An kona wani dan Najeriya har lahira a kasar Afrika ta Kudu

An kona wani dan Najeriya har lahira a kasar Afrika ta Kudu

- An kona wani dan Najeriya a Rustenburg dake South Africa sakamakon motarsa da wasu ‘yan ta’adda da ba’asan ko suwanene suka sawa wuta

- Hukumar ‘Yan Sanda ta Arewa maso Kudu basu yadda cewa hakan nada alaka da rikicin zanga-zanga da akayi ba a farkon wannan makon

- Motoci biyu aka sawa wuta a warare daban daban, wanda wasu ‘yan ta’adda da ba’a san ko suwanene ba sukayi a rahotanni da aka samu

An kona wani dan Najeriya a Rustenburg dake Afriika ta Kudu sakamakon motarsa da wasu ‘yan ta’adda da ba’asan ko suwanene suka sawa wuta.

Hukumar ‘Yan Sanda ta Arewa maso Kudu basu yadda cewa hakan nada alaka da rikicin zanga-zanga da akayi ba a farkon wannan makon, wanda akayi game da bukatar cire North West Premier Supra Mahumapelo.

An kashe dan Najeriyan ne kasa da kwanaki 10 bayan kisan wani ThanksGod Okoro, mai shekaru 30, dan Ogbaku a karamar hukumar Awgu dake jihar Enugu, a Najeriya, wanda ke zama a kasar ta Afriika ta Kudu.

An kona wani dan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu
An kona wani dan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu

Motoci biyu aka sawa wuta a warare daban daban, wanda wasu ‘yan ta’adda da ba’a san ko suwanene ba sukayi a rahotanni da aka samu.

KU KARANTA KUMA: Saraki da Tambuwal sun bawa PDP ka’idoji na dawowa jam’iyyar

Kungiyar watsa labarai da Afriika ta Kudu ta ruwato cewa mai magana da yawun hukumr ‘Yan Sandan Ofentse Mokgadi, yace ba’a kama kowa ba har yanzu, amma dai yace sunan nan suna gudanar da bincike.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel