman wurare a cikin Isra'ila, inda aka ce Iran ce ke ba shi kudi
- Bayan binciken farko, rundunar 'yan sandan Isra'ila ta ce za a gurfanar da shi gaban kotu a nan gaba kadan, inda ta ce za ta cigaba da kakkabe irinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Isra'ila - Hukumomin Isra'ila sun kama wani ɗan ƙasar Amurka bisa zargin gudanar da ayyukan leƙen asiri a madadin hukumomin leƙen asirin Iran.
Legit ta tabbatar da cewa 'yan sandan Isra'ila da hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet suka sanar da kama shi a ranar Talata, 30 ga Yunin 2026.

Source: Getty Images
Roya News ta wallafa cewa an kama wanda ake zargin, mai shekaru 20, tun a ranar 9 ga Yunin 2026, ƙarƙashin umarnin kotu da ya hana fitar da bayanan shari'ar, sai dai daga baya an sassauta wannan umarni.
Laifin dan Amurka a Isra'ila
A cewar 'yan sanda, ana tuhumarsa da manyan laifuffukan da suka shafi tsaro, waɗanda suka jefa tsaron Isra'ila da al'ummarta cikin haɗari.
Lamarin ya kara daukar hankali ne musamman lura da zargin ya shafi tallafawa Iran da bayanai alhali tana zaman doya da manja da Isra'ila.
Zargin da ake wa dan Amurka
Masu bincike sun ce wanda ake zargin ya kasance yana ci gaba da hulɗa da jami'an leƙen asirin Iran na tsawon watanni kafin kama shi.
A wannan lokacin, ana zargin an ba shi umarnin bibiya, ɗaukar hotuna da tattara bayanai kan wurare masu muhimmanci a faɗin Isra'ila.
Ana kuma zargin cewa yana karɓar kuɗi kaɗan-kaɗan, daga dala goma-goma zuwa ɗaruruwan daloli, bayan kammala kowane aiki.
Bayanin 'yan sandan Isra'ila
Babban sufeton 'yan sandan Isra'ila, Amichai Fanta, ya ce ana sa ran shigar da matashin ƙara gaban kotu cikin kwanaki masu zuwa.
Times of Israel ta wallafa cewa hukumomi sun ƙi bayyana ko ɗan ƙasar Amurkan ya shiga Isra'ila ne a matsayin baƙo ko kuma mazauni.
“Za mu ci gaba da gano da kuma bankado irin waɗannan laifuffuka, mu kama masu aikata su, sannan mu gurfanar da duk wanda ya jefa tsaron ƙasa da al'umma cikin haɗari,”
In ji Fanta.

Source: Getty Images
Isra'ila ta zargi kasar Iran
Hukumomin Isra'ila sun ce wannan lamari na nuna ci gaba da abin da suka bayyana a matsayin yaƙin leƙen asiri mai ƙarfi da Iran ke gudanarwa.
Sun ce tun daga shekarar 2023, Isra'ila na fuskantar ƙaruwar ƙungiyoyin leƙen asiri na cikin gida da Tehran ke ɗaukar nauyinsu.
A cewar hukumomin, an gurfanar da aƙalla 'yan ƙasar Isra'ila 60 cikin shekaru uku da suka gabata kan zargin cin amanar ƙasa da leƙen asiri.

Kara karanta wannan
NDC ta ɗauki mataki bayan hukuncin kotu, ta fara tura sunayen 'yan takara ga INEC
An raunata sojan Isra'ila
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Isra'ila ta tabbatar da cewa an jikkata sojan ta yayin sintiri a Kudancin kasar Lebanon.
Sojojin Isra'ila sun sanar da cewa wasu abubuwan fashewa ne suka tashi da sojan, lamarin da ya sanya ya samu munanan raunuka a jikin sa.
A daya bangaren kuma, Lebanon ta sanar da cewa Isra'ila ta kai hari kasar a ranar Litinin, 29 ga Yunin 2026, lamarin da ya jawo barna sosai.
Asali: Legit.ng

