Lebanon Ta Watsa wa Trump Kasa a Ido, Ta Dauki Mataki na ban Mamaki kan Isra'ila

Lebanon Ta Watsa wa Trump Kasa a Ido, Ta Dauki Mataki na ban Mamaki kan Isra'ila

  • Shugaban Lebanon ya ki amincewa ya tattauna da firaministan Isra'ila duk da kokarin da Donald Trump ya yi na shiga tsakanin su
  • Gwamnatin Lebanon ta jaddada cewa ba za ta amince da tattaunawa kai tsaye ba har sai Isra'ila ta tsagaita kai hare hare a sassan kasar
  • A halin da ake ciki, Hezbollah da sojojin Isra'ila na ci gaba da kai wa juna hare-hare, lamarin da ke kara jawo asarar rayuka da ruguza muhalli

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Lebanon – Shugaban ƙasar Lebanon, Joseph Aoun, ya ƙi amincewa da yin tattaunawa ta tarho da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, a ranar Alhamis, 16 ga Afrilu, 2026.

Wannan tattaunawa da Shugaba Donald Trump ya sanar, ta kasance mataki na farko na tattaunawa kai-tsaye tsakanin shugabannin ƙasashen biyu cikin sama da shekaru 30, da nufin tsagaita yaƙi tsakanin Isra'ila da Hezbollah.

Kara karanta wannan

Italiya ta datse yarjejeniyar sayar wa Isra'ila makamai kan yakin Lebanon

Shugaban Lebanon ya ki amince wa da bukatar tattaunawa da Firayim Ministan Isra'ila.
Shugaban kasar Lebanon, Joseph Aoun (hagu), Shugaban Amurka, Donald Trump (tsakiya) da Firayim Minista Benjamin Netanyahu (dama). Hoto: Alexi J. Rosenfeld and Ronen Zvulun Via Getty Images
Source: Getty Images

Lebanon ta fasa tattaunawa da Isra'ila

Wani babban jami'in gwamnati wanda ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatar wa kafar labarai ta CNN cewa, Lebanon ta sanar da Amurka cewa ba ta shirya ɗaukar wannan matakin ba a yanzu.

Wannan bayani ya fito ne yayin wata tattaunawa da ministan wajen Amurka, Marco Rubio, inda jami'in ya bayyana cewa Washington ta fahimci matsayar Lebanon na ƙin tattaunawa ba tare da tsagaita wuta ba.

Duk da cewa ƙasashen biyu sun gudanar da wasu jerin zaman tattaunawa na diflomasiyya a birnin Washington a ranar Talata, Lebanon ta dage kan cewa dole ne a tsagaita buɗe wuta kafin a ci gaba da kowace irin tattaunawa.

Gwamnatin Lebanon ta yi alƙawarin kwance wa ƙungiyar Hezbollah ɗamarar yaƙi, amma ta ce ba za ta yi hakan ba ƙarƙashin matsin lambar hare-haren Isra'ila.

Shirin da Isra'ila take yi a Kudancin Lebanon

Kara karanta wannan

Uganda: Kasar Afrika ta gargadi Iran, za ta tura sojoji 500,000 su kwace Tehran

A ɓangare guda, Isra'ila na kallon waɗannan tattaunawa a matsayin shawarwari kawai, amma ta kuduri aniyar mayar da hankali kan rusa ƙarfin soji na Hezbollah, in ji rahoton The Guardian.

Yayin da tattaunawar ke fuskantar cikas, dakarun Isra'ila sun ci gaba da kutsa kai cikin kudancin Lebanon, inda Firaminista Netanyahu ya bayyana cewa suna shirin samar da "yankin tsaro" da zai kai kilomita takwas zuwa 10 cikin ƙasar Lebanon.

Yayin da ake wannan takun-saƙa, shugaban rundunar sojin Pakistan ya gana da kakakin majalisar dokokin Iran domin tursasa batun tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da ta dakatar da yaƙin makonni bakwai tsakanin Isra'ila da Amurka da kuma Iran.

Isra'ila da Hezbollah na ci gaba da kai wa juna hare-hare, lamarin da ya jawo kisan mutane da dama a Lebanon
Hayaki na tashi daga wani wuri da makamin Isra'ila ya sauka a Kudancin Beirut a ranar 8 ga Afrilu, 2026. Hoto: anwar amro / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Hezbollah da Isra'ila sun dage da kai hare-hare

Wannan na zuwa ne yayin da Lebanon ke ci gaba da kasancewa cikin rarrabuwar kai kan batun kulla dangantaka da Isra'ila, wadda suke fafata yaƙi da ita tun shekarar 1948.

Hare-hare tsakanin Isra'ila da Hezbollah sun fi tsananta a yankunan da ke kan iyaka, musamman a garuruwan Tyre, Nabatieh, da Bint Jbeil.

Hezbollah na amfani da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami wajen kai hari Arewacin Isra'ila, yayin da sojojin Isra'ila ke ƙara ƙaimi wajen luguden wuta a kudancin Lebanon domin kakkabe mayakan ƙungiyar.

Kara karanta wannan

Bayan tattaunawar Iran da Amurka ta rushe, an harba wasu makamai kan Isra'ila

Hezbollah ta harba makamai kan Isra'ila

A wani labari, mun ruwaito cewa, an harba wasu makaman roka guda biyu daga kudancin ƙasar Lebanon zuwa yankin Upper Galilee da ke arewacin Isra'ila a ranar Lahadi, 12 ga Afrilu, 2026.

Hukumar tsaron cikin gida ta Isra'ila (IHFC) ta tabbatar da cewa an kunna ƙararrawar gargaɗi a yankin Metula da ke kusa da iyaka domin ankarar da mazauna yankin su nemi mafaka.

Wannan sabon farmakin ya ƙara rura wutar fargaba ga mazauna Arewacin Isra'ila waɗanda suka daɗe suna fuskantar barazanar makamai daga Lebanon.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com