An Cafke Sojan Amurka da Ya Je Kama Shugaban Kasar Venezuela
- An kama wani sojan runduna ta musamman a Amurka bayan zargin ya samu $400,000 daga caca kan farmakin kama shugaban kasar Venezuela
- Hakan na zuwa ne bayan dogon bincike da kasar ta yi ta gano ya fitar da wasu bayanai 'yan sa'o'i kafin Amurka ta kaddamar da farmakin
- Hukumomin Amurka sun sanar da cewa sojan zai fuskanci hukunci ba sani ba sabo domin abin da ake zargin ya aikata babban laifi ne a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - An cafke wani sojan rundunar Amurka da ya je farmakin kama shugaban Venezuela, Nicolás Maduro, tare da tuhumarsa da zargin yin caca kan farmakin, inda ya samu ribar kusan $400,000.
A cewar takardar tuhuma da aka bayyana a ranar Alhamis, Sajan Gannon Ken Van ya bude asusu a karshen watan Disamban 2025 a dandalin caca na Polymarket.

Kara karanta wannan
Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100

Source: Getty Images
Dalilin kama sojan Amurka
CNN ta wallafa cewa ya saka kusan $32,000 cewa za a cire Maduro daga mulki kafin watan Janairun 2026, wanda hakan ke nuna ya san da shirin da Amurka ta yi.
Sai dai masu gabatar da kara sun ce Van na cikin masu tsarawa da aiwatar da farmakin, kuma yana da damar samun bayanan sirri kafin ya shiga cacar.
Rahotanni sun nuna cewa wannan ne ya sa ribar da ya samu mai yawa a cacan kama Maduro ta ja hankalin jami’an tsaro kuma aka fara bincike nan take.
Tuhumar da ake wa sojan Amurka
Van, wanda ke aiki a rundunar soja kuma yana sansanin Fort Bragg, na fuskantar tuhume-tuhume guda biyar da suka hada da satar bayanan gwamnati na sirri, amfani da su ba bisa ka’ida ba, zamba da kuma sata.
BBC ta rahoto cewa ana zargin ya yi caca har sau 13 tsakanin ranar 27 ga Disamba zuwa 2 ga Janairun 2026, inda na karshe ya zo ne ‘yan sa’o’i kafin a kai farmakin kama Maduro da daddare.
Masu gabatar da kara sun ce ya aika kudin ribarsa da ya haura dala $400,000 zuwa wani asusun kudi na Kirifto kafin ya mayar da su cikin wani asusun kasuwanci ta yanar gizo domin boye asalinsu.
“Dole ne wadanda aka daura musu alhakin kare sirrin kasa su kiyaye su, ba wai su yi amfani da su domin samun riba ta kashin kai ba,”
In ji Jay Clayton, lauya a Amurka a yankin Kudancin New York.

Source: Getty Images
Takardun kotu sun kuma nuna cewa an dauki hoton Van bayan aikin, yana tsaye a saman jirgin ruwa a teku da safe, sanye da kayan sojan Amurka tare da bindiga, yana tare da wasu jami’ai uku.
Sojan Iran da ya addabi Amurka
A wani labarin, mun kawo muku cewa sojan Iran maras sassauci, Janar Ahmad Vahidi ne ya ke kawo wa Amurka cikas wajen shawo kan Iran.
Janar Vahidi ya kasance daya daga cikin sojojin da suka rike manyan mukamai a baya, ciki har da minista, lamarin da ya kara masa tasiri.
Wasu na ganin a yanzu haka shi ke da fada a ji sosai a Iran duk da an nada Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addini na kasar.
Asali: Legit.ng
