Cakwakiya: Gwamna Ya Rufe 'Gidan Karuwai' da Ake Baɗala a Makarantar Firamare

Cakwakiya: Gwamna Ya Rufe 'Gidan Karuwai' da Ake Baɗala a Makarantar Firamare

  • Gwamnatin Monday Okpebholo ta bankado gidan karuwai a makaranta a Esan ta Yamma a jihar da ake zargin ana aikata badala
  • Mai kula da kare kadarorin gwamnati, Eugene Okolosie ya ce an kwato fiye da filaye 2,000 daga wasu da ke almundahanar fili
  • An gano wasu makarantu da wuraren gwamnati da aka sayar da su ba bisa ka'ida ba, an sha alwashin hukunta masu hannu a lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Benin-City, Edo - Gwamnatin jihar Edo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Monday Okpebholo ta rufe wani otal a makarantar firamare.

Gwamnatin Edo ta gano kuma ta rufe gidan karuwai da ke cikin wata makarantar firamare a karamar hukumar Esan ta Yamma da ke jihar.

An rufe otal a makarantar firamare
Gwamna ya rufe otal da aka samu a makarantar firamare a Edo. Hoto: Legit.
Asali: Original

Gwamnatin jihar Edo ta kwato filaye 2,000

Mai kula da kare kadarorin gwamnati, Hon. Eugene Okolosie, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a birnin Benin, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa an kwato fiye da filaye 2,000 da aka mamaye ba bisa ka'ida ba, daga hannun masu almundahana a fadin jihar.

Okolosie ya ce sama da gidaje 150,000 an gina su ne a kan ƙasar gwamnati ba tare da izini ba, ya nemi mutane su duba tsarin 'GIS' kafin saya.

Zargin badala: An rufe otal a makarantar firamare

Ya bayyana cewa kashi 70 cikin ɗari na wasu filayen sun faɗa hannun masu mamaye ƙasa, inda makarantu suka fi fuskantar wannan matsala.

Ya ce:

“A jami’ar AAU kadai mun kwato filaye da dama daga masu ƙwace ƙasa, har da na makarantu."

A Ujuele Okolosie ya tabbatar da cewa, an gina gidan karuwai a cikin makaranta wanda ake zargin baɗala kawai ake aikatawa.

“Mun rufe gidan kuma muna tattaunawa da gwamnati kan batun domin sanin matakin da ya kamata a dauka saboda kare faruwar haka a nan gaba."

- Cewar Okolosie

Gwamna ya kama otal a cikin makarantar firamare
Gwamnatin Edo ta rufe wani otal a makarantar firamare. Hoto: Sen. Monday Okpebholo.
Asali: Twitter

Yadda ake badakalar filaye a Edo

A unguwar Iyoba, al’umma sun raba makarantar gida biyu suka sayar da rabin, har da ma’ajiyar abinci kuma ana bincike yanzu, cewar rahoton Daily Post.

Ya ce sun karɓi korafe-korafe sama da 3,000 daga al’ummomi kan ƙwace kadarorin gwamnati a cikin wata biyu da suka wuce wanda ke barazana ga tsaron dokokin filaye.

Okolosie ya yaba wa Gwamna Monday Okpebholo bisa samar da lauyoyi da ke taimakawa wajen gurfanar da masu laifi da kuma kare kadarorin gwamnati.

Hisbah ta rufe otal makare da giya a Yobe

A baya, kun ji cewa Hukumar Hisbah tare da haɗin guiwar NDLEA da NSCDC sun rufe 'Maina Lodge' a Damaturu a jihar Yobe inda suka kama kwalaye 209 na giya.

Shugaban hukumar, Dr. Yahuza Abubakar, ya ce an gano giya a motar 'Golf' da kuma daki na musamman a otal din da aka kai samame.

Shugaban hukumar ya ce gidan haya da ake zargin ana amfani da shi wajen fasikanci shi ma an rufe, yayin da ake ci gaba da bincike.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.