Wata mahaukaciyar guguwa tayi sanadiyyar asarar gidaje sama da 1,000 a wata jiha a arewacin Najeriya

Wata mahaukaciyar guguwa tayi sanadiyyar asarar gidaje sama da 1,000 a wata jiha a arewacin Najeriya

Mutum daya ya mutu sannan mutane uku suna cikin wani hali, dalilin wata guguwa data lalata kauyuka 12 a kananan hukumomi 5 a cikin jihar Jigawa, a rahoton da sakataren hukuma taimakon gaggawa ta kasa ya bayar, Yusuf Sani Babura

Wata mahaukaciyar guguwa tayi sanadiyyar asarar gidaje sama da 1,000 a wata jiha a arewacin Najeriya
Wata mahaukaciyar guguwa tayi sanadiyyar asarar gidaje sama da 1,000 a wata jiha a arewacin Najeriya

Mutum daya ya mutu sannan mutane uku suna cikin wani hali, dalilin wata guguwa data lalata kauyuka 12 a kananan hukumomi 5 a cikin jihar Jigawa, a rahoton da sakataren hukuma taimakon gaggawa ta kasa ya bayar, Yusuf Sani Babura. Babura ya bayyanawa manema labarai jiya a Dutse babban birnin jihar cewa, guguwar ta lalata gida je sama da guda dubu daya a kananan hukumomin, Guri, Kiyawa, Dutse, Gumel da kuma Babura.

DUBA WANNAN: Rikici na neman barkewa a majalisa kan shugaba Buhari

"Mutum daya ya mutu a karamar hukumar Kiyawa bayan gini ya fado mishi. Sai kuma mutane uku da suka samu karaya a kafafuwan su a kauyen Adiyani dake karamar hukumar Guri bayan suma gini ya fado musu a wurare daban daban," inji shi.

A fadar shi, yace abin ya shafi kowanne kauye a yankin kananan hukumomin Guri da Kiyawa, sai kuma kauyuka guda bakwai a yankin karamar hukumar Dutse, sai biyu a karamar hukumar Babura da Gumel.

Yace a kauyen Adiyani dake karamar hukumar Guri, mutane 305 sunyi asarar dakuna 543, a kauyen shuwarin kuma dake karamar hukumar Kiyawa mutane 108 sunyi asarar dakuna 228, sai kuma kauyukan da suka hada da Warwade, Sayasaya, Sabon Gari, Jidawa, Tumballe, Sabuwar Takur, Jigawar Habuba duk dake karamar hukumar Dutse, mutane 273 sunyi asarar dakuna 456, yayinda mutane 58 suka yi asarar dakuna 84 a kauyukan Ajja, Dorawa, dake karamar hukumar Babura, sai kuma karamar hukumar Gumel da mutane 101 suka yi asarar dakuna 208 sanadiyyar guguwar.

Ya ce hukumar taimakon gaggawar ta dauki rahoton duk wuraren da lamarin ya shafa, sannan kuma zata kawo taimako idan ta gama tsara yanda lamarin zai kasance.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: