Ana Wata ga Wata: Jirgin Iran Ya Kutsa Wajen da Trump Ya Jibge Sojoji a Hormuz

Ana Wata ga Wata: Jirgin Iran Ya Kutsa Wajen da Trump Ya Jibge Sojoji a Hormuz

  • Rahotanni sun nuna cewa wani babban jirgin dakon man Iran ya wuce ta mashigar Hormuz duk da barazanar da shugaba Donald Trump ya yi
  • A farkon makon nan shugaban Amurka ya sanar da cewa zai toshe wata hanya da ke kusa da mashigar Hormuz domin dakile tattalin Iran
  • Yayin da ake maganar sake tattaunawa tsakanin kasashen, wani rahoto ya nuna cewa Amurka ta sake tura wasu dakarun sojoji Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Wani babban jirgin dakon mai na Iran da ke ƙarƙashin takunkumi ya tsallaka mashigar ruwan Hormuz zuwa tashar Imam Khomeini duk da katangar da Amurka ta sanya.

Jirgin, wanda ke daukar kaya sosai, na iya ɗaukar gangunan mai har miliyan biyu, amma ba a tabbatar ko yana ɗauke da mai ba ko kuma babu kaya a cikinsa lokacin da yake dawowa ba.

Kara karanta wannan

China ta dura kan Amurka, ta yi magana mai zafi kan zargin tura makamai zuwa Iran

Jirgin ruwan Iran a teku
Jirgin ruwa dauke da tutar Iran na tafiya a teku. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa, bisa bayanan bin diddigin jiragen ruwa, wani jirgin da ke ɗauke da kayan abinci ya shiga Tekun Fasha kuma yana kan hanyarsa zuwa tashar Imam Khomeini.

Haka kuma, wani rahoto ya ce wani jirgin mai da ke cikin jerin takunkumin Amurka shi ma ya shiga cikin yankin Iran da safiyar yau.

Hormuz: Martanin Iran ga Amurka

Dangane da shigen da Amurka ta sanya, Ministan harkokin cikin gida na Iran ya ce suna da iyakokin ƙasa da na teku masu fadin sama da kilomita 8,000, saboda haka toshe mashigar Hormuz ba zai yi tasiri ba.

Ya kuma bukaci a bude wasu hanyoyi daban-daban, ciki har da yankunan kasuwanci na musamman, domin sauƙaƙa shigo da kaya da fitar da su.

Ya ce:

"Babban kaso na kasuwancin Iran yana gudana ne ta gabar Kudancin ƙasar, wanda ke da matuƙar muhimmanci.
"Saboda haka, rundunar sojin ƙasar ta ce za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaro a yankunan da suka hada da Tekun Fasha, Tekun Oman da mashigar Hormuz."

Kara karanta wannan

JD Vance ya fito da gaskiya, an ji matakin Iran da ya fi cutar da Amurka a lokacin yaki

Amurka ta tura sojoji kusa da Iran

A gefe guda, rahotanni sun nuna cewa Amurka na shirin tura karin dubban sojoji zuwa Gabas ta Tsakiya nan da kwanaki masu zuwa, duk da cewa Donald Trump ya ce yaƙin na “gab da ƙarewa”.

Rahoton The Independent ya nuna cewa har yanzu ba a san adadin sojojin da za a tura ba, kuma babu wani jami’in Amurka da ya tabbatar da wannan shiri a hukumance.

Shugaba Donald Trump da wasu sojojin Amurka
Donald Trump yana yi wa sojojin Amurka jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya riga ya bayyana cewa Tehran na son cimma yarjejeniya domin kawo ƙarshen rikicin, yana mai cewa idan ya janye yanzu, zai ɗauki Iran shekara 20 kafin ta sake farfaɗowa.

Shugaba Trump ya caccaki Fafaroma

A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake caccakar Fafaroma Leo game da yakin da ya ke da Iran.

Trump ya bukaci a sanar da Fafaroma abin da ya faru a kasar Iran a lokacin zanga-zangar da aka yi a karshen 2025 idan bai sani ba.

Sukar da Trump ya yi tazo ne bayan wani martani da Fafaroman ya masa a lokacin da yake shirin zuwa kasashen Afrika ziyara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng