A karshe, gwamnatin Yobe ta yi martani kan mace-macen mutane a jihar

A karshe, gwamnatin Yobe ta yi martani kan mace-macen mutane a jihar

Gwamnatin jihar Yobe ta yi martani game da rahotannin mace macen da ake samu a jihar cikin sati daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa fiye da mutum 100 ne suka mutu cikin sati daya bisa la'akari da alkalluman da aka samu daga garurruwan Potiskum, Gashu’a da Nguru.

Mataimakin shugaban kwamitin kar ta kwana na yaki da COVID-19 a jihar wadda shine kuma kwamishinan Lafiya na jihar, Dr Muhammad Lawan Gana ya ce gwamnatin za ta yi bincika gawarwakin wadanda suka mutu don gano dalilin mace-macen a jihar.

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Alhamis 7 ga watan Mayu a gidan gwamnati da ke Damaturu.

A karshe, gwamnatin Yobe ta yi martani kan mace macen mutane a jihar
A karshe, gwamnatin Yobe ta yi martani kan mace macen mutane a jihar. Hoto daga Aljazeera
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Nasarawa: Yadda mata ta daba wa miji wuka har lahira saboda amsa wayar budurwa

A cewarsa, a kan samu karin mace mace a lokacin zafi ba ma a Yobe kadai ba har da wasu sassan Najeriya.

Ya ce ba daidai bane a alakanta mace macen da COVID-19 a halin yanzu tunda ba a gudanar da gwaje gwaje ba an tabbatar da hakan.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ba za tayi kasa a gwiwa ba wurin kiyaye lafiyar mutanen jihar inda ya ce a halin yanzu tana samar da takunkumin fuska da za ta raba wa mutane kyauta da nufin dakile yaduwar COVID-19.

Ya bayyar da tabbacin cewa nan ba da dade wa ba za a samar da cibiyar killace majinyata a garurruwan Bade, Potiskum da Nguru.

A wani labari na daban, hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Nasarawa ta kama wata mata mai juna biyu mai shekaru 22, Veronica Boniface, saboda kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka saboda ya amsa wayar budurwarsa.

Da ake holen wacce ake zargin a hedkwatan hukumar a Lafia, Kwamandan NSCDC a jihar, Habu Fari, ya ce an kama matar ne a garin Obene a karamar hukumar Keana bayan samun bayanan sirri.

Veronica ta amsa cewa ita ta kashe mijinta amma ta nemi ayi mata rangwame inda ta ce sharrin shaidan ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel