Kasar Isra’ila Ta ‘Bankado’ Wani Shirin da Iran Ke Kullawa a Birtaniya

Kasar Isra’ila Ta ‘Bankado’ Wani Shirin da Iran Ke Kullawa a Birtaniya

  • Kasar Isra’ila ta yi Allah wadai da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da amfani da ofishin jakadancinta a London domin ta'addanci
  • Isra'ila ta ce Iran amfani da ofishin wajen daukar mutane don ayyukan ta’addanci, tana cewa kariyar diflomasiyya ba za ta boye barna ba
  • Rahotanni sun nuna cewa jakadan Iran ya kira ‘yan kasarta da ke Birtaniya su shiga wani shirin “sadakar da kai”

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta yi Allah-wadai da Iran kan zargin kaddamar da wani shiri da ta ke yi a Birtaniya.

Kasar Isra'ila ta ce Iran a watan da ya gabata na daukar ‘yan ta’adda ta hanyar jakadancinta da ke Birtaniya da ke London.

Isra'ila ta zargi Iran da rura wutar ta'addanci
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Gil Cohen-Magen.
Source: Getty Images

Sakon jakadan Iran ga yan kasar a London

Rahoton Daily Mail ya ce ofishin jakadancin Tehran da ke London ya buƙaci mazauna Birtaniya da suke shirye su mutu domin gwamnatin Iran su shiga wani shirin 'shahada'.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Peter Obi sun samu tayin tikitin takara kai tsaye a zaɓen 2027

Jami’an ofishin jakadancin sun wallafa saƙon da ke ƙarfafa “’yan ƙasar Iran masu alfahari da ke zaune a Birtaniya” su yi rajista a shirin “sadaukar da rai”.

Sun buƙaci “dukkan jarumai da mutanen kirki ‘ya Iran” masu “sha’awar kare ƙasar Iran da jama’arta” su fito domin nuna haɗin kai, biyayya da kishin ƙasa.

Hakan ya biyo bayan wasu bayanai da ke cewa wai jakadan Iran a London ya ba yan kasarsa shawara game da wani shiri na musamman wanda zai amfane su a rayuwa.

Martanin Isra'ila kan sakon jakadan Iran a London

Shafin ofishin ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta wallafa martani a X inda ta yi Allah wadai da sakon da jakadan Iran ya tura ga yan kasarsa.

Ya ce:

"Ana zargin gwamnatin Iran da amfani da ofishin jakadancinta da ke Birtaniya wajen ɗaukar ‘yan ta’adda aiki.
'Ba za a bari a yi amfani da kariyar diflomasiyya a matsayin garkuwa don ayyukan ta’addanci ba. Ɗaukar mataki kan irin waɗannan ofisoshi martani ne da ya dace ga gwamnatin da ke amfani da diflomasiyya wajen yaɗa tashin hankali."

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani

Roger Macmillan, tsohon daraktan tsaro na Iran International, ya ce abin firgita ne yadda ake kokarin tsaurara ra’ayi a Birtaniya ta yanar gizo

Nadeh Fallah ya gargadi cewa dole Birtaniya ta haramta IRGC, yana cewa kungiyar na kokarin daukar mutane da yada tasiri a cikin kasar.

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya bayyana cewa za a gabatar da kudirin doka domin haramta IRGC a zaman majalisar dokoki mai zuwa.

Putin Ya Yi wa Iran Alkawari kan Yaki da Amurka

Mun ba ku labarin cewa firaminstan Rasha, Vladimir Putin ya yaba da jarumtakar jama'ar Iran yayin ziyarar ministan harkokin wajen Tehran, Abbas Araghchi.

Jagororin kasashen sun tattauna da juna ne yayain da ake cigaba da samun takaddama tsakanin Iran da Amurka kan mashigar Hormuz.

Abbas Araghchi ya bayyana cewa ya ziyarci kasar Rasha ne domin tattaunawa kan wasu muhimman abubuwa da suka shafi yaki da Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.