"Suna Farin Ciki": Shugaba Trump Ya Fadi Nasarar da Ya Samu a Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake yin magana kan yakin da kasarsa ta yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Donald Trump ya bayyana cewa ya samu nasara kan daya daga cikin abubuwan da ya so ya cimmawa a yakin wanda aka fara a watan Mayun 2026
- Shugaban kasar na Amurka ya jaddada cewa kasashe da dama suna farin ciki kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Iran - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce ya cimma nasarar ‘sauya gwamnati’ a Iran.
Shugaba Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cimma nasarar gwamnati a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai, a ranar Laraba, 17 ga watan Yunin 2026.
Trump ya yi magana kan shugabannin Iran
Trump ya sake jaddada kalaman da ya yi a makwannin da suka gabata cewa gwamatinsa ta cimma nasarar “sauya gwamnati” a Iran.
Yayin da yake magana kan jagororin kasar na yanzu, Trump ya ce yana tsammanin za su gudanar da jagorancinsu cikin wani salo na daban.
“Ina tsammanin za su gudanar da harkokinsu cikin wani salo na daban."
- Donald Trump
Meyasa Trump ya ki ci gaba da yaki da Iran?
Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa da zai iya ci gaba da yaƙin, amma baya son ganin an samu koma baya ta fannin tattalin arziki.
"Ba na son ganin babban koma-bayan tattalin arziki. A duk lokacin da muka yi magana kan yiwuwar samar da zaman lafiya, kasuwa tana tashi sama kamar kumbon sararin samaniya."
- Shugaba Donald Trump
Trump ya ce ana farin ciki da yarjejeniyar
Yayin da yake yaba wa yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) da aka cimma da Iran, shugaban na Amurka ya ce ya tattauna kan wannan yarjejeniya ta “tarihi” da ƙasashe abokan kawance da dama, tare da ƙasashen kungiyar G7.
“Shugabannin ƙasashe da firaministoci da dama, suna matukar farin ciki da muka cimma wannan yarjejeniya, kowannensu."
“Babu wata ƙasa guda da ta zo mana ta ce, ‘Don Allah yallabai, ka ci gaba da jefa masu bama-bamai, don Allah ka ci gaba da jefa bama-bamai’. Wawayen mutane ne kawai ke faɗar hakan.”
- Shugaba Donald Trump

Source: Getty Images
Karanta wasu labaran kan Trump
- Trump ya ballo ruwa, 'yan majalisa sun bude masa wuta kan shirin yarjejeniya da Iran
- Shugaba Trump ya ragargaji Iran duk da shirin kulla yarjejeniya
- Duniya za ta huta: Trump ya ce yaki da Iran ya zo karshe, babu sauran kai hari
Trump ya soki Benjamin Netanyahu na Israila
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi kakkausar suka kan firaministan Israila, Benjamin Netanyahu.
Shugaban kasar na Amurka ya bayyana cewa ya kamata Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi taka tsan-tsan game da Lebanon.
Donald Trump ya ce yana da kyakkyawar alaƙa da Netanyahu, amma ya yi ikirarin cewa da tuni an tarwatsa Isra’ila tun da dadewa da bai sa baki ba.
Asali: Legit.ng

