Ana Zargin Trump da Netanyahu Sun Yi Cacar Baki game da Sake Kai Hari kan Iran
- Rahotanni sun ce an samu sabani mai zafi tsakanin Shugaba, Donald Trump da Firayim minista, Benjamin Netanyahu
- Lamarin ya biyo bayan zargin cewa shugabannin biyu sun samu sabani kan sake kai hari Iran bayan tattaunawar sirri mai tsawo
- Wani rahoto ya bayyana cewa Isra’ila da Amurka sun yi shirin mayar da Mahmoud Ahmadinejad kan mulki bayan kashe Ayatollah Ali Khamenei a farkon yakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Rahotanni daga kafafen yada labarai sun bayyana cewa an samu sabani mai tsanani tsakanin Donald Trump da Benjamin Netanyahu.
Majiyoyin sun tabbatar da cewa rigimar ta barke ne tsakaninsu kan yiwuwar sake kai hare-hare kan Iran.

Source: Getty Images
Rahoton Daily Mail ya ce hakan ya biyo bayan tattaunawar waya mai tsawo da zafi tsakanin shugabannin biyu.
Mahangar Netanyahu kan tattaunawa da Iran
An ce Netanyahu yana ganin tattaunawar zaman lafiya da Tehran ba za ta haifar da mafita ba, saboda haka yana son Isra’ila ta koma kai hare-haren soji.
Sai dai Trump yana matsa kaimi wajen ganin an cimma yarjejeniya da Iran domin kasar ta dakatar da shirinta na mallakar makaman nukiliya kafin sake komawa yaki.
Rahoton ya zo ne bayan jaridar The Times of Israel ta bayyana cewa Isra’ila tare da amincewar Trump sun shiga yakin da wani babban shiri na mayar da Mahmoud Ahmadinejad kan mulkin Iran.
An ce shirin ya tanadi cewa bayan kashe Ayatollah Ali Khamenei a hare-haren farko, Ahmadinejad zai zama sabon shugaban Iran domin jagorantar kasar bayan rikicin.
Sai dai shirin ya rushe tun ranar farko bayan wani harin Isra’ila ya raunata Ahmadinejad a gidansa da ke Tehran, inda aka ce ana kokarin kubutar da shi daga tsarewa.
Rahoton ya ce Ahmadinejad ya yi imanin cewa Amurka na son ya taka muhimmiyar rawa a shugabancin Iran bayan yakin ya lafa gaba daya.
Wani makusancin tsohon shugaban Iran ya shaida cewa Amurka ta dauke shi tamkar yadda Delcy Rodríguez ta zama jagora a Venezuela bayan canjin siyasa.

Source: Facebook
Harin da ya kashe jami'an tsaron Iran
An kuma bayyana cewa jami’an tsaron da aka ce sun mutu a harin ba masu gadi kawai ba ne, jami’an rundunar 'Revolutionary Guard' ne da ke kula da shi tare da tsare shi a gida.
Bayan mutuwar jami’an, Ahmadinejad ya yanke hulda da jami’an leken asirin kasashen Yamma saboda ya rasa kwarin gwiwa kan shirin sauya gwamnatin Iran.
Rahotanni sun ce hare-haren farko na Isra’ila sun kashe Ayatollah Ali Khamenei tare da wasu manyan jami’an gwamnatin Iran a Tehran.
Sai dai wasu jami’an gwamnatin Trump sun yi gargadin cewa kashe Khamenei ba zai tabbatar da sauya gwamnati cikin sauki ba kamar yadda Isra’ila ke tsammani.
Daraktan CIA John Ratcliffe ya bayyana batun sauya gwamnati a Iran a matsayin abin dariya, yayin da Marco Rubio ya yi watsi da wannan tunani
Croatia ta ki amincewa da sabon jakadan Isra'ila
A baya, an ji cewa shugaban ƙasar Croatia, Zoran Milanovic, ya yi fatali da shirin Isra'ila na turo sabon jakada zuwa kasar yayin da ake cikin yaki da Iran.
Milanovic ya dauki matakin ne kin amincewa ne da hakan saboda manufofin gwamnatin Isra’ila da rikicin diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
Fadar shugaban Croatia ta ce Isra’ila ta karya ƙa’idar diflomasiyya bayan bayyana sunan jakadan kafin samun amincewar shugaban ƙasar a hukumance.
Asali: Legit.ng


