Yadda bakin talauci ke tilasta 'yan mata shiga harkar karuwanci a jihohin kasar nan

Yadda bakin talauci ke tilasta 'yan mata shiga harkar karuwanci a jihohin kasar nan

- Wata kungiya mai zaman kanta ta bayyana wasu dalilai da ya sanya 'yan mata shiga harkar karuwanci a kasar nan

- Kungiyar ta ce bakin talauci da wahalar rayuwa ke tilasta da yawa daga cikin 'yan matan shiga harkar karuwancin

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna "Smart Mothers Foundation" ta kwarai da gaske akan yadda 'yan mata suke tsunduma harkar sana'ar karuwanci, musamman a jihar Akwa-Ibom saboda bala'in talauci da wahalar rayuwa, inda ko audugar al'ada basa iya samun kudin siya.

Kungiyar ta bayyana cewa wannan dalilin ne yasa sanya 'yan mata da yawan gaske suke yin cikin shege sai kuma su rasa yadda zasu yi dashi a lokuta da dama.

Yadda bakin talauci ke tilasta 'yan mata shiga harkar karuwanci a jihohin kasar nan
Yadda bakin talauci ke tilasta 'yan mata shiga harkar karuwanci a jihohin kasar nan
Asali: Facebook

Wata daya daga cikin mambobin kungiyar Sifon Udo ta yi korafi akan wannan lamarin, a wani taro na inganta rayuwar yara kanana da jaridar Premium Times ta gabatar a garin Uyo babban birnin jihar Akwa-Ibom.

Matar ta yi bayanin cewa a yanzu haka kungiyar ta su tana lura da wasu 'yan mata su uku da suka dauki cikin shege suka rasa yadda za su yi dashi.

Ta kara da cewa bakin talauci, mu'amala da abokanan banza da rashin tarbiya sune abubuwan da suke haddasa irin wannan matsala ga 'yan matan.

KU KARANTA: Jonathan yayi wata magana mai ratsa zuciya, yayin da Buhari yake shirin shiga Ofis a karo na biyu

Udo ta bayyana cewa kungiyar ta su tana koyar da 'yan matan da ta samu a irin wannan hali, sana'o'i irin na hannu domin su samu su dogara da kansu, ba sai sun koma irin sana'ar su ta karuwanci ba.

Hakazalika Uduak Ekong shugabar kungiyar mata manema labarai na jihar (NAWOJ) da kuma Imaobong Akpan sun yi korafi matuka akan wata halayya da mata suke yi yanzu ta shiga kungiyar asiri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel