Rigima Ta Ƙara Zafi, Kasar Iran Ta Dauki Matakin da Amurka ba Ta So a Hormuz

Rigima Ta Ƙara Zafi, Kasar Iran Ta Dauki Matakin da Amurka ba Ta So a Hormuz

  • Dakarun rundunar IRGC ta kasar Iran sun sanar da rufe mashigar ruwa ta Hormuz har sai baba-ta-gani bayan hare-haren Amurka
  • Kasar Iran ta yi barazanar kai hari kan sababbin sansanonin wadanda ta kira da abokan gaba idan aka sake kai mata hari
  • Matakin na iya kara dagula tattaunawar zaman lafiya taakanin Iran da Amurka tare da shafar kasuwar makamashi ta duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun sanar da cewa an rufe mashigar ruwan Hormuz har sai baba-ta-gani.

Dakarun Iran sun dauki wannan mataki ne bayan sun kai harin gargadi kan wani jirgin ruwa da suka ce ya bi hanyar da ba a amince da ita ba.

Hormuz.
Jiragen ruwa a hanyar wucewarsu ta mashigar Hormuz Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta rawaito cewa matakin na iya kara dagula kokarin farfado da tattaunawar Iran da Amurka bayan musayar hare-hare da barazanar da bangarorin biyu suka yi a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi, Iran ta kai mummunan harin ban mamaki kan Amurka

Iran ta dakatar da zirga-zirga a Hormuz

Rahotanni sun ce wasu kafafen yada labarai na Amurka sun bayyana cewa Washington ta bai wa Tehran wa'adin zuwa ranar Asabar ta dakatar da kai hare-hare kan jiragen da ke amfani da mashigin Hormuz.

Sai dai IRGC ta ce ta yi harbin gargadi tare da dakatar da wani jirgin ruwa bayan ya yi watsi da umarnin amfani da hanyar jiragen ruwa da aka amince da ita.

A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, IRGC ta ce:

"Bayan wannan lamari, an rufe mashigar Hormuz har sai baba-ta-gani, kuma har sai Amurka ta dakatar da tsoma baki a wannan yanki. Ba za a bari wani jirgin ruwa ya ratsa ba."

Iran ta yi sabuwar barazana

IRGC ta kuma yi gargadin cewa za ta kai hari kan wasu sababbin sansanonin abokan gabanta a yankin idan aka sake daukar matakin soja a kanta.

Mashigin Hormuz na daya daga cikin muhimman hanyoyin safarar mai da iskar gas a duniya, kamar yadda tahsar Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yaƙin Amurka da ƙasar musulunci ta Iran ya zama 'alheri' ga attajirin Najeriya, Dangote

Kusan kashi 20 cikin 100 na safarar danyen mai da iskar gas mai ruwa (LNG) ta duniya na bi ta wannan mashiga, lamarin da ke sa duk wani cikas a yankin ya zama babban abin damuwa ga kasuwannin makamashi.

Takaddama kan makomar Hormuz

Iran ta dage cewa tana da ikon tsara yadda ake zirga-zirga ta mashigar Hormuz, tare da bayyana aniyarta ta karbar harajin wucewa daga jiragen ruwa da ke amfani da hanyar.

Khamenei.
Jagoran addinin kasar musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Jami'an Iran sun kuma ce ba za su koma tsarin da ake amfani da shi kafin yakin ba, inda jiragen ruwa ke wucewa ba tare da wani takunkumi ba.

Sai dai Amurka ta yi watsi da wannan matsaya, tana mai cewa dole ne jiragen kasuwanci su ci gaba da amfani da mashigin cikin 'yanci.

Ƙasar Iran ta shirya ɗaukar fansa

Kun ji cewa an wallafa jerin shugabannin kasashen waje 13 da ta ce za a dauki fansa a kansu bayan kashe marigayi Jagoran Koli Ayatollah Ali Khamenei.

Sabon Jagoran Koli Mojtaba Khamenei ya yi alkawarin daukar fansa, inda ya fitar da sakonsa na farko tun bayan jana'izar da aka yi.

Sai dai Mojtaba bai ambaci sunayen mutanen da ake nufi ba, kuma babu wata alama da ke nuna gwamnatin Iran ta amince da jerin sunayen da aka fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262