Gwamnatin Abba Ta Bada Umarni a Ruguza Gidaje, Rigima Ta Kaure da ‘Yan Unguwa

Gwamnatin Abba Ta Bada Umarni a Ruguza Gidaje, Rigima Ta Kaure da ‘Yan Unguwa

  • An yi rikici tsakanin masu gidaje a Salanta da Jami’an Gwamnati da aka turo domin yin rushe-rushe
  • An ga faifen bidiyon wani Bawan Allah tare da iyalinsa cikin tsakar dare, ya na ikirarin an fasa masa kai
  • Jama’a sun kashe makudan kudi sun yi gine-gine a makarantun gwamnati, hukuma ta ce a ruguza su

Kano - A daren yau ne aka ji Gwamnatin jihar Kano ta shiga kwalejin fasaha na jihar Kano da yake Salanta, ta ruguza wasu gine-gine da aka yi.

Rahotannin da mu ka samu daga gidan rediyon Freedom sun bayyana an rushe gidajen jama’a da aka gina a cikin wannan makaranta ta gwamnati.

A tsakar daren Asabar ne aka ji rikici ya kaure tsakanin wasu mazauna wannan unguwa ta Salata da kwamitin da ke da alhakin rushe-rushen.

Kara karanta wannan

An Zabo Mana Bala'i: Kanawa Sun Fusata Da Rushe-Rushen Abba, Sun Hana Rushe Gidajensu

Abba Gida Gida a Kano
Gwamnan Kano, Abba Gida Gida Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Wasu daga cikin na kusa da Gwamnati, sun yi kokarin musanya wannan labari, su ka ce tuni aka ruguza gine-ginen kamar yadda aka bada umarni.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Bakin mulkin Fir'auna"

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Ahmad Prince Gandujiyya, an ga yadda wani magidanci yake kokawa a kan abin da ya kira mulkin Fir'auna.

Wannan mutum mai suna Aliyu Rabiu Alfawa ya zargi jami’an gwamnati da fasa masa kai da dukar mai dakinsa wanda ya ce ta na dauke da juna biyu.

Aliyu Alfawa ya shaida cewa su zaune aka yi wa gidansu lamba cewa za a ruguza shi duk da ya cika sharudan mallakar fili, kuma ya kashe N800m a ginin.

A bidiyon da yake yawo, attajirin ya koka cewa shi ba ‘dan siyasa ba ne, ya ce bai kamata rikicin Gwamna da Abdullahi Ganduje ya tozarta iyalinsu ba.

Kara karanta wannan

Akwai Dalili: Abba Gida Gida Ya Fadi Hikimar Ruguza Shatale-Talen Gidan Gwamnati

Abin da hukuma ta fadawa masu gidajen da aka gina a filin makaranta shi ne umarni aka bada daga sama, don haka sai dai su komawa addu’a kawai.

Me dokar kasa ta ce?

A zantawar Legit.ng Hausa da Barista Abba Hikima, ya shaida mana cewa a doka duk wanda ya samu CofO, shi yake da gida, amma fili na gwamnati ne.

Lauyan ya ce ko da gwamnatin jiha ta karbe filayen, babu abin da ya halatta ayi wa al’umma da gine-ginen mutane saboda ba dukiyar hukuma ba ce.

Baya ga haka, rahoton ya kara da cewa jami’an gwamnati sun cigaba da ruguje shagunan da aka gina a filin masallacin Idin Kofar Mata a Kano.

Ruguza shagu a filin idi

Gwamnatin NNPP ta fake da sunan tsaro, ta ce bai dace a yanka shaguna a wurin yin ibada ba. An rahoto Rabiu Kwankwaso ya na bayani kan batun.

Da yake maida martani, Abdullahi Ganduje ya ce masarauta ke da iko da masallacin, kuma ta nemi ta gina shaguna domin samun 'yan kudin shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel