Turkiyya: An Gano Kasar da Isra'ila za Ta Sako a gaba bayan Iran

Turkiyya: An Gano Kasar da Isra'ila za Ta Sako a gaba bayan Iran

  • Ministan harkokin wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya yi gargadin cewa Isra’ila na iya mayar da hankali kan wata kasar a Gabas ta Tsakiya
  • Isra'ila ta sako Iran a gaba har ta kai ta hada kai da Amurka wajen kai harin da ya kashe jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamnei
  • Hakan Fidan ya bayyana damuwa kan hare-haren Isra’ila a Lebanon da Syria, tare da yiwuwar barazana ga yankin Gabas ta Tsakiya baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Turkiye – Ministan harkokin wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya bayyana cewa Isra’ila na iya karkatar da hankalinta wajen kallon Turkiyya a matsayin sabon abokin gaba a yankin, bayan Iran.

Fidan ya bayyana cewa Isra’ila na iya neman ayyana Turkiyya a matsayin sabon abokin gaba bayan Iran, yana mai cewa tsarin siyasar Isra’ila na dogaro da gano wani abokin gaba a waje domin ci gaba da wanzuwa.

Kara karanta wannan

Kasar Afrika ta gargadi Iran, za ta tura sojoji 500,000 su kwace Tehran

Turkiyya ta ce Isra'ila ta fara neman ayyana ta a matsayin abokin gaba
Shugaban Turkiyya Raccep Tayyib Erdogan, Firaminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu Hoto: Raccep Tayyib Erdogan/The Prime Minister of Israel
Source: Facebook

TRT Afrika ta wallafa cewa Hakan Fidan ya kara da cewa wannan fahimta na nuna yadda Ankara ke kallon yadda manufofin Isra’ila ke sauyawa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Isra'ila na neman sabon makiyi - Turkiyya

The New Arab ta ruwaito cewa Fidan ya jaddada bukatar kasashen yankin su hada kai wajen kafa wata yarjejeniya ta tsaro wadda za ta ginu kan mutunta ikon kasa, cikakken ikon yankuna da kuma tsaron kasa.

Ministan ya kuma yi zargin cewa hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Lebanon sun yi kama da irin barnar da ta yi a Gaza, yana mai cewa ana lalata gidaje da muhimman ababen more rayuwa.

Ya bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na rage yawan jama’a a yankunan da ake kai hare-hare. Game da Syria, Fidan ya ce hare-haren Isra’ila a can na zama babbar matsala.

Ya kara da bayyana cewa kasar Isra'ila ta haifar da barazana mai tsanani ga Turkiyya. Yake cewa bai dace kasashen da ke yankin su nade hannaye ba su yi komai ba.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan da suka faru bayan tsagaita wutar Iran, Amurka da Isra'ila

Turkiyya na son a bude Hormuz

A bangaren diflomasiyya, ya ce Iran da Amurka na nuna sahihanci wajen ci gaba da yarjejeniyar tsagaita wuta, amma ya yi gargadin cewa wasu bangarori na waje na iya kawo cikas ga wannan kokari.

Turkiyya ta nemi Gabas ta Tsakiya ta dunkuld wuri uda
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan yayin taro a Ankara. Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Hakan Fidan ya kuma sake jaddada goyon bayan Turkiyya ga bude mashigar Hormuz ta hanyar zaman lafiya, yana gargadin cewa amfani da karfin soji zai iya haifar da manyan hadurra.

Dangane da kungiyar tsaro ta NATO, ya ce taron da za a yi a Ankara ranar 7 zuwa 8 ga watan Yuli 2026 na iya zama daya daga cikin mafi muhimmanci a tarihin kungiyar, tare da samar da dama wajen kara tsara dangantakar NATO da Amurka.

Kasar Turkiyya ta gargadi Isra'ila

A baya mun wallafa cewa Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya yi gargadi ga Isra'ila yayin da ake ci gaba da yaki tsakaninta da kasar Iran a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ke jefa yankin a hadari.

Kara karanta wannan

Ana batun tattaunawa tsakanin Iran da Amurka, Netanyahu ya dauko rigima da wata ƙasa

Erdogan ya bayyana damuwa ganin yadda yakin Iran da Isra'ila ya jefa Gabas ta Tsakiya cikin mummunan rikici, inda ya zargi Benjamin Netanyahu da fadada rikici zuwa kasashe kamar Lebanon da sauransu.

Erdogan ya yi wannan bayani ne yayin wani taron jam’iyyarsa a Ankara inda ya ce yakin ya jefa yankin cikin mawuyacin hali mafi muni cikin shekaru 100 a cikin watan Maris na shekarar 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng