Karfin Hali: Wata Matashiya 'Yar Najeriya Ta Buɗe Gidan Karuwai a Kasar Waje
- Rundunar ƴan sandan Ghana ta cafke wata matashiya 'yar Najeriya mai shekaru 28, Esther Egbuhama, kan zargin gudanar da gidan karuwai
- An gudanar da samamen ne a gidan karuwan mai suna "Mama Nice" da ke yankin Manso Watreso a jihar Ashanti bayan samun bayanan sirri
- Duk da cewa karuwanci ya zama ruwan dare a Ghana, dokar ƙasar ta haramta shi, inda ƴan sanda suke kame bisa tanadin sashi na 277
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ghana – Rundunar ƴan sandan ƙasar Ghana ta kama wata mata 'yar asalin ƙasar Najeriya, Esther Egbuhama, mai shekaru 28.
Ana zargin cewa Esther da wasu, sun bude gidan karuwai a yankin Ashanti, kuma ita ce da kanta take gudanar da harkokin gidan.

Source: Getty Images
An cafke 'yar Najeriya a Ghana
Kamar yadda kafar yaɗa labarai ta GhanaWeb ta ruwaito, an cafke wacce ake zargin ne a ranar Lahadi, 19 ga watan Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan
Yadda rikicin Iran ya buɗe kasuwar man Najeriya, ƙasashen Turai sun zo neman agaji
Jami’an rundunar ƴan sandan Manso Nkwanta ne suka gudanar da samamen a gidan karuwan mai suna "Mama Nice Lodge" da ke garin Manso Watreso.
Wannan mataki ya biyo bayan bayanan sirri da ƴan sandan suka samu kan harkokin baɗala da ake gudanarwa a wurin.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu, ta bayyana cewa wannan samame wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi na ruguza sansanonin masu aikata laifuffuka a yankin.
Abokan badalar Esther sun tsere
Ko da yake an kama Esther a wurin, dukkan sauran abokan hulɗarta da sauran waɗanda ake zargi sun ranta a na kare, inda suka tsere kafin jami’an tsaro su ƙarasa wurin.
Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa:
"Ƴan sanda sun sami bayanan sirri kan abubuwan da ke faruwa a wurin, hakan ya sa aka shirya samamen domin dakatar da laifuffukan da ake yi tare da kama masu laifin."
A halin yanzu, ana tsare da Esther Egbuhama a ofishin ƴan sanda na Manso Nkwanta inda take taimaka wa masu bincike ta hanyar bada bayanai, in ji rahoton Punch.
Karuwanci a Ghana
Karuwanci, wanda aka fi sani da "ashawo" ko "toutou" a Ghana, haramun ne a ƙarƙashin doka, amma rashin aikin yi da talauci sun sanya ya zama ruwan dare a garuruwa da tashoshin jiragen ruwa.
Wani rahoto da aka wallafa a WikiPedia ya nuna cewa karuwai sun sha yin fafutukar ganin an halatta sana'ar tasu, yayin da hukumomi ke nuna damuwa kan yaduwar cutar kanjamau da safarar yara.

Source: Getty Images
Akwai rukunai hudu da ake gudanar da harkar karuwanci a Ghana, kamar haka:
- Gidajen karuwai: Ana gudanar da su a tsofaffin rumbuna, tantuna, ko masauki kamar yadda ya faru a Manso Watreso.
- 'Yan zama wuri daya: Waɗannan tsofaffin mata ne ko zawarawa da ke zama a ƙofofin gidajensu suna kiran kwastomomi.
- 'Yan yawo: Mata ne matasa da ke yawo a kan tituna, mashaya, da manyan otel otel.
- Kawalai: Mafi akasari masu tuka tasi ne da ke zama kawalai tsakanin mata da kwastomomi, inda suke karɓar kamasho daga kowane ɓangare.
Rundunar ƴan sandan yankin Ashanti ta Kudu ta tunatar da jama’a cewa gudanar da gidan karuwai babban laifi ne a ƙarƙashin sashi na 277 na dokar laifuka ta ƙasar Ghana.
Tilasta yara yin karuwanci a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar Amotekun ta ceto ‘yan mata daga gidan karuwa a Ifo, Ogun, inda aka kama mutane 15, ciki har da magajiyar gidan.
Waɗanda aka ceto sun bayyana cewa an yaudare su ne tun farko, sannan aka tilasta su yin karuwanci, inda suke lalata da maza 10 zuwa 12 a kowace rana.
Wasu 'yan mata biyu, sun yi bayani dalla dalla yadda mai kula da gidan karuwan ta yi masu barazanar kisa idan suka gudu.
Asali: Legit.ng

