Onochie ta lissafa matakai 8 da gwamnatin tarayya ta dauka kan kin jinin 'yan Najeriya a Afirka ta Kudu

Onochie ta lissafa matakai 8 da gwamnatin tarayya ta dauka kan kin jinin 'yan Najeriya a Afirka ta Kudu

Biyo bayan ci gaba da kai farmaki da munanan hare-hare na kin jinin al'ummar Najeriya da kuma harkokin kasuwancin su a kasar Afirka ta Kudu, gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauki matakai.

Lauretta Onochie, hadimar shugaban kasa a kan kafofin sada na zumunta, ita ce ta bayyana hakan a ranar Laraba a kan shafin ta na Twitter, lamarin da ta ce shugaba Buhari ya dauki matakai sabanin yadda ake ikirarin cewa ya yi gum da bakin sa.

Mrs Onochie ta yi Allah wadai dangane da tababar kin jinin baki da ake yi a kasar Afirka Ta Kudu, biyo bayan hare-haren da aka zartar kan 'yan Najeriya a kwana-kwanan nan.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na sada zumunta, hadimar shugaban kasar ta zayyana matakai takwas da gwamnatin tarayya ta dauka:

1. Gwamnatin Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta fara biyan diyya ga dukkanin 'yan Najeriya da hare-haren ya shafa.

2. Gwamnatin Najeriya ta nemi a tabbatar da adalci ta hanyar hukunta wadanda ke da hannu wajen zartar da wannan munanan hare-hare.

3. Shugaba Buhari ya aika da jakada na musamman zuwa kasar Afirka ta Kudu domin bayyana rashin dadinsa kan wannan cin zarafi.

4. Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai dangane da rashin kulawa ta hukumomin tsaron kasar Afirka ta Kudu, a yayin da suka gaza bai wa 'yan Najeriya kariya da kuma tsare rayuka da dukiyoyinsu.

5. Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya ce mun ja layi kuma hakurin Najeriya ya kare kan irin hare haren da 'yan Afirka ta Kudu ke kaiwa kan yan kasar ta mazauna can.

6. Najeriya ta janye jakadanta da ke Afirika ta Kudu, Kabir Bala yayin da ta kuma fice daga taron tattalin arzikin duniya da aka fara gudanarwa a birnin Cape Town a wannan Laraba saboda hare-haren da ake kai wa ‘yan kasarta.

7. Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kausasa harshe tare da bayyana bacin rai akan wannan lamari, inda ya ce mahukuntan Afirka ta Kudu su fito su yi bayani da babban baki.

8. Gwamnatin Najeriya a yanzu tana kalubalantar kasar Afirka ta Kudu da ta kawo karshen wannan kin jini da kyamar baki cikin gaggawa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel