Yadda Donald Trump Ya Tsorata, Ya Ki Zuwa China da Wayar Shi
- Shugaba Donald Trump ya je birnin Beijing domin halartar wani taron koli na kwanaki biyu, wanda shi ne ziyararsa ta farko zuwa China tun shekarar 2017
- Maimakon tafiya da waya, Trump zabi amfani da na’urorin sadarwa na wucin gadi masu takaita bayanai, kwamfutocin tafi-da-gidanka na wucin gadi
- Rahotanni sun nuna cewa jami'an Trump sun yi haka ne domin rage barazanar leken asiri da kutse ta yanar gizo a yayin da za su zauna a kasar China
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaba Trump bai yi amfani da wayarsa ta salula da yake matukar so ba yayin da yake China, daya daga cikin matsalolin da shi da ma’aikatan Fadar White House suka fuskanta a Beijing.
An gargadi shugaban, kamar yadda aka gargadi duk masu tafiya zuwa China, da kada su yi amfani da na’urorinsu na kashin kai domin kare bayanansu daga masu kutse ta yanar gizo.

Source: Getty Images
New York Times ta rahoto cewa hakan ya sanya kwanakin suka zama masu wahala ga Trump, wanda aka san yana yawan amfani da waya.
Trump bai je China da waya ba
Wani jami’in White House ya tabbatar da cewa shugaba Trump bai yi amfani da wayarsa ta kashin kai ba yayin da yake kasar China.
Sakonni a shafinsa na Truth Social sun ragu yayin taron, kuma an ce ana wallafa su ne daga Washington DC, inda wasu ma’aikatan White House ke aiki bisa lokacin Beijing suna tallafawa daga nesa.
Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ba shugaban kadai ne bai je China da wayar sa ta asali ba, ciki har da wadanda suka taka masa baya.
Ma’aikatan gwamnati sun yi amfani da wayoyi na wucin gadi da kuma adireshin imel na wucin gadi yayin taron na kwanaki biyu — duk a matsayin wani bangare na kokarin White House na kare bayanai tare da tabbatar da tafiyar tana gudana lafiya.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka tana gargadin ‘yan Amurka masu tafiya China cewa babu tabbacin sirri a kan hanyoyin sadarwar wayar salula ko wasu hanyoyin sadarwa a China.

Source: Getty Images
Wasu sun ajiye waya a jirgi
Ga ma’aikatan White House, an adana na’urorinsu na kashin kai a cikin jakunkunan Faraday a cikin jirgin Air Force One, wadanda ke toshe duk wata alamar kutse, ciki har da GPS, Wi-Fi, Bluetooth da RFID.
ND TV ta wallafa cewa jakunkunan suna kare bayanai masu muhimmanci daga kutse ta yanar gizo da sauransu daga nesa.
An cire mafi yawan muhimman manhajoji da daga wadannan na’urori domin su zama “na’urori masu kariya” da aka tsara domin rike bayanai idan aka yi kutse.
Taiwan: China ta gargadi Trump
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasar China, Xi Jinping ya gargadi Donald Trump game da Taiwan yayin da suka hadu a birnin Beijing.
Shugaba Xi ya bayyana wa Donald Trump karara cewa tsoma bakin Amurka a kan Taiwan zai iya jawo rikici a tsakanin kasashen biyu.
Donald Trump ya tattaunawa da shugaban China, Xi Jinping, kan batutuwa masu sarkakiya, ciki har da yakin Iran da bude Hormuz.
Asali: Legit.ng

